Malumfashi
![]() | ||||
---|---|---|---|---|
![]() | ||||
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jiha | Jihar Katsina | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 674 km² | |||
Bayanan tarihi | ||||
Ƙirƙira | 1975 | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Malumfashi (ko Malum Fashi ) karamar hukuma ce a Jihar Katsina, Najeriya. Hedkwatar ta tana cikin garin Malumfashi.
Tana da fadin kimanin 674 km² da yawan mutum 182,920 a bisa ƙidayar 2006. Shugaban Ƙaramar hukumar na yanzu shine Alhaji Muktar Ammani sannan kuma Mai shari'a Saddiq Abdullahi Mahuta ne Galadiman Katsina kuma Hakimin Malumfashi.
Lambar ofishin tura sakonni na yankin ita ce 822.[1]
Wakilin majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Malumfashi/Kafur shine Ibrahim Babangida Mahuta.[2]
Malumfashi tana da kyakkyawar mu'amala tsakanin al'ummar kiristoci da Musulmai Hausawa. Suna zaune lafiya da makwabtansu Hausawa da danginsu.
Fitattun mutane[gyara sashe | gyara masomin]
- Mai shari’a Saddik Abdullahi Mahuta, wanda ya fi kowa dadewa a kan mulki a jihar Katsina, daga shekara ta alif 1991 zuwa shekara ta 2013 da kuma Galadiman Katsina na 11, Hakimin Malumfashi.
- Sunusi Mamman, Vice Chancellor of Umaru Musa Yar'adua University and Sa'in Galadiman Katsina, daga ƙaramar hukumar Malumfashi.