Karekare

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search


Karekare ko kuma Karaikarai kamar yadda ake furta sunan ƙabilar /Ka'rai'Ka'rai/. Daya ne daga manyan harsunan arewa maso gabashin Najeriya. Mafi girman sashen da al'ummu masu wannan harshen suke da zama sun hada da jihar Yobe da kuma Bauchi. Garin Jalam dake karamar hukumar Dambam a jihar Bauchi shi ne babban birni mafi tsufa da kuma dadewa daga garuruwan al'ummar Karaikarai kuma a cikin shi wannan gari ne ake gudanar da manyan bukukuwan al'ada na al'ummar Karaikarai da suka hada da bikin Bala baràà ma Jalam a filin wasa da sukuwa dake kofar fadar mai martaba sarkin Jalam HRH Alhaji Saleh Ibn Muhammad Nyako.

Bara ma jalam rawa.jpg

Tarihi[gyara sashe | Gyara masomin]

Tarin bayanai da aka tattara daga bincike da kuma tarihi na zantukan baka da dama sun bayyana asalin al’ummar Karaikarai da samuwar harshen su. Daya daga cikin fitattu a jerin wadannan bayanan shi ne wanda Adamu A.A ya wallafa a littafinsa mai suna Takaitaccen Tarihin Al’ummar Karaikarai inda ya bayyana cewa asali al’ummar Karaikarai sun fito ne daga tsatson sarauta na gidan Tabba’ui Awal na ƙabilar Banu Humaira dake ƙasar Yemen wadda take yankin yammacin daular larabawa. Bayanin yayi nuni da hakan a matsayin tushen samuwar al’ummar Karaikarai din da aka sani a yau.

Sai dai kuma a ra’ayin Batten kamar yadda ya rubuta tashi ruwayar a cikin littafinsa cewa yayi, al'ummar Karaikarai tsatso ne na jinsin larabawa mazauna yankin gabas ta tsakiya inda kuma tsohon birnin su wani gari ne a daular Misira wato ƙasar Masar. Bayanin ya kuma dora da cewa asali kuma al’ummar Karaikarai kafin zamanin zamansu a Masar sun fito ne daga yankin nahiyar Asiya wato yankin da aka yi imanin cewa can ne mafarin samuwar dukkanin wasu dadaddun kabilu da harsuna na jinsin Dan Adam. Wato abinda Batten yake kokarin nunawa anan shi ne, al’ummar Karaikarai da harshen su na daga jerin dadaddun al’ummar da suka fara wanzuwa a doron duniya.

Shi ma Mai Madubi kamar yadda A.B. Hassan ya kattaba a na shi littafin kusan yana da ra’ayi iri daya da na A.A. Adamu cewa asali al’ummar Karaikarai tsatson larabawan daular Yemen ne. Amma kuma bayanin na sa ya dora da cewa bayan da labarin kafuwar garin Fustat dake daular Masar ya riski al’ummar Karaikarai a mazaunin su dake kasar Yemen wanda kuma shugaban rundunar musulmi masu yakin jihadi da suka fito daga kasar ta Yemen din ne ya kafa garin wato Amr ibn al-'As a shekara ta 641AD an samu wasu daga daga cikin al’ummar Karaikarai da suka kaura izuwa wancan garin na Fustat inda suka cigaba da rayuwa anan tare da sauran al’ummun da suka tafi tare da su daga Yemen wanda hakan ya sanya kaso mafi yawa daga al’ummar da suka fara zama a birnin duk sun kasance ‘yan asalin kasar Yemen ne sai kuma wasu al’ummun da su kuma suka fito daga yankin gabas ta tsakiya wadanda suka hada da mutanen daular Romawa, Hibirawa daga kasar isra’ila da kuma Yahudawa wanda duk suka hadu suka cigaba da rayuwa a wannan garin na Fustat har izuwa zamanin rushewarsa a shekara ta 1168 sakamakon farmaki na wani yaki daga daular Rum. Wannan bayani ya zo daidai da ruwayar da babban kundin adana tarihin duniya ya kattaba.

Ƙarin wani abin sha’awa game da tarihin al’ummar Karaikarai shi ne ba a samu bambance-bambancen a zo gani ba dangane da bayanan da aka kattaba da kuma wadanda aka samo na daga tarihin zantukan baka. Abu mafi daukar hankalin kuma shi ne yadda bakin daukacin masana tarihin ya zo daya ta fuskar bayanin su na cewa noma ne sana’ar da al’ummar Karaikarai suka fi yin fice akai. Hakan kuwa ya zo a cikin littafin da A.B. Hassan ya rubuta inda yake bayyana cewa, bayan al’ummar Karaikarai sun shiga garin Fustãt ba su manta da sana’ar su ta gado ba wato ‘noma’ wadda suka gada tun kaka da kakanni a kasar su ta Yemen.

