Bauchi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Bauchi (asali Yakoba) birni dake a arewa maso gabashin Najeriya, cibiyar gudanarwa ta jihar Bauchi da kuma masarautar Bauchi ta gargajiya na ƙaramar hukumar Bauchi a cikin wannan jihar. Ƙaramar hukumar tana da faɗin ƙasa kilomita 3,687Jahar na iyaka da Kano da Jigawa daga arewa, Plateau atsayin mita 616 daga kudu, Gombe da Yobe daga gabas, Kaduna ta yamma. Ya samo sunansa daga garin Bauchi mai ɗimbin tarihi, wanda kuma ke zama babban birninsa. An kafa jihar ne a shekarar 1976 lokacin da aka wargaza tsohuwar jihar Arewa maso Gabas. Asalin garin ya haɗa da yankin da a yanzu ya zama jihar Gombe, wanda ya zama jiha ta daban a shekarar 1996.

Jihar Bauchi tana da ƙabilu masu yawa, wanda sunkai ƙabilu 55 da suka hada da Fulani, Gerawa, Sayawa, Jarawa, Kirfawa, Turawa Bolewa, Karekare, Kanuri, Fa'awa, Butawa, Warjawa, Zulawa, Boyawa MBadawa. Amma Fulani su ne babbar ƙabila. Wannan yana nufin cewa suna da asali, tsarin sana'a, imani da sauran abubuwa da yawa waɗanda ke cikin kasancewar al'ummar jihar.

Akwai kamanceceniya na al'adu a cikin harshen mutane, ayyukan sana'a, bukukuwa, sutura da kuma yawan mu'amalar kabilanci musamman wajen zaman aure da tattalin arziki. Wasu daga cikin ƙabilun suna da alaƙar barkwanci da ke tsakanin su, misali; Fulani da Kanuri, Jarawa da Sayawa, da sauransu.

Bikin Daba (Durbar) babban abin jan hankali ne na shekara-shekara[1]


Birnin Bauchi na cikin ƙananan hukumomi ashirin da ke jihar Bauchi:

Bauchi, Tafawa Balewa, Dass, Toro, Bogoro, Ningi, Warji, Ganjuwa, Kirfi, Alkaleri, Darazo, Misau, Giade, Shira, Jamaare, Katagum, Itas/Gadau, Zaki, Gamawa da Damban.[2]


Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "A 100-Year-Old Muslim Festival of Horse Riding"
  2. "Bauchi State List of Local Governments Zip codes | Nigeria Zip Codes"