Nangere

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Nangere


Wuri
Map
 11°51′N 10°58′E / 11.85°N 10.97°E / 11.85; 10.97
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaJihar Yobe
Labarin ƙasa
Yawan fili 980 km²

Nangere karamar hukuma ce dake jihar Yobe a Najeriya. Hedkwatarta na nan a garin Sabon Gari Nangere (ko Sabon Garin) a kan hanyar zuwa Gashua daga Potiskum a11°51′50″N 11°04′11″E / 11.86389°N 11.06972°E / 11.86389; 11.06972.

Geography na Nangere[gyara sashe | gyara masomin]

Karamar hukumar Nangere tana da girman kilomita murabba'i 980 kuma tana da matsakaicin yanayi na zafi/sanyi na 34 °C. Ƙaramar hukumar ta nada manyan yanayi guda biyu da suka hada da rani da damina yayin da aka kiyasta yawan ruwan sama a yankin ya kai milimita 890 na ruwan sama a shekara.[1]

Yawan jama'a[gyara sashe | gyara masomin]

Garin na da jimillar yawan jama'a 87,823 a ƙidayar 2006.

Lambar gidan waya[gyara sashe | gyara masomin]

Nangare na da lambar akwatin gidan waya na yankin ita ce 631.[2]

Garuruwa da Kauyuka[gyara sashe | gyara masomin]

Sauran garuruwa da ƙauyukan da suka hada da karamar hukumar Nangere sun hada da Dawasa, Tagamasa, Sabon Gari Nangere, Tikau, da Dorowa.

Tattalin Arzikin Nangere[gyara sashe | gyara masomin]

Yawancin mazauna Nangere suna gudanar da ayyukan noma. Ana noman amfanin gona iri-iri a ƙaramar hukumar yayin da ake kiwon dabbobi da sayar da su a yankin. Har ila yau ciniki ya bunkasa a karamar hukumar Nangere inda yankin ke da kasuwanni da dama inda ake saye da sayar da kayayyaki iri-iri. Sauran muhimman ayyukan tattalin arziki da jama'ar karamar hukumar Nangere ke gudanarwa sun haɗa da farauta, sana'ar fata da sana'o'in hannu da sauran su.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Nangere Local Government Area". www.manpower.com.ng. Retrieved 2022-05-09.
  2. "Post Offices- with map of LGA". NIPOST. Archived from the original on 2009-10-07. Retrieved 2009-10-20.