Malam Madori
|
| ||||
|
| ||||
| Wuri | ||||
| ||||
| Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
| Jihohin Najeriya | Jihar Jigawa | |||
| Yawan mutane | ||||
| Faɗi | 164,791 (2006) | |||
| • Yawan mutane | 215.13 mazaunan/km² | |||
| Labarin ƙasa | ||||
| Yawan fili | 766 km² | |||
| Bayanan Tuntuɓa | ||||
| Kasancewa a yanki na lokaci | ||||

Malam Madori Karamar Hukuma ce dake a cikin Jihar Jigawa, Arewa maso yamman Nijeriya. Ƙaramar hukumar Malam Madori tana a ƙarƙashin Masarautar Hadejia ne, dake a cikin Jihar Jigawa.

Karamar hukumar Malam Madori tana da mazaɓu goma sha ɗaya a ƙarƙashin ta.
MAGANAR HAUSA DA MANGANCI A GARIN MALLAM MADORI
[gyara sashe | gyara masomin]Mangawa ƙabila ce ta bare-bari. Shi kuwa harshen manganci kuwa karin harshe ne daga cikin kare-karen harshen managanci da ya haxa da Bare-bari na Tsakiya (Central Kanuri ), da Mangawa, da kuma Tumori. Harshen kanuri wanda Hausawa ne suke kiran sa da barbaric, qabilar kuma su ake kira da bare-bari, ya samo asali ne daga Daular Borno da ke yankin kogin Chadi. Hasali ma su suka mamaye wannan yanki. Galibi Harshen Hausa da Larabci shi ne harshe na biyu a wajen Mangawa da bare-bare, sannan suma suna amfani da haruffan ajami wajen rubutu.
Idan aka yi la’akari da tarihin Malam madori da Birniwa wanda zai zo a qasa, za a ga cewa mangawa ne asalin waxanda suka kafa garuruwa su ne bare-bari, don haka za a iyakance zuwan Mangawa qaramar Hukumar Malam madori.
