Kebbi
Jihar Kebbi Sunan barkwancin jiha: Ƙasar adalci. | ||
Wuri | ||
---|---|---|
![]() | ||
Ƙidaya | ||
Harshe | Hausa | |
Gwamna | Abubakar Atiku Bagudu (APC) | |
An kirkiro ta | 1991 | |
Baban birnin jiha | Birnin Kebbi | |
Iyaka | 36,800km² | |
Mutane 1991 (ƙidayar yawan jama'a) 2005 (jimila) |
2,062,226 3,630,931 | |
ISO 3166-2 | NG-KE |
Jihar Kebbi jiha ce dake a ƙasar Najeriya. Tana da yawan fili kimani na kilomita murabba’i 36,800 da yawan jama’a milyan uku da dubu dari shida da talatin da dari takwas da talatin da daya (jimilar 2005). Babban birnin tarayyar jahar ita ce Birnin Kebbi. Abubakar Atiku Bagudu shi ne gwamnan jihar tun zaben shekara ta 2015 har zuwa yau. Mataimakin gwamnan shi ne Samaila Yombe Dabai. Dattijan jihar sune: Bala Naallah, Ahmed Ogembe da Yahaya Abdullahi.
Jihar Kebbi tana da iyaka da misalin jihhohi hudu sune: Sokoto, Zamfara kuma da Nijar.
Kananan Hukumomi[gyara sashe | Gyara masomin]
Jihar Kebbi nada Kananan hukumomi guda ashirin da daya (21), da masarauta hudu, sune; (Gwandu, Argungu, Yauri da Zuru), da gundumomi (35). Kananan hukumomin sune:
- Aleiro
- Arewa Dandi
- Argungu
- Augie
- Bagudo
- Birnin Kebbi
- Bunza
- Dandi
- Fakai
- Gwandu
- Jega
- Kalgo
- Koko/Besse
- Maiyama
- Ngaski
- Sakaba
- Shanga
- Suru
- Danko/Wasagu
- Yauri
- Zuru
Jihohin Najeriya |
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara |