Maradi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Globe icon.svgMaradi
Maradi 2.JPG

Wuri
 13°30′N 7°06′E / 13.5°N 7.1°E / 13.5; 7.1
JamhuriyaNijar
Region of Niger (en) FassaraYankin Maradi
Department of Niger (en) FassaraMadarounfa (sashe)
Babban birnin
Yawan mutane
Faɗi 267,249 (2012)
Labarin ƙasa
Altitude (en) Fassara 385 m
Tsarin Siyasa
• Shugaban gwamnati Kassoum Mamane Moctar (en) Fassara (2011)
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci


Maradi gari ne, da ke a yankin Maradi, a ƙasar Nijar. Shine babban birnin yankin Maradi. Bisa ga ƙidayar jama'a a shekarar 2012, jimillar mutane 206,414 (dubu dari biyu da shida da dari huɗu da sha huɗu). An gina birnin Maradi a karni na sha tara haihuwan annabi Issa.


Tarihi[gyara sashe | Gyara masomin]

Asalin garin Maradi bangare ne na Katsina, masarauta ta Hausawa, ta bice daga masarautar ne a karni n 19.[1] Daga farkon karni na 19, Maradi tushe ce ta masarautun Hausa da dama, wadda wasu shugabannin da suke da asali da Daular Fulani ta Sokoto suka kafa.[2] Wasu manya a masarautar Katsina na ganin Maradi a matsayin wani sashe na masarautar su, hakanne yasa haryanzu akema sarkin Maradi lakani da "Sarkin Katsinan Maradi". Maradi tayi amfani da karfi wajen tilastama kasar Gobir wadda ke yamma da ita, Masarautar Damagaram dga gabas da kuma Sokoto daga Kudu, suka zama bangaren ta. Zuwan turawan Faransa a 1899 yayi sanadiyyar zubar da jini da kisan gilla daga yan mulkin mallaka na Voulet-Chanoine Mission, amma daga baya komi ya daidaita inda birnin yazama cibiyar kasuwanci a shekarun 1950.

maradi.

Cikin gaggawa birnin ya bazu tun a tsakiyar karni na 20. A tsakanin shekarun 1911 da 1950 birnin yacigaba da yaduwa.[3] Haryazuwa 1945, birnin Maradi na a tsakanin tsaunukan Up until 1945, Goulbi N'Maradi, wata magudanar ruwa mai tushe daga Najeriya. Asalin dadadden birnin zagaye yake da katanga wadda magabatan baya sukayi domin kare birnin daga mahara. Daga baya turawa sun canza fasalin birnin wanda hakan yayi sanadiyyar gushewar abubuwan tarihi na birnin masu dama musamman ma gine gine na birnin.[3] Faransa ta kirkiro sana'ar noman kayan sayarwa domin kara bunkasa tattalin arziki da harkokin kasuwanci. Saboda cigaban kasuwanci da tattalin arziki, a shekarun 1950 yawan mutane na ta habaka a birnin daga 8,661 in 1950 zuwa 80,000 har zuwa shekarar 1983.[3] Zuwa lokacin samun yancin Nijar a 1960, Maradi ta zama babbar cibiya ta al'adun Hausa.

A shekarar 2000 wani rikici ya barke a Maradi inda musulmai suka nuna bacin ransu biyo bayan wani biki maisuna Festival International de la Mode en Afrique (FIMA) a birnin Niamey. Hakan yayi sanadiyyar lalacewar gine-ginen da ake zaton ba na Musulunci bane, kamar Mashayu.[2][4]

Labarin kasa[gyara sashe | Gyara masomin]

Kasar Maradi, ta kai girman murabba'in kilomita 38500 kuma tana a kudancin kasar Nijar a tsakiya. Birnin Maradi na a nisan kilometa 540 daga babban birnin kasar Nijar wato Niamey. Hanyoyi da dama suna bi ta birnin Maradi ne. Kamar Hanyar Zinder, hanyar Kano da Katsina. Yanayin kasar Maradi hili ne mike wanda bai da tudu da yawa. Magudanar ruwa guda ce; wato Gulbin Maradi. Lokacin rani (wato lokacin zafi) yafi jimawa ga lokacin damina. kowace shekara a na samun ruwan saman da suke kai wa 650 a ma'aunin milimeta kowace shekara. A cikin watan mayu akan yi zafin da zai kai kimanin 33 a ma'aunin Celcius °C. Yanayin sanhi kuma yana zowa ne a watan Disamba da Januari. [5]

Yawan jama'a[gyara sashe | Gyara masomin]

Kididdiga ta bayan nan da akayi a 2012 ta nuna cewar Maradi na da yawan jama'ar da ya kai kimanin dubu dari biyu da sittin da bakwai (267 249). A shekarar 2018, alkalamomin yawan haifuwa sun nuna cewar, kowace mace a Maradi na haifuwar diya 8; wanda shine mafi girma duk duniya. Kuma Unicef ta ce kusan kashi 89 cikin dari na mata a Maradi sunyi aure ne kafin su samu shekara 18.

Tattalin arziki[gyara sashe | Gyara masomin]

Maradi ce cibiyar kasuwancin kasar Nijar. Kasuwanci, noma (musamman noman gyada, wake, hatsi, dawa da sauransu), kiwo awaki, tumaki da shanu. Wajen kiwo an san Maradi ne da wannan akuyar ja da kuma Rago Balami. Maradi na da kasuwanni kamar, babbar kasuwa, El kasuwa tsohuwa, Kasuwar Sonitan, Kadro da kuma kasuwar zamani mai suna Kalla Transa Mall. Akwai masana'antu kamar Olga oil, Niger Plastique, Matelas Enipriom, Sonitan, da sauransu.

Ilimi[gyara sashe | Gyara masomin]

A Birnin Maradi akwai Makarantu na Gomnati da makarantun allo da kuma madarissoshi na addinin Musulumci. Babbar Jami'a a Maradi ita ce Jami'ar Dan Dicko Dan Koulodo (2010). Akwai kuma Jami'ar Bouzou Dan Zambadi ko kuma Université libre de Maradi wadda aka kafa ta ne a shekarar 2004.

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. Abdourahmane Idrissa, Samuel Decalo, Historical Dictionary of Niger, Scarecrow Press, USA, 2012, p. 316
  2. 2.0 2.1 Geels, Jolijn, (2006) Bradt Travel Guide - Niger, pgs. 203-212
  3. 3.0 3.1 3.2 Les alhazai de Maradi – l’histoire d’une groupe de riche marchands saheliens. Emmanuel Gregoire. Éditions de I'ORSTOM. 1990.
  4. Saidou Arji and Noel Tadegnon (15 November 2000). "NCULTURE-NIGER: Government to Ban Islamic Groups Opposed to Fashion Festival". Retrieved 29 October 2019.CS1 maint: uses authors parameter (link)
  5. www.stat-niger.org, Le Niger en chiffres, 2018