Awka ta Kudu
|
| ||||
|
| ||||
| Wuri | ||||
| ||||
| Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
| Jihohin Najeriya | Jahar Anambra | |||
| Yawan mutane | ||||
| Faɗi | 130,664 (1991) | |||
| Bayanan Tuntuɓa | ||||
| Kasancewa a yanki na lokaci | ||||

Awka ta Kudu wata Ƙaramar Hukuma ce dake cikin Jihar Anambra, a Nijeriya. Ƙaramar hukumar ta ƙunshi garuruwa tara (9), wato Amawbia, Awka, Ezinato, Isiagu, Mbaukwu, Nibo, Nise, Okpuno da Umuawulu.[1] Awka ta Kudu tana ƙarƙashin mazabar sanatoci ta Anambra ta Arewa.[2] Akwai manyan tituna uku da suka ratsa yankin, waɗanda suka haɗa da Zik Avenue, Works Road da Arthur Eze Avenue.[3] A da, mutanen Awka ta Kudu sun shahara sosai wajen sana’ar ƙira da sarrafa ƙarfe.[4] A yau kuma ana girmama su a tsakanin al’ummar Igbo na Najeriya saboda ƙwarewarsu a fannoni na fasaha da kasuwanci. Bisa ƙidayar jama’a ta shekarar 2006, jimillar mutanen yankin ta kai 189,654.[5]
Awka wani gari ne da ke cikin Ƙaramar Hukumar Awka ta Kudu.[6] Ita ce cibiyar gwamnatin jihar kuma tana da fitattun mutane da dama a ciki da wajen Najeriya.[7][8] Amawbia kuma ita ce cibiyar gidan gwamnatin jihar, wato gidan gwamna da kuma gidan yarin jihar.[9] Garin Nise yana da muhimman cibiyoyi irin su babban ofishin WAEC (West African Examinations Council) na jihar da kuma St. Paul University College.
Al’ummar Isiagu wata gari ce da ke cikin Ƙaramar Hukumar Awka ta Kudu. Yankin yana daga cikin wuraren noma a jihar saboda yalwar ƙasa mai ni’ima da ta dace da noma. Ana kuma kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin tsoffin garuruwan yankin kudu maso gabashin Najeriya (ƙasar Igbo).
Al’ummar Isiagu sun taɓa samun sarakunan gargajiya guda biyu kacal zuwa yanzu. Sarkin gargajiyar yankin na yanzu shi ne Igwe Augustine Nwankwo, wanda ake kira Igwe Agu I na Isiagu.
Isiagu na da makarantu firamare guda biyu da makarantar sakandare guda ɗaya. Garin ya shahara da zaman lafiya da kuma ƙarfi wajen kiyaye al’adu da gargajiyarsa, kuma har zuwa yau al’ummar Isiagu suna ci gaba da riƙe al’adunsu da gargajiyarsu.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Postcodes.NG - Rural Areas in Awka South L.G.A." postcodes.naijaz.com. Archived from the original on 2025-06-29. Retrieved 2025-06-29.
- ↑ "Anambra Senatorial Districts". Centre for Community and Rural Development (in Turanci). Retrieved 2025-06-26.
- ↑ "OBI CONTINUES TO MAKE IMPACT IN AWKA". Archived from the original on 2023-10-05. Retrieved 2026-05-30.
- ↑ Headliners (2022-01-02). "Build blacksmith village in Awka, Monarch tells Anambra, Federal govts | Nigeria News Headlines Today" (in Turanci). Archived from the original on 2022-09-29. Retrieved 2022-09-29.
- ↑ "Nigeria: Administrative Division (States and Local Government Areas) - Population Statistics, Charts and Map". www.citypopulation.de. Retrieved 2025-06-30.
- ↑ Nigeria, Media (2018-04-18). "List Of Towns And Villages In Awka South L.G.A, Anambra State". Media Nigeria (in Turanci). Retrieved 2023-06-25.
- ↑ "Anambra State – SEREDEC" (in Turanci). Retrieved 2023-06-25.
- ↑ "List of Local Government Areas in Anambra State with Headquarters". Xplorer.ng (in Turanci). 2024-11-09. Retrieved 2025-06-30.
- ↑ ene (2022-08-31). "Towns & Villages in Akwa South « Anambra State « Nigeria". Towns & Villages (in Turanci). Retrieved 2023-06-25.
