Ƙananan hukumomin Nijeriya
(an turo daga Kananan Hukumomin Nijeriya)
Jump to navigation
Jump to search
Nijeriya nada adadin Kananan hukumomi dari bakwai da saba'in da hudu (774) (LGAs). Kowace karamar hukuma nada Shugabanni dasuke da ikon gudanar da harkokin wannan karamar hukuma. Wadanda suka hada da Shugaba (chairman) wanda shine Babban mai Iko zartarwa a wannan karamar hukumar da kuma wasu mambobinsa wadanda ake zabensu a tare, sune: Kansiloli. Kowace karamar hukuma anraba ta zuwa Kananan mazabu mazabu wanda duk karamar hukuma nada adadin mazaba, karanci guda goma (10), mafi yawa kuma guda goma sha biyar (15).
Ayyukan Ƙaramar Hukuma a Nijeriya[gyara sashe | Gyara masomin]
Ayyukan da Kananan hukumomin dake Nijeriya keyi ko suke da damar yi, na nan a bayyane cikin Constitution amma ga daga cikin irin ayyukan da sukeyi:
- Bijiro da tsarin tattalin arziki ga gwamnatin jiha;
- Karbar haraji da kudaden datayi ayyuka;
- Samarwa, Kafawa da kula da makabartu, wuraren binne mutane da gidajen gajiyayyu ko marasa karfi;
- Bayar da izini ga masu ababen hawa, kamar, keke, trucks (other than mechanically propelled trucks), kwale-kwale, baro, da amalenke;
- Samarwa, Kulawa da gudanar kasuwanni, wuraren ajiye motoci da wuraren shakatawan jama'a;
- Ginawa da kula da Kananan hanyoyi (roads), layika (streets), hanyoyin ruwa (drains) da wasu manyan hanyoyin jama'a, wurin hutu, da wasu budaddun wuraren;
- Sama hanyoyi da layika suna, daba gidaje lamba;
- Samarwa da kula da ababen tafiye-tafiye na jama'a da wurin zubda shara;
- Yin rijista wadanda aka haifa, wadanda suka mutu, da wadanda suka yi aure;
- Binciken gidajen al'ummah ko na yan'haya saboda kayyade adadin kudin daya kamata subiya haraji, kamar yadda majalisar jiha ta kayyade,
- Tsarawa da kula da yadda ake gudanar da tallace-tallace, tafiya da ijiye dabbobin kiwo, shaguna da kiosks, wuraren cin abinci da wasu wuraren da ake sayar da abinci ga jama'a, da kuma wuraren wanki da guga.
Jerin Ƙananan Hukumomi[gyara sashe | Gyara masomin]
Anazarci[gyara sashe | Gyara masomin]
- ↑ 1.00 1.01 1.02 1.03 1.04 1.05 1.06 1.07 1.08 1.09 1.10 1.11 1.12 1.13 1.14 1.15 1.16 1.17 Cite web |title=List of Local Government Areas in Cross River State |url=http://www.the-nigeria.com/2014/05/local-government-areas-in-cross-river.html |archiveurl=https://www.webcitation.org/6XzVnEOmv?url=http://www.the-nigeria.com/2014/05/local-government-areas-in-cross-river.html |archivedate=23 April 2015 |deadurl=no |df= }}