Sarauniya Amina
![]() | |
---|---|
![]() | |
Rayuwa | |
Haihuwa | 1533 |
ƙasa | Zazzau |
Ƙabila | Hausawa |
Harshen uwa | Hausa |
Mutuwa | 1610 |
Karatu | |
Harsuna | Hausa |
Sana'a | |
Sana'a | Jarumi |
Imani | |
Addini | Musulunci |



Sarauniya Amina Sarauniyar Zazzau, ta rayu daga shekara ta alif 1533 zuwa shekara ta alif 1610, ɗaya ce daga cikin yara biyu da sarkin Zazzau Bakwa Turunku ya haifa. Wato ita Amina ɗin da kuma ƙanwarta mai suna Zariya. Ta yi sarautar Zazzau bayan rasuwar mahaifinta, daga shekara ta alif 1509 zuwa shekara ta alif 1522, wato shekarunta sha uku kenan a kan karagar mulki. Kuma ita ce mace ta farko da ta mulki masarautar Zazzau, kuma ta shida (6) a cikin sarakunan haɓe waɗanda sukai mulki bayan Addinin Musulunci ya fara bayyana a ƙasar Zazzau. Har ila yau a cikin jerin sarakunan Zazzau gaba ɗaya ita ce ta ashirin da uku.
Mulki
[gyara sashe | gyara masomin]Ana kallon Sarauniya Amina a matsayin mace ƴar siyasa kuma ma’abociyar al’ada wacce tayi gagarumin mulki a ƙarni na sha shida a ƙasar hausa,[1] Sarauniya Amina ta shahara matuƙa a ƙasar Hausa da ma yankunan da Daular Usmaniyya ta mulka. Ta yi kaiwa da komowa na yaƙe-yaƙe a wurare da dama. Idan aka ɗauki tun daga Zariya har zuwa Abuja akwai ƙananan garuruwa da dama da sarauniya Amina ta kafa, sai dai ba masu girma ba ne, saboda kamar dai wurare ne da ta ci zango a wajen. Jarumtarta da ƙwazonta ya kasance abin jinjina ne a ƙasar Najeriya, Afirka da kuma duniya baki ɗaya.
Dangane da batun waje ko kuma garin da Sarauniya Amina ta rasu, a gaskiya babu tabbas, to amma masana tahiri suna kyautata zaton cewa ta rasu ne a can ƙasar Gara, wato ƙasar Igala kenan, wadda ke cikin Jihar Kogi a arewacin Najeriya a halin yanzu. Wannan dalili ne ma ya sa ba a san takamaiman inda kabarin Sarauniya Amina ya ke ba.
Tatsuniyoyi da Sidney John Hogben ya ambata sun ce tana ɗaukan sabon masoyi a duk garin da ta shiga, kowannensu da safe yake gamuwa da irin rashin alheri: “An fille kan ɗan angonta kaɗan don kada kowa ya rayu ya ba da labarin".[1] A zamanin Amina, Zazzau ta mallaki yankuna fiye da kowane lokaci. Domin yin alama da kuma kare sabbin ƙasashenta, Amina ta sa aka kewaye garuruwanta da katangar ƙasa. Wadannan ganuwar ta zama ruwan dare gama gari a fadin kasar har zuwa lokacin da turawan Ingila suka mamaye birnin Zazzau a shekarar 1904, kuma da yawa daga cikinsu sun rayu a yau, wanda ake kira ganuwar Amina.[1]
Nasaba
[gyara sashe | gyara masomin]Idan aka koma ga maganar zuriyar sarauniya Amina, a gaskiya abu ne mai wuya ace ga waɗansu da suke zuriyarta ne, tun da a gaskiya yadda tarihi ya nuna, Sarauniya Amina har ta mutu ba ta yi aure ba. Don haka babu wata shaida dake nuna cewa a ciki ko wajen zazzau akwai wasu da za a iya cewa zuriyarta ne.
To sai dai duk da cewa, akwai bayanai masu sarƙaƙiya da kuma saɓani na masana tarihi a game da rayuwar sarauniya Amina, to amma dai magana mafi rinjaye ita ce; Sarauniya Amina ta taɓa wanzuwa a doron ƙasa a matsayin sarauniya a Zazzau.
Mutuwar sarauniya Amina
[gyara sashe | gyara masomin]Ba a dai san hakikanin halin da Amina ta rasu ba. Malamin addinin Musulunci a karni na goma sha tara, Dan Tafa yana cewa "Ta rasu a wani wuri da ake kira Attaagar, don haka ne masarautar Zazzau ta kasance mafi girma a cikin masarautun kasar Hausa, tunda Bauchi ta hada da yankuna da dama.[2] Da ake zantawa da Tafa, Sidney John Hogben ya ruwaito cewa, “Amina ta rasu ne a Atagara, kusa da ranar Idah, domin a lokacin Amina ta tura kan iyakar Zazzau a kudancin yankin Neja-Benue. Amma akwai sabani da yawa dangane da mutuwar ta; da yawa. mawallafa a cikin littattafansu sun kawo cewa ta rasu a Vom Jos yayin da wasu masana tarihi suka ce ta rasu a Atagara.[2]
Gado
[gyara sashe | gyara masomin]Kamar yadda masanin tarihin Birtaniya Michael Crowder ya bayyana, bayan rasuwar Amina Wata 'yar wasan kwaikwayo da ke nuna Sarauniya Amina a cikin wani wasan kwaikwayo ...Matan Hausa masu mulki sun sami raguwar tasirinsu a kai a kai kuma an hana su yancin kai. Lakabi da mukamai na gargajiya da suka shafi iko a kan mata da gyara korafe-korafensu yanzu sun zama na banza ko kuma an yi watsi da su gaba daya.[3]
Diddigin bayanai na waje
[gyara sashe | gyara masomin]Bibiliyo
[gyara sashe | gyara masomin]- Kabir, Hajara Muhammad,. Northern women development. [Nigeria]. ISBN 978-978-906-469-4.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 Kabir, Hajara Muhammad.Northern women development. [Nigeria].p.110. ISBN 978-978-906-469-4.
- ↑ 2.0 2.1 https://www.blackpast.org/global-african-history/queen-amina-1533-1610/#:~:text=Queen%20Amina%20reigned%20for%2034,Arts%20Theatre%20in%20Lagos%20State.
- ↑ https://academic.oup.com/ia/article-abstract/40/1/146/2664767?redirectedFrom=PDF