Yankin Maradi
| Maradi (fr) | |||||
|
| |||||
|
| |||||
| Wuri | |||||
| |||||
| Jamhuriya | Nijar | ||||
| Babban birni | Maradi | ||||
| Yawan mutane | |||||
| Faɗi | 3,402,094 (2012) | ||||
| • Yawan mutane | 96.93 mazaunan/km² | ||||
| Labarin ƙasa | |||||
| Yawan fili | 35,100 km² | ||||
| Sun raba iyaka da | |||||
| Bayanan Tuntuɓa | |||||
| Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
| Lamba ta ISO 3166-2 | NE-4 | ||||





Yankin Maradi takasance daya daga cikin yankin gwamnatin ƙasar Nijar; babban birnin yankin itace Maradi.
Yankin Maradi na da girman murabba'in kilo mita 35,100, kuma yana iyaka da Arewacin Najeriya ta Kudanci da yankin Tahoua ta Yammaci, sai yankin Zinder ta Gabashi.
Kidayar shekara ta 2001 ta nuna yawan jama'ar yankin ya kai 2,235,748, wanda hakan ya nuna shi ne yanki mafi yawan jama'a wadanda yawancinsu Hausawa ne.
Akan yiwa yankin Maradi kirari da cibiyar ciyar da kasa, sabili da harkokin kasuwanci da noman da ake yi a yankin.
Yawancin abubuwan da ake nomawa a yankin domin amfani da su a cikin gida da fitarwa waje sun hada da gyada da hatsi da gujjiya, ko da yake a wasu wuraren akan noma taba da mangwaro da alkama da waken soya da ma auduga.
Duk da irin wannan kirarin da ake yiwa yankin Maradi, jama'ar yankin na yawan fama da yunwa ko Tamowa musamman a duk lokacin da aka samu karancin ruwan sama a kasar.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://www.bbc.com/hausa/news/2010/07/100721_niger_regions
