Zariya
![]() | |||||
---|---|---|---|---|---|
Zaria (en) | |||||
|
|||||
![]() | |||||
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Jiha | Jihar Kaduna | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 408,198 (2006) | ||||
• Yawan mutane | 725.04 mazaunan/km² | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 563 km² | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Majalisar zartarwa |
supervisory councillors of Zaria local government (en) ![]() | ||||
Gangar majalisa |
Zaria legislative council (en) ![]() | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Zariya (ko kuma da turanci Zaria, sai kuma, Zazzau laƙabin ta kenan) Zaria gari ne dake cikin arewacin Najeriya, karamar hukuma ce a cikin jihar Kaduna, tana da iyaka da Funtuwa, babban birnin Kaduna da kuma Igabi, duka a ƙasar Najeriya. A bisa ga ƙidayar jama'a na shekarar ta 2006, jimillar mutane dubu ɗari bakwai da sittin ne a garin Zariya, amman daga bisani an ƙimanta yawan su a shekara ta 2017, ga jimillar mutane miliyan ɗaya. Birnin Zariya kilomita ɗari biyu da sittin ne daga Abuja, kilomita tamanin ne daga Zariya, kilomita ɗari ɗaya da sittin ne daga Kano.[1] garin Zazzau an saka masa suna ne daga Sarauniya Amina.[2]
Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]
Asalin zaria sarakunan Haɓe ne ke mulkin su, wanda su ka yi sarauta tun daga shekara ta 1505 zuwa shekarar 1802, A shekara ta 1804 ne Shehu Usman Ɗan Fodiyo yayi jihadi, inda ya yaƙi sarkin gobir mai suna Yunfa, a Yaƙin Ƙwoto, daga nan ne ya fara yaɗa sarautarsa da musulunci zuwa masarautun Hausawa, A garin zariya akwai Malam Musa wanda ya daɗe yana da’awar zuwa ga addinin musulunci, Malam Musa Bafillatani ne, Jin Jihadin Usman Ɗan Fodiyo yasa shima ya karɓa Tuta daga Usman Ɗan Fodiyo.Da Malam Musa da Yamusa mutumin fulani Barno suka doso Zariya suka yaƙi sarki Makau ɗan ƙabilar Haɓe, Makau sai ya gudu shi da mutanensa zuwa Zuba, wani gari ne na Gwari da Koro a yankin Abuja a yau, Malam Musa sai ya zama Sarkin zazzau na farko daga ƙabilar Fulani, bayan rasuwarsa sai aka naɗa Yamusa a shekarar ta 1821 a matsayin sarkin zazzau, shi kuma fulanin Barno ne, daga nan ne Bare-Bari da Fulanin Mallawa suka fara sarauta a kasar zazzau.[3]
Birni ne a kasar Hausa wanda kuma yana ɗaya daga cikin garuruwan da Shehu Usman ya bada tuta kuma addinin musulunci ya tabbata a ciki. Birni ne mai dadin zama saboda yanayinsa gashi kuma cibiyar ilimin addini dana boko a arewacin Najeriya. Wannan gari Allah ya albarkace shi da ƙasa ta noma da kuma ilimin addinin musulunci dana zamani wanda a dalilin haka ne baƙi daga maƙotan garin suke zuwa domin neman ilimi kai harma da na ƙasashen waje da kuma mutanen garin Zariya su kansu, Waɗannan garuruwa a wancen lokacin duka suna ƙarƙashin mulkin garin zazzau ne, inda Zariya take a matsayin babban birni, amman yanzu wasu daga cikin waɗannan garuruwan basa ƙarƙashin zazzau.[3]
s/n | Garuruwa | Garuruwa | |
---|---|---|---|
1-2 | Anchau | Zaria | |
3-4 | Soba | ||
5-6 | Damo | Likoro | |
7-8 | Ɗan Alhaji | Igabe/Igabi | |
9-10 | Garu | Ikara | |
11-12 | Gimba | Zuntu | |
13-14 | Giwa | Richifa | |
15-16 | Fatika | Kargi | |
17-18 | Funkwi | Kauru | |
19-20 | Ɗan Maliki | Lere | |
21-22 | Durum | Kubau | |
23-24 | Ɗan Lawal | Kudan | |
25-26 | Faki | Kuadaru |
Mutane[gyara sashe | gyara masomin]
Asalin mulkin Zariya yana ƙarƙashin Sarakunan haɓe ne, ana kiran garin da zazzau, zakzak ko zegzeg, dukkan waɗannan sunayen ana kiran garin zazzau da shi, amman daga bisani sunan zazzau ya canza zuwa Zariya, A inda kuma sarautar aka fi kiranta da zazzau, shiyasa sarkin garin ake kiran shi da sarkin zazzau, mutanen da suka fito daga garin ana kiransu da suna Bazazzagi, jam’i kuma Zazzagawa.[3].
