Jump to content

Abubakar Atiku Bagudu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abubakar Atiku Bagudu
Gwamnan Jihar Kebbi

29 Mayu 2015 - 29 Mayu 2023
Aminu Musa Habib Jega (en) Fassara
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

6 ga Yuni, 2011 - 4 ga Yuni, 2015
District: Kebbi Central
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

5 ga Yuni, 2007 -
District: Kebbi Central
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya

2003 - 2007
Rayuwa
Cikakken suna Abubakar Atiku Bagudu
Haihuwa Gwandu, 26 Disamba 1961 (62 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Makaranta Usmanu Danfodiyo University Faculty of Social Sciences (en) Fassara
Jami'ar Jos
Matakin karatu BSc Economics and Politics (en) Fassara
Harsuna Turanci
Hausa
Larabci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Mabiya Sunnah
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Abubakar Atiku Bagudu (An haife shi a ranar 26 ga watan Disamba shekara ta alif 1961) Dan Najeriya ne, kuma ɗan siyasa, wanda ya taba zama Sanatan Jihar Kebbi ta tsakiya, kuma ya rike mukamin Ministan Babban Birnin Tarayya a watan December shekarar 2008. ya zama ɗan takarar gwamna a karkashin jam'iyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen shekarar 2015 kuma ya samu nasarar zama Gwamna da sau biyu 2015-2019 da kuma 2019-2023.[1]

Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

Atiku Bagudu Yayi digirin farko na Kimiyya (B.Sc.) a fannin tattalin arziki a Jami'ar Usman Dan Fodio da ke Jihar Sakkwato. Yana kuma da M.Sc. Ya karanta Economics a Jami'ar Jos ta Jihar Filato sannan ya yi digiri na biyu a fannin fasaha (M.A.) a harkokin kasa da kasa daga Jami'ar Columbia ta Amurka.[2]

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

An zaɓe shi a matsayin Sanata mai wakiltar mazabar Kebbi ta tsakiya a jihar Kebbi a Najeriya a zaɓen cike gurbi bayan da Sanata Adamu Aliero ya zama ministan babban birnin tarayya a watan Disambar shekarar 2008. Ya yi nasarar sake tsayawa takara a watan Afrilun 2011.zaɓen ƙasa gabada a tutar jam'iyyar People's Democratic Party (PDP).[3] A matsayinsa na Sanata, ya kasance memba a kwamitin majalisar dattawa kan ilimi (Majalisar Tarayya ta 6), kwamitin harkokin kasashen waje da kwamitin harkokin cikin gida.[4]

Ya zama ɗan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kebbi a zaɓen 2015 ya kuma lashe zaɓen sannan an rantsar da shi a matsayin gwamna a ranar 29 ga Mayun shekarar 2015.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]