Daura

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Globe icon.svgDaura
Daura.jpg

Wuri
 13°02′11″N 8°19′04″E / 13.0364°N 8.3178°E / 13.0364; 8.3178
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaJihar Katsina
Ƙaramar hukuma a NijeriyaDaura (en) Fassara
Labarin ƙasa
Altitude (en) Fassara 474 m
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
ƴan makaranta a GDSS Daura
Ƙofar sarki Musa

Daura wata Ƙaramar hukuma ce wacce take a cikin jihar Katsina, a Arewacin Najeriya. Masarautar Daura ta hada da wasu kananan hukumomi da suke kewaye da ita wadanda suka haɗa da Daura, Ɓaure, Zango, sandamu, dutse, Mai'aduwa da kuma ita Daurar. Daura ta yi iyaka da nijar kuma tana daya daga cikin garuruwan Hausa bakwai, wadanda suka haɗa da Gobir, Biram, Katsina, Kano, Zazzau da Rano, Wanda 'yayan Bayajidda da jikokin shi suka mulka.

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Tarihin Daura ya fara ne daga lokacin da wasu mutane daga garin daura wanda take garin katsina a yanzu ƙarƙashin jagorancin wani Namangi, ya kasance mutum ne mai daraja wanda ya taɓa shan kayi a wajen takarar sarautar Daura. Ya yanke shawara ya koma da zama a wani ƙaramin gari kusa da ƙaraye, wanda ake kira ƴardozama.[1] Ya kasance yana zuwa bakin wani kogi a cikin garin inda ya gano cewa lallai wajen zai yi daɗin zama, ya samu fili a wajen kuma ya gina gida. Zai huta a gidan na wasu lokuta Sannan ya wuce ƙaraye. A haka ne har aka far kiran wajen da suna Daurawa. Wannan shine asalin tarihin ƙauyen Daura.[1] Garin baida katanga da ta zagaye shi, saboda tayi kusa da ƙaraye sosai, kuma duk lokacin da za a buga tambarin sarauta, mutanen cikin garin Daura zasu garzayo cikin ƙaraye saboda su samu tsaro. [1]

Ƙauyuka[gyara sashe | gyara masomin]

Ta haɗa iyaka da magajin gari da taurawa kafin ginin challawa gorge Dam, ƙauyen yola, ƙauyen ma, da kuma magajin hajj ta kudu, yamma, gabas da kuma arewa.

Ƙauyen Daura ya ƙunshi Gundumomi guda shida:

1-    Daura Cikin Gari

2-    Daura Mai Ruwa

3-    Gatarawa

4-    Alfawa

5-    Kwari

6- Daura Saƙo[1]

Bibilyo[gyara sashe | gyara masomin]

  • G. Karaye, Ibrahim, J. Philip, Shae. History of karaye. ISBN 978-125-341

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 G. Karaye, Ibrahim, J. Philip, Shae. History of karaye. p.p 168-169 ISBN 978-125-341