Jigawa
![]() | |||||
---|---|---|---|---|---|
|
|||||
![]() | |||||
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Babban birni | Dutse | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 6,000,163 (2016) | ||||
• Yawan mutane | 259.14 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Turanci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 23,154 km² | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | jihar Kano | ||||
Ƙirƙira | 27 ga Augusta, 1991 | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Majalisar zartarwa | Majalisar zartaswa ta Jihar Jigawa | ||||
Gangar majalisa | Zauren majalisar dokokin jihar Jigawa | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Lambar aika saƙo | 720001 | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Lamba ta ISO 3166-2 | NG-JI | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | jigawanigeria.com |






Jigawa Jiha ce dake Arewa maso Yammacin Tarayyar Najeriya. An kafa jihar Jigawa ne a ranar 27 ga watan Agustan 1991 daga jihar Kano a lokacin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida. Babban birnin jihar shi ne Dutse. Jigawa ta yi iyaka da Jamhuriyar Nijar da jihohin Yobe a arewa maso gabas, Bauchi a kudu maso gabas da kudu, Kano a kudu maso yamma da kuma.
Katsina arewa maso yamma.
Tattalin Arziki[gyara sashe | gyara masomin]
Tattalin Arzikin Jihar Jigawa yana da alaƙa da ayyukan ɓangaranci na yau da kullum tare da aikin noma a matsayin babban aikin tattalin arziki. Fiye da kashi 80% na al'ummar jihar sun tsunduma cikin noma da kuma kiwon dabbobi. Ana gudanar da ciniki da kasuwanci na kanana da matsakaita, musamman a harkar noma, kiwo da sauran kayayyakin masarufi. Jigawa ta shahara a fannin Noma da kiwo, Manyan amfanin gona na jihar sun haɗa da gyaɗa, dawa, gero, shinkafa, Ridi, da kuma Zoɓo (yakuwa).a fannin kiwo kuma, Kiwon shanu, awaki, da tumaki ya yaɗu sosai a jihar.
Faɗin Ƙasa da yawan Jama'a[gyara sashe | gyara masomin]
Jihar Jigawa Tana da faɗin ƙasa kimanin muraba'in kilomita dubu ashirin da uku, da ɗari da hamsin da huɗu (23,154) da yawan jama’a kimanin miliyan biyu da dubu ɗari takwas da ashirin da tara da ɗari tara da ashirin da tara (ƙidayar yawan jama'a shekara ta 1991). Babban birnin jihar shi ne Birnin Dutse.

Jihar Jigawa tana da iyaka da jihohi huɗu dake Najeriya, su ne: jahar Bauchi, jahar Kano, jahar Katsina,da kuma Yobe. [1] [2].
Harsuna[gyara sashe | gyara masomin]

Jigawa wani sassa ne na ƙasar , a Arewa maso yammacin Nigeria .Hausa hausawa sune mafi rinjaye a jihar Jigawa sannan akwai Fulani da Mangawa da Badawa da Ngizimawa wadanda yarukan kanuri ne. Mafiyawancin su suna a ƙananan hukumomin Birniwa, Guri da Kiri kasamma.

.
Masarautu[gyara sashe | gyara masomin]
Tsarin masarautar gargajiya a Jihar ya kasu zuwa masarautu guda biyar kowacce tana da basaraken gargajiya mai suna sarki (sarki) da yake gudanarwa tare da Hakimai da dagatai da masu unguwanni suna taimaka musu. Sarakuna da Hakimai, ba kamar sauran masu rike da madafun iko ba, ba sa gudanar da harkokin siyasa, sai dai a matsayin masu kula da al’adu da masu ba gwamnati shawara kan harkokin gargajiya da na addini. Duk sarakunan masu rike da mukamai ne ajin farko.
- MASARAUTAR HADEJIA
- MASARAUTAR GUMEL
- MASARAUTAR DUTSE
- MASARAUTAR RIGIM
- MASARAUTAR KAZAURE
GWAMNONI[gyara sashe | gyara masomin]
https://en.m.wikipedia.org/wiki/List_of_governors_of_Jigawa_State
Ƙananan Hukumomi[gyara sashe | gyara masomin]
Jihar Jigawa tana da ƙananan Hukumomi guda ashirin da bakwai (27). Kananan Hukumomin kuwa su ne:
- Auyo.
- Babura.
- Biriniwa.
- Birnin Kudu
- Buji.
- Dutse.
- Gagarawa.
- Garki.
- Gumel.
- Guri.
- Gwaram.
- Gwiwa.
- Hadejia.
- Jahun.
- Kafin Hausa.
- Kaugama.
- Kazaure.
- Kiri Kasama.
- Kiyawa.
- Maigatari.
- Malam Madori.
- Miga.
- Ringim.
- Roni.
- Sule Tankarkar.
- Taura.
- Yankwashi.
-
Masarautar Gumel
-
Masarautar Dutse
-
Masarautar Ringim
-
Masarautar Hadejia
-
Masarautar Kazaure
Bibiliyo[gyara sashe | gyara masomin]
- Bello, Ahmadu, Sir, a shekara ta 1910-1966. (1999). Alhaji Sir Ahmadu Bello, Sardauna of Sokoto : his thoughts and vision in his own words : selected speeches and letters of the great leader. Nchi, Suleiman Ismaila, Mohammed, Samai̕la Abdullahi. Makurdi: Oracle. ISBN 978-34637-2-1. OCLC 44137937.
Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]
- ↑ https://www.britannica.com/place/Jigawa
- ↑ https://www.familysearch.org/wiki/en/Jigawa_State,_Nigeria_Genealogy
- ↑ "Nigeria". Ethnologue (22 ed.). Retrieved 2020-01-10.
Jihohin Najeriya |
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara |
/gallery>
Bibiliyo[gyara sashe | gyara masomin]
- Bello, Ahmadu, Sir, a shekara ta 1910-1966. (1999). Alhaji Sir Ahmadu Bello, Sardauna of Sokoto : his thoughts and vision in his own words : selected speeches and letters of the great leader. Nchi, Suleiman Ismaila, Mohammed, Samai̕la Abdullahi. Makurdi: Oracle. ISBN 978-34637-2-1. OCLC 44137937.