Danja

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Danja, Nigeria)
Danja

Wuri
Map
 11°23′00″N 7°34′00″E / 11.3833°N 7.5667°E / 11.3833; 7.5667
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaJihar Katsina
Labarin ƙasa
Yawan fili 501 km²
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci

Danja karamar hukuma ce da ke a Jihar Katsina, Arewa maso yammacin kasan Najeriya.

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

An ƙirƙiri Danja ne a shekarar 27/9/1991 An fiddata ne a daga cikin ƙaramar hukumar Bakori Jihar Katsina,

Ɗanja garin jajaye in kaga baƙi, baƙo ne, marmara ci ‘yar uwar ki ki kwana[1]. Akwai saɓani mai yawa tsakanin masana, game da ainihin wanda ya fara kafa garin Danja. Ance wani bamaguje ne mai suna ɗanjakau wanda kwararren manomi ne kuma maharbi wanda ya gina rijiya mai zurfin gaske fiye da kafa arba’in da shida[1], sannan kuma ance ja ne, daga garin ɗanja ya kafa wannan garin. A wani ƙaulin kuma har wa yau ance wani mutum ne mai suna ɗanja, ya kafa garin[1].

A zamanin sarkin Ɗanja Duna, ya kori dukkan maguzawan dake cikin garin Ɗanja, shi kuma ya gina ganuwar garin[2].

Tarihi ya nuna cewa kwararrafa taci garin Danja da yaƙi wanda daga nan ne mutane daga wurare daban daban kamar mutanen Likorobda Wazata daga ƙasar Zazzau daga Kagoro, daga Kagora da Bare-bari daga gobirawa da Kanawa suka kafa unguwannin su a wurare daban-daban wanda ta hakan aka samu unguwar kanawa, unguwar fulani, da unguwar gobirawa, da unguwar kagora, unguwar bare-bari da sauransu a garin Ɗanja[2].

Bayan jihadin Shehu Usman Dan-fodiyo, an samu zaman lafiya a dukkan ƙasashen hausa da bunƙasar kasuwanci dalilin musulunci da kuma ƙarin yawan garuruwa[2]. A lokacin sarkin katsina Muhammad Dikkko ne aka fara gina yar ganuwar Ɗanja, kuma canza wa kofofin suna zuwa kofar Arewa, kudu, yamma da Gabas[2].

Daga cikin abubuwan tarihin garin Ɗanja sun hada da rijiyar Ɗanja da Ɗanja ya gina, sannan akwai rijiyar Duhu wanda idan dare yayi za’ayi ta jin kiɗa na tasowa daga cikinta saboda wannan dalilin ba mai ƙara zuwa bakin rijiyar da zarar magariba ta yi. Shi kansa kabarin Ɗanja yana nan a gindin wata giginya kan tsauni dake tsakanin Ɗanja zuwa Dabai[3]. Sannan akwai wata kuka mai kogo a ƙofar yamma inda ake haƙo ƙarfen tama don ƙera makaman yaƙi da gyara su tun kafin jihadin Shehu Usman Ɗan Fodio[3].

Kasuwa[gyara sashe | gyara masomin]

A shekara ta 1903 aka bude kasuwar Ɗanja kuma an buɗe fulotin sayan auduga a 1913. Wanda a wannan shekarar har wa yau aka samo gundumar Ɗanja, aka naɗa “’iya labaran” matsayin hakimin ɗanja a 1914[3]

An kafa kamfanin buredin “bega” a 1918.

A shekarar 1921 kuma aka gina kurkuku da makarantar elementary.

Har wa yau an gina rijiyar kwakware a 1946.

An gina hanyar ɗanja zuwa bakori a 1947 sannan aka gina ɗanja zuwa zariya a 1951.

An bude asibitin zamani a ɗanja a 1956.

NTC ta buɗe ofishin ta ta kuma gonar taba a ɗanja shekara ta 1962.

A garin ɗanja kuma aka gina kamfanin mazarkwaila na farko a duk fadin garin Katsina.

Har ila yau dai akwai fim na “baban larai” wanda yayi suna a ƙasar hausa, anyi shine a ɗanja wanda ‘iya iro ne magajin farko da ya fara hawa babur a duk katsina.

A shekarar 1977 aka bunkasa babbban asibitin ɗanja ya zama babban asibiti.

Haka kuma nayi hanyar bakori zuwa ɗanja wacce ta zarce zuwa hunkuyi har ta hadu da titin zariya 1978.

A 1974 aka bude “sito da ofishin DI’o’” na frojet a shekara ta 1980.

Gundumar ɗanja ta samu zama ƙaramar hukuma a ranar 24 ga watan satumba a 1991[4].

Tarihin sarautar ɗanja da masana suka nuna ya fara daga lokacin da akai wa ɗanja Ganuwa a 1913 aka taro makaman Katsina Iya Labaran ya fara zama Hakimin Ɗanja. Sai kuma Makama Idi (1928 - 1938) wanda ya zauna a Bakori, sannan an samu canjin suna daga Iya zuwa Makama daga lokacin Makama Idi, Bayan shekara ta 1939 aka koma ana kirar sarautar Ɗanja Sarkin Fulani. Daga 1992 har wa yau bayan ƙirƙiro gundumar Ɗanja aka canza sunan sarautar zuwa Sarkin Kudun Katsina[4].

Sarauta[gyara sashe | gyara masomin]

Ga jerin sunayen wasu daga cikin sarakunan ɗanja. Sun haɗa da;

Sarakuna da shekarun da sukai mulki
Suna Hawa mulki Barin mulki
Makaman Katsina Iya Labaran 1914 1928
Makaman Katsina Idi 1928 1938
Sarkin Fulani Ibrahim 1939 1953
Sarkin Fulani Muntari 1953 1956
Sarkin Fulani Usman 1956 1987
Sarkin Fulani Abubakar Sadiq 1987 1991
Sarkin Kudu Muhammadu Yazid Sadiq 1991 Zuwa yau[5]

Biblio[gyara sashe | gyara masomin]

Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Danwaire : gwanki sha bara. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. ISBN 978-2105-93-7. OCLC 59226530.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 1.2 Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Danwaire : gwanki sha bara. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p.25 ISBN 978-2105-93-7.
  2. 2.0 2.1 2.2 2.3 Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Danwaire : gwanki sha bara. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p.26 ISBN 978-2105-93-7.
  3. 3.0 3.1 3.2 Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Danwaire : gwanki sha bara. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p.27. ISBN 978-2105-93-7.
  4. 4.0 4.1 Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Danwaire : gwanki sha bara. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. pp.27-28. ISBN 978-2105-93-7. .
  5. Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Danwaire : gwanki sha bara. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p.29. ISBN 978-2105-93-7. .