Mallam Musa
Mallam Musa |
---|
Sarki Mallam Musa shine sarkin farkon na ƙabilar Fulani inda shi ne ya assasa gidan Ƙabilar Mallawa a masarautar Zazzau. Mallam Musa yayi mulki daga shekarar 1804 zuwa shekara ta 1821. Mallam Musa ya amshi tutar Musulunci daga Mujaddadi Usman Dan Fodiyo. Mallam Musa ya amshi sarauta ne daga hannun Sarkin Haɓe (Hausa) na karshe mai suna Makau inda kuma ya kafa bangaren Daular Musulunci ta Sokoto a Zariya a karkashin tutan Shehu Usman Ɗan Fodio.[1]
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Asalin garin zaria sarakunan Haɓe ne ke mulkan su, wanda sukayi sarauta tun daga shekarar 1505 zuwa 1802, A shekarar 1804 ne Shehu Usman Ɗan Fodio yayi jihadi, inda ya yaƙi sarkin gobir mai suna Yunfa, a Yaƙin Ƙwoto, daga nan ne ya fara yaɗa sarautarsa da musulunci zuwa masarautun Hausawa, A zariya akwai Mallam Musa wanda ya daɗe yana da’awar zuwa ga addinin musulunci, Mallam Musa Bafillatani ne, Jin Jihadin Usman Ɗan Fodio yas shima ya karɓa Tuta daga Usman Ɗan Fodio. Da Mallam Musa da Yamusa mutumin fulani Barno suka doso zaria suka yaƙi sarki Makau ɗan ƙabilar Haɓe, Makau sai ya gudu shi da mutanensa zuwa Zuba, wani gari ne na Gwari da Koro a yankin Abuja a yau, Mallam Musa sai ya zama Sarkin zazzau na farko daga ƙabilar Fulani, bayan rasuwarsa sai aka kuma naɗa Yamusa a shekarar 1821 a matsyin sarkin zazzau, shi kuma fulanin Barno ne, daga nan ne Bare-Bari da Fulanin Mallawa Suka fara sarauta a kasar zazzau.[1]
Bibiliyo
[gyara sashe | gyara masomin]- Professor lavers collection: Zaria Province, Arewa House.
- The Sokoto Caliphate : history and legacies, 1804-2004. Bobboyi, H., Yakubu, Mahmood. (1st ed ed.). Kaduna, Nigeria: Arewa House. 2006. ISBN 978-135-166-7. OCLC 156890366.
- Smaldone, Joseph P. (1977). Warfare in the Sokoto Caliphate : historical and sociological perspectivesISBN0-521-21069-0OCLC2371710