Katsina (birni)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Globe icon.svgKatsina
The view from peak of Gobarau Minaret.jpg

Wuri
Locator Map Katsina-Nigeria.png
 12°59′20″N 7°36′03″E / 12.9889°N 7.6008°E / 12.9889; 7.6008
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jerin jihohi a NijeriyaJihar Katsina
Babban birnin
Labarin ƙasa
Yawan fili 142 km²
Bayanan tarihi
Ƙirƙira 1987
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwa supervisory councillors of Katsina local government (en) Fassara
Gangar majalisa Katsina legislative council (en) Fassara
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci

Katsina wato Babban birnin Katsina wanda akafi sanida qaramar hukumar Katsina (Katsina LGA) garine mai girman gaske da ci gaba da kuma yawan mutane wacce akan kira (Katsina Metropolis).

Tarihi[gyara sashe | Gyara masomin]

Katsina gari ne mai daɗaɗɗen tarihi, kuma tana da ƙofofi da akayi su saboda garin zagaye yake da ganuwa[1]. Katsina birni ne, da ke a Jihar Katsina, a ƙasar Nijeriya.[1] A wani tarihin kuma an nuna cewa wani mutum da aka kira Bayajidda ɗan sarkin bagadaza ya kafa katsina dalilin zuwansa Daura kuma ya aura sarauniyar Daurama.[1]

Masarautar Katsina[gyara sashe | Gyara masomin]

Gidan Korau watau "Katsina Royal Province" kayataccen masarautace wacce aka ginata a tsakiyar Birnin Katsina. Gidan Korau na daya daga cikin alamomi ne dake nuna tsawon tarihi da qwarewar al'adun qasar Hausa. Kamar yadda masana tarihi suka fada, an ginata ne a shekara ta 1348 AD lokacin sarki Muhammadu Korau, wanda shi ne sarki na farko a garin Katsina muslimi. Wannan shi ne dalilin da yasa ake kiran masarautar katsina da 'Gidan Korau'. Kuma tana daya daga cikin dadaddun masarautun kasar hausa, kamar su masarutar Daura, Kano da Zazzau. kuma an kewaye masarautar da ganuwa City wall 'Ganuwar Gidan Sarki' (Wanda a halin yanzu babu wannan ganuwan). Babar kofar da zata kai mutun zuwa fada ana kiranta 'Kofar Soro', kuma kofar bayan gidan sarki ana kiranta 'Kofar Bai' (yanzu babu wannan kofar). Gidan Sarkin yana cikin masarautar, wacce aka kawatata da gine-gine da kuma kayan al'adu dabab-daban.[2] Sarkin katsina na yanzu shi ne Alhaji Abdulmumini Kabir Usman.

Kidaya[gyara sashe | Gyara masomin]

Bisa ga ƙidayar jama'a a shekarar 2006, akwai jimillar mutane 318,459 (dubu dari uku da sha takwas da dari huɗu da hamsin da tara).[3] An gina birnin Katsina a karni na sha huɗu.

Kofofi[gyara sashe | Gyara masomin]

Tarihi ya nuna cewa a da akwai ƙofofi guda 9 a Birnin Katsina wanda suka hada da ƙofar ƙaura, durbi, ƴan ɗaka, sauri, Guga da ƙwaya, Marusa, Keke, Agulu, Waziri,Gazobi. Amman yanzu babu ƙofofin Keke, Agulu, Waziri da gazobi[4].

Kofar Kaura round about, Katsina

Kofar Kaura: Kofa ce dake tsakiyar Birnin Katsina wacce take da shatale tale mai tambarin ''kwarya da Ludayin fura da nono'' da kuma kofa wadda ke arewacin shataletalen kuma tana kan hanyar birnin Katsina zuwa Kano.[5]

Kofar Fadan Sarkin Katsina

Kofar Soro[6] koface mai dumbin tarihi tarihi wacce ke da tsofaffin unguwanni da gine-ginen tarihi musaman Gidan Sarkin Katsina da kuma tsibirin Gobarau wacce aka ginata a shekara ta "dubu daya da dari hudu da talatin da takwas (1438).

Kofar Sauri[7]:

Kofar Durbi[4]:

Kofar Marusa[8]:

Kofar Kwaya[9]:


Alqalam university Logo.jpg
University Gate
Senate building

Ilimi[gyara sashe | Gyara masomin]

Katsina tana daya daga cikin jihohin da sukafi kowa ilimin addini dana zamani a Nijeriya. Sannan suna cikin wanda suka fara amsar ilimin zamani lokacin turawan mulkin mallaka a Arewacin Nijeriya. sannan kuma akwai Katsina Teachers' College wacce aka ginata a 1845. Sannan akwai jami'oi na zamani manya guda biyu, Umaru Musa Yar'adua University da aka ginata a 2007 wanda shuga Umaru Musa Yar'adua ya gina, sai kuma Alqalam University waccce aka fi sani da "Islamic University" wacce itace Jami'ar musulunci na farko a Nijeriya.

Umyu First gate.jpg

Sannan akwai kolejin malamai ta Federal College of Education (FCE) da kuma Polytechnic wacce aka fi sani da Hassan Usman Katsina Polytechnic.

Sarakuna Fulani[gyara sashe | Gyara masomin]

Tun kafuwar katsina har zuwa yanzu akwai gidajen sarauta huɗu a garin katsina, gidajen sune, Durbawa, Gidan korau, Gidan Dallazawa, da kuma gidan Sulluɓawa[10].

Sarakanan Fulanin katsina sun kasu gide biyu ne; Gidan Dallazawa da kuma Sullubawa[11].

DALLAZAWA SULLUƁAWA
Ummaru Dallage      1805 – 1835 Muhammad Dikko           1906 – 1944
Siddqu                         1835 – 1844 Usman Nagoggo                1944 - 1981
Muhammadu Bello   1844 – 1869 Muhammadu kabir usman 1981[12] -
Ahmad Rufa’i              1869 – 1870
Ibrahim                        1870 – 1882
Musa                             1882 – 1887
Abubakar                      1887 – 1904
Yero                                1904 - 1906

Biblio[gyara sashe | Gyara masomin]

Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. ISBN 978-135-051-2. OCLC 43147940.

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

 1. 1.0 1.1 1.2 Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. p.2. ISBN 978-135-051-2.
 2. "KATSINA EMIRATE COUNCIL".. Retrieved 6 August 2015.
 3. Katsina (State, Nigeria) - Population Statistics, Charts, Map and Location". www.citypopulation.de. Retrieved 2021-03-31
 4. 4.0 4.1 Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. p.27. ISBN 978-135-051-2.
 5. Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. p.28. ISBN 978-135-051-2.
 6. Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. p.34. ISBN 978-135-051-2.
 7. Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. p.30. ISBN 978-135-051-2.
 8. Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. p.33. ISBN 978-135-051-2.
 9. Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. p.32. ISBN 978-135-051-2.
 10. Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. p.3. ISBN 978-135-051-2.
 11. Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. p.6. ISBN 978-135-051-2.
 12. Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. p.6-7. ISBN 978-135-051-2.