Daga cikin dadaddun abubuwan da tarihi ya nuna cewa al’ummar Karaikarai sun dade suna nomawa tun a wancan zamanin da suke Yemen shi ne noman gangala (gurjiya/mai ƙoƙo) wadda a harshen Karaikaranci ake kiranta da suna Dibèèràu. Sai dai a lokacin da suka shiga daular Misira tarihi ya nuna cewa sun tarar da mutanen wannan yanki wadanda tuntuni suka gabace su zuwa wajen suna noman gyada wadda a gabannin zuwan al’ummar Karaikarai wannan wajen a baya can ba su san wannan iri na gyadar ba sai a zamanin wannan tafiyar da suka yi zuwa garin Fustat.

Bisa wannan dalili ne kuma sai Karaikarai suka sanyawa shi wannan bakon irin wato ‘gyada’ suna Dibèèràu ta Masar, yayin da ita kuma gurjiya sai suka kara mata kalmar Jagàu. Daga nan ne kuma aka samo sunayen wadannan iri guda biyun a harshen Karaikarai wato gyada da kuma gurjiya inda ake kiran su da suna Dibèèràu tà Masar wanda ma’anar sunan yana nufin ‘gyadar kasar Masar’ ita kuma Dibèèràu tà Jagàu ma’anar sunan shi ne ‘gyadar gida’.

Ƙarin bincike da nazarce-nazarce akan al’ummar Karaikarai sun kara bada tabbaci kan sahihancin wadancan zantuka da aka kattaba a littattafan tarihi da dama har da ma wadanda na ambata cewa sun samu ne ta hanyar zantukan baka wanda tsofaffi kan bayar akan wannan al’umma da ake kira da Karaikarai.

Daga cikin muhimman abubuwa daga jerin bayanan da na samo a sakamakon binciken da na gudanar na kuma tattara shi a dan wannan rubutun kuwa shi ne, a karshe an gano cewa akwai kusanci da kuma kamanni ta fuskar al’adu, yanayin zamantakewa, da tsarin tafiyar da mulki da kuma kusancin harshe a tsakanin al’ummar Karaikarai da kuma al’ummun daular larabawa mazauna yankin gabas ta tsakiya.

Duniyar masana ilimin harsuna da ta masu ilimin tarihi sun yi amanna cewa cudanya da zamantakewa a tsakanin al’ummu masu al’adu daban-daban tana yin tasiri ga junan su inda a karshe hakan kan kawo musanyar dabi’u, al’adu da ma sauyin harshe ta hanyar aron kalmomi da kuma amfani da sabbin kalmomi daga wani harshen zuwa wani wanda kuma ta hanyar hakan ne ake samun fadaduwa da kuma bunkasar harshe har ma ci gaban sa.

Nazarin kuma ya sake nuni da cewa a wasu lokutan ma wannan ire-ire na shi wannan tasirin da wani harshen kan yi akan wani kan iya zama sanadi na bacewar harsunan da ba su da karfi kamar dai yadda ya faru akan harsunan duniya da dama bisa nisan tafiya a cudanya da kuma juyawar zamani.

Bayan gudanar da bincike na masana tarihi da suka gabata an gano cewa kamar yadda wani harshen kan yi tasiri akan wani, haka harshen larabci da kuma hibiranci (yaren al’ummar kasar isra’ila) da al’adunsu suka yi matukar tasiri akan na al’ummar Karaikarai da kuma harshen Karaikarainci wanda saboda karfin wannan tasirin nasu akan al’ummar ne ya sanya har izuwa wannan lokaci ake cigaba da samun tarin wasu abubuwan da dama wanda har kwanan gobe al’ummar Karaikarai din ba su rabu da su ba, asali ma sun zamo sashe ne na al’adun Karaikarai din wanda ake amfani da su wajen bambance su daga wasu kabilun a duk inda suka tsinci kan su.

An danganta wannan tasiri da harsunan al’ummar larabawa mazauna yankin gabas ta tsakiya suka yi akan al’ummar Karaikarai da cewa akwai yiwuwar ya faru ne tun a zamanin da suka yi rayuwa a garin Fustat na tsohuwar daular Masar kimanin shekaru dubu da dari biyar (1,500) baya.

Misali daga jerin wadannan tasiri da harsunan mutanen gabas ta tsakiya suka yi akan al’ummar Karaikarai da kuma harshen su shi ne yadda aka gano kamanni tsakanin sunayen gargajiya na al’adar Bakarkarai da kuma na larabawan yankin gabas ta tsakiya wato masu harshen larabci da kuma Hibiranci wadanda mazauna ne a kasar isra’ila da wasu sassa na kasashen Jodan da wasu yankuna dake kan iyakar kasar falasdinu a wancan lokaci.

A binciken an gano yadda wasu sunaye na wadancan larabawan suka zamo iri daya sak da irin sunayen gargajiya na Bakarkarai ba tare da an samu bambanci a yanayin yadda ake furucin su ba ko kuma a yadda ake rubuta su da harsunan ko kuma bambanci a irin jinsin da ake amfani da su ba. Ma’ana sunan da ake kiran namiji da shi a can nahiyar larabawan gabas ta tsakiya idan aka zo cikin al’ummar Karaikarai namiji za a tarar ana kira da irin wannan sunan haka idan sunan mace ce ake kira da shi a can daular larabawan ma mace za’a tarar ana kira da irin wannan sunan. Ga kuma wasu misalan daga ire-iren wadancan sunayen wanda aka gano cewa da larabawan gabas ta tsakiya da kuma Karaikarai sun yi tarayya akai wajen amfani da su.

