Gobir

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Gobir na daya daga cikin kasashin Hausa na ainahi. Tsohuwar daular Gobir wata babbar kasace wadda ke da iyaka kamar haka: tun daga Agades daga Arewa har zanhwara daga Kudu, kuma tun daga Mayahi (Gabas) har Konni (Yamma). Kamar yada tarihi ya nuna, Gobirawa sun hitone daga gabas ta tsakiya, musamman ma daga misira, indama akeda yakinin cewa, sarakuna ukku daga cikin sarakunan misira, Gobirawa ne.