Batagarawa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Globe icon.svgBatagarawa

Wuri
 12°54′N 7°37′E / 12.9°N 7.62°E / 12.9; 7.62
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jerin jihohi a NijeriyaJihar Katsina
Labarin ƙasa
Yawan fili 433 km²
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci

Batagarawa karamar hukuma ce dake a jihar Katsina,arewa maso yammacin Nijeriya.Mafi akasarin mutanen Batagarwa hausawa ne da fulani da ke magana da harshen hausa.kuma garin shine ke da sarautar mallamawa na masarautar Katsina. garin na da yawan mutane kimanin mutum 132,094.Garin ya kasance karamar Hukuma a shekarar 1991, garuruwan da ke karkashin karamar hukumar sun hada da Bakiyawa, Kayauki, Batagarawa,Barawa,Ajiwa, da kuma kauyen dabaibayawa.Akasarin mutanen Batagarawa mabiya addinin musulunci ne.[1].

Tarihi[gyara sashe | Gyara masomin]

An kirkiri karamar hukumar Batagrawa a shekarar 1991.

Labarin Kasa[gyara sashe | Gyara masomin]

Batagarawa na da fadin kasa kimanin 433kmsq. Kuma tana da yanayin zafi/sanyi 35○c a duk shekara, sannan karfin guguwa kan kai 5km/h. sai kuma akasarin ruwa a iska (humidity) kan kai kashi 11%.

Tattalin arziki[gyara sashe | Gyara masomin]

Mafi akasarin mutanen cikin garin Batagarawa hedikwatar mulki ma'aikatan gwamnati ne, amma talakawan na kauyuka sun dogara ne da noman hatsi kamar dawa, gero, masara da wake. sannan mafi yawan mutanen sun dogara ne da kiwon shanu. sannan harkan saye da sayarwa na da matuqar mahimmanci a karamar hukumar musamman yadda suke da manyan kasuwanni kaman kasuwar nama da sababbin kasuwanni na zamani.

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.

.

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. "Batagarawa Local Government Area". www.manpower.com.ng. Retrieved 2021-07-12.