Ma’anonin da na bayar anan irin ma’anonin da sunayen suke da su ne a can daular larabawa. A bangaren sunayen maza akwai irin su Aleh = ganye, Saaban/Saban = makeri, Ari = Zakin Allah, Udeh = mai yabon Ubangiji, Malo = mai nasara, Dale = kogi, Jalam = mai zurfin ciki dasauran su. A bangaren sunayen mata kuwa akwai irin su Bibale = abar so, Malecka = sarauniya da kuma dasauransu. Amma ga al’ummar Karaikarai suna Malecka ana iya amfani da shi ga jinsin namiji ko mace.

ƙabilu[gyara sashe | Gyara masomin]

Al'ummar Karaikarai sun rarrabu izuwa manyan azuzuwa ko kabilu guda uku;

Jalalum

Akwai ƙabilar da ake kira Jalalum (Jalamawa) wadanda ake kira da Karaikaran yamma kuma ana samun su ne a jihar Bauchi da kuma yankunan jihar Jigawa da wasu sassan jihar Kano amma ainihin cibiyar su shi ne garin Jalam dake jihar Bauchi. Sarkin Jalam Saleh Ibn Muhammad Nyako shi ne babban shugaban ƙabilar Jalalum ko Jalamawa kamar yadda ake kiran su.

Birkaì ko Birkayì

Su ma wadannan rukuni ne daga azuzuwan ƙabilar Karaikarai da ake kiransu da suna Karaikaran arewa. Ana samun wannan ƙabilar ne a yankin kudancin jihar Yobe. Wadannan Karaikarai baki dayan su suna mubaya'a ne ga Masarautar Tikau wato babban jagoransu shi ne mai martaba Alhaji Muhammadu Abubakar Ibn Grema Mai Tikau.

Pakaràu Pakarò

Su kuma ƙabilar Karaikaran da ake Kira da Ngwajum su ne Karaikaran gabas da Jalalum wadanda ake samu a yankin karamar hukumar Fika dake jihar Yobe.Har wayau ana kiran wannan kabila da suna Ngwajum

Karekare /ka'rai'ka'rai/
Yawan mutane a kidayar 1952 50,000
Yawan mutane a kidayar 1963 129,000
Karfin yawan mutane a shekarar 1987 na 33rd a jerin kabilun Najeriya
Yawan mutane a kidayar 2006 1,000,406
ƙiyasin yawan mutane a yanzu 3,040,796 a duniya

Rubutu[gyara sashe | Gyara masomin]

Harufan da ake rubutu na Karakarai
Manyan baƙaƙe A B Ɓ C D Ɗ E G H I J K L M N O P R S T U V W ʼW Y ʼY Z
Kananan baƙaƙe a b ɓ c d ɗ e g h i j k l m n o p r s t u v w ʼw y ʼy z

Har wa yau Karaikarai su na da bakake masu dori da suka hada da: dl, hn, tl, zh.

Akwai wasula guda goma sha daya a harshen Karaikaranci
Wasulan Karaikaranci a á à o ò e è i ì u úKalmomi[gyara sashe | Gyara masomin]

Kalmomin Karaikarai da Hausa da Turanci:[1][2]

Karaikarai Hausa Turanci
bai mălà duniya the world
bai baya back
bå kùlè wanzami barber
bakta yadi cloth
bārìmè makami weapon
bārìmè makami weapon
bàru tattabara pigeon
bàyā aya tiger nuts
băyă dukiya wealth
bìdò biri monkey
bikùrù gumi sweat
cącą labari news
bārìmè makami weapon
càfā kanwa potash
càlum inuwa shade
càmò soyayya love
bārìmè makami weapon
càn kawu uncle
bārìmè makami weapon
cānà musu argument
capkarā matsefi comb
cēwì tsuntsu bird
cìdàm iri seed
dabè karaya fracture
dàbi dinya black plump
dādàkà kira forging
dāgwàlò kunu pap

Al'ada[gyara sashe | Gyara masomin]

Abinci[gyara sashe | Gyara masomin]

Tufafi[gyara sashe | Gyara masomin]

Sana'a[gyara sashe | Gyara masomin]

Bukukuwa[gyara sashe | Gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]


https://www.mujallaradabi.com/2020/04/karaikarai-yaren-da-ke-kama-da-na.html?m=1

External links[gyara sashe | Gyara masomin]

  • Doris Löhr, H. Ekkehard Wolff (with Ari Awagana). 2009. Kanuri vocabulary. In: Haspelmath, Martin & Tadmor, Uri (eds.) World Loanword Database. Leipzig: Max Planck Institute for Evolutionary Anthropology, 1591 entries.
  • Ari Awagana, H. Ekkehard Wolff (with Doris Löhr). 2009. Hausa vocabulary. In: Haspelmath, Martin & Tadmor, Uri (eds.) World Loanword Database. Leipzig: Max Planck Institute for Evolutionary Anthropology, 1668 entries.