Faskari

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Globe icon.svgFaskari

Wuri
 11°43′00″N 7°02′00″E / 11.7167°N 7.0333°E / 11.7167; 7.0333
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jerin jihohi a NijeriyaJihar Katsina
Labarin ƙasa
Yawan fili 1,750 km²
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci

Faskari karamar hukuma ce da ke a jihar Katsina, Nijeriya. Faskari na da kimanin jama'a 125,181 a shekara ta 2003. Sarkin Faskari na yanzu shine Sarki Muhammadu Tukur Saidu.Faskari ta hada iyaka da Funtua daga gabas, karamar hukumar tsafe na jihar Zamfara daga yamma, Birnin Gwari (Jihar Kaduna) daga kudu-maso-yamma, Sabuwa daga kudu, Kankara daga arewa, Bakori daga arewa-maso-gabas da kuma karamar Dandume daga kudu-maso-gabacin garin.

Tarihi[gyara sashe | Gyara masomin]

Duk da akwai labarai da almarori da ke kokarin bayanin ainifin asalin garin faskari,an yarda cewa Faskari ta samo asali ne daga wasu fitattun larabawa da suka yi hijira daga Alkalawa (Gobir) zuwa Zaria wato Gido da Wori wanda suka yada zango a wani mafaskara (wato wajen sare itace) suka tadda wasu mutane ne da basu da addini. Tarihin Birnin Faskari ya soma daga shekara ta 1778. Daya daga cikin tsatson Kaura Kuren Gumaru ne ya tsara ginin ta na zamani na lokacin, a lokacin mulkin Sarki Katsina Muhammadu Bello (1844-1886).

Faskari ta zama karamar hukuma a watan Mayun shekara ta 1989, bayan an cire ta daga karamar hukumar Funtua. Cibiyar Faskari na nan a kudu-maso yammacin Katsina.

Karamar Hukumar Faskari ta rabu zuwa gundumomi guda biyu, "Gundumar Faskari" da kuma "Gundumar Maruwa" wanda kauyuka da yawa ke karkashinsu.

Daga farko, shuwagabannin garin su gamu da cikas iri-iri musamman na hare-hare da yakuna daga garuruwan dake makwabtaka dasu. Amma daga baya sun jure duk wadannan matsaloli saboda zaratan mayaka da jarumai da ke garin, wannan ya hassada tasowar kauyuka a gefen garin.Daga cikin wadannan garuruwa akwai Bilbis,Yarmalamai,Tsafe, Sauri,Zagami da sauransu wanda daga baya suka zamo garuruwan mu na yau.

Sanadiyyar tsaro ya samar da zaman lafiya a garin,har mutane suka fara sha'awar zama a garin karkashin jagoranchi masarutu guda biyu, wanda tarihi Faskari ba zai taba mantawa dasu ba; "Birnin Kogo" da kuma "Faskari". Wannan garuruwa sunyi kaurin suna a harkan siyasa na adalci tun kafin zuwan turawan mulkin mallaka a karkashin jagorancin Galadaci na masarautar Katsina.

Bare-Bari ke jagorancin Birnin Kogo, inda Gobirawa ke mulkan Faskari.A farko lamari,garuruwan guda biyu suna tafiyar da mulkinsu daban daban.Daga baya garin sun hade don tafiyar da tsarin mulkinsu a hade a matsayin Katsina ta tsakiya.

=== Kauyukan Faskari ===
 • Bilbis.
 • Yarmalamai.
 • Sauri.
 • Zagami.
 • Ruwan Godiya.
 • Tafoki.
 • Daudawa.
 • Nasarawa.
 • Maigora.
 • Machika.
 • Sabon Layi.
 • Birnin Kogo.
 • Mai Ruwa.
 • Faskari.
 • Yan Kara.

Jerin Sarakunan Faskari daga 1811-Yau[gyara sashe | Gyara masomin]

 1. Faskari Muhammadu Gidado 1811-1842
 2. Faskari Danyabani 1842-1879
 3. Faskari Ali 1879-1886
 4. Faskari Yunusa 1886-1879
 5. Faskari Danbardo. 1897-1918
 6. Faskari Abu 1931-1934
 7. Faskari Abdu 1934-1934
 8. Faskari Dan Ali 1934-1936
 9. Faskari Bawa 1936-1936
 10. Faskari Madauci 1936-1938
 11. Faskari Muhammadu Dankurciya 1938-1941
 12. Faskari Dandaguma. 1941-1943
 13. Faskari Ahmadu 1943-1952
 14. Faskari Sani 1952-1957
 15. Faskari Umaru Gajabu 1957-1959
 16. Faskari Umaru Dandago 1959-1990
 17. Faskari Ibrahim Sabon Gari 1990-2000
 18. Faskari Lawal Garba 2001-.....

Zama Karamar Hukuma[gyara sashe | Gyara masomin]

An kirkiri karamar hukumar Faskari a shekarar 1989.

Manazarata[gyara sashe | Gyara masomin]

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.

.

Ibrahimyakubu8026@gmail.com