Anaocha
| Igbo (ig) | ||||
|
| ||||
| Wuri | ||||
| ||||
| Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
| Jihohin Najeriya | Jahar Anambra | |||
| Yawan mutane | ||||
| Faɗi | 284,215 (2006) | |||
| Tsarin Siyasa | ||||
| Majalisar zartarwa |
supervisory councillors of Anaocha local government (en) | |||
| Gangar majalisa |
Anaocha legislative council (en) | |||
| Bayanan Tuntuɓa | ||||
| Kasancewa a yanki na lokaci | ||||


Anaocha wata karamar hukuma ce da ke Anambra, a yankin kudu maso gabashin Najeriya. Garuruwan da suka haɗa ƙaramar hukumar sun haɗa da Aguluzigbo, Agulu, Neni, Ichida, Adazi-Ani, Adazi-Enu, Adazi-Nnukwu, Akwaeze, Nri da Obeledu, yayin da hedikwatar ƙaramar hukumar take a Neni.[1] Ƙaramar Hukumar Anaocha tana ƙarƙashin mazabar sanatoci ta Anambra ta Kudu a Jihar Anambra.[2] Bisa ƙidayar jama’a ta shekarar 2006, jimillar mutanen yankin ta kai mutane 284,215.As at the 2006 census, this LGA has a total population of 284,215 people.[3]
Tattalin arziki
[gyara sashe | gyara masomin]Masana’antar noma a Ƙaramar Hukumar Anaocha tana bunƙasa sosai, inda ake noma dimbin amfanin gona irin su ƙocoyam, doya da rogo. Wata muhimmiyar sana’ar tattalin arziki a yankin ita ce sarrafa itace. Haka kuma, mazauna yankin suna gudanar