Sarauta[gyara sashe | gyara masomin]
Asalin mulkin Zariya tana ƙarƙashin Sarakunan haɓe ne, wadanda ke mulkan masarautan Zazzau, amma daga baya sarakunan Mallawa da fulani suka haɗa hannu da Ƙarfi suka yaƙi sarakunan haɓe a shekarar 1804. Sarakunan Haɓe na farko sun rayu ne a Ƙarni na 15, wadanda a wannan lokacin ba'a iya tina shekarun da sukayi sarauta, amman sarakunan haɓe na biyu sunyi mulki ne a karni na 16, inda aka taskace shekarun mulkin su, har zuwa lokacin da sarakunan Fulani suka yake su, sarkin su na karshe shine Makau a Zariya, a Gobir kuma shine Yunfa.
s/n | Sarakuna | Shekara |
---|---|---|
1 | Gunguma | |
2 | Matazo | |
3 | Tumsah | |
4 | Tamusa | |
5 | Suleimanu | |
6 | Maswaza | |
7 | Ɗinzaki | |
8 | Nayoga | |
9 | Kauchi | |
10 | Nawainchi | |
11 | Machikai | |
12 | Kewo | |
13 | Bahikarr | |
14 | Majidada | |
15 | Dahirahi |
s/n | Sarakunan Haɓe | Shekara |
---|---|---|
1 | Moman Abdu | 1505 – 1530 |
2 | Gudan Dan Masukanan | 1530 – 1532 |
3 | Nohirr | 1532 – 1535 |
4 | Bakwa Turunku | 1535 – 1536 |
Arziki[gyara sashe | gyara masomin]
Masana'antu[gyara sashe | gyara masomin]
Garin Zariya an san su da sana’o’i daban daban, Garin jere da kajuma suna ƙarƙashin Zariya, sun yi suna akan saƙa ta hannu.[4] Abu mai muhimmancin gaske a ƙasar Zariya shine Audiga, wanda ake ɗiba daga Zariya da kano zuwa ƙasashen turawa domin amfanin masana’antu, garin Zariya sun shahara da saƙan kayan sakawa, hula, da kuma rini.[5]
Kasuwanci[gyara sashe | gyara masomin]
Zariya gari ne, na kasuwanci da harkar noma.
Noma[gyara sashe | gyara masomin]
Allah ya ba Zariya kasar noma mai kyau.ana noma masara, doya, dawa, dauro, rake, barkono, shinkafa, dss.
Sufuri[gyara sashe | gyara masomin]
Zariya suna da hanyar sufurin jirgin ƙasa da hada Zariya da garuruwan Lagos , Kano, Abuja da kuma Kaduna (birni).[6][7]
Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]
Zyaria cibiya ce ta ilimin addini da boko, a garin ne jami'ar Ahmadu Bello ta ke, bayan ABU akwai makarantun Ilimi kusan 9 a cikin garin Zariya.Kamar; 1. Federal College of Education ((F.c.e)). 2. Nuhu Bamalli Polytechnic. 3. Ameer Shehu Idris. 4. National Institute of transport Technology((Nitt)). 5. Leather Research. 6. Narict 7. National College of Aviation((Ncat)). 8. Napri 9. Institute of Animal research((I.A.R)). Akwai kuma malaman addinin Musulunci manya kaman; 1. Sheikh Mua'azu 2. Sheikh Abdulkadir 3. Sheikh Yahuza
Da dai sauran su.
Addini[gyara sashe | gyara masomin]
Musulunci[gyara sashe | gyara masomin]
Mutanen Zariya ma fi yawansu mabiya addinin Musulunci ne.
Kiristanci[gyara sashe | gyara masomin]
Kasantuwar ma'aikatu na Gwamnatin tarayya a garin Zariya da kuma hanyoyin sufuri da yanayin kasuwanci a garin, hakan ya sa mabiya addinin Kiristiyaniti na ƙara yawa a garin.
Masana'antu[gyara sashe | gyara masomin]
Akwai masana'antu kamar su "Sunseed", Pz, dasau ransu.
Garuruwa[gyara sashe | gyara masomin]
Da a garin Zariya akwai Ganuwa, amma daga baya duk an cire su.[8][9]
Bibiliyo[gyara sashe | gyara masomin]
- Professor lavers collection: Zaria Province, Arewa House.
- Maiwada, Salihu and Renne, Elisha P. (2007) "New Technologies of Embroidered Robe Production and Changing Gender Roles in Zaria, Nigeria, 1950–2005"
- Gihring, Thomas (1984). "Intraurban Activity Patterns among Entrepreneurs in a West African Setting". Geografiska Annaler. Series B, Human Geography.
- Smith, Michael G. (1960) Government in Zazzau 1800–1950 International African Institute by the Oxford University Press, London, OCLC 293592; reprinted in 1964 and 1970.
- Dan Isaacs (28 September 2010). "Nigeria's emirs: Power behind the throne". BBC News. Retrieved 29 September 2010.
Diddigin bayanai na waje[gyara sashe | gyara masomin]
- Fayal masu alaƙa da Zaria a commons.wikimedia.org
- Asalin tushe
Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]
- ↑ http://www.britannica.com/eb/article-9078266/Zaria
- ↑ https://www.britannica.com/place/Zaria-Nigeria
- ↑ 3.0 3.1 3.2 professor lavers collection: zaria province.
- ↑ Maiwada, Salihu and Renne, Elisha P. (2007) "New Technologies of Embroidered Robe Production and Changing Gender Roles in Zaria, Nigeria, 1950–2005" Textile History 38(1): pp. 25-58, page 25
- ↑ Gihring, Thomas (1984). "Intraurban Activity Patterns among Entrepreneurs in a West African Setting". Geografiska Annaler. Series B, Human Geography. 66 (1): 19–20.
- ↑ https://www.bbc.co.uk/news/world-africa-21364541
- ↑ https://www.economist.com/news/middle-east-and-africa/21571481-renovated-railway-line-welcome-more-are-still-sorely-needed-slow
- ↑ https://web.archive.org/web/20091027035909/http://www.abu.edu.ng/bsn/zaria.php
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2009-10-27. Retrieved 2020-12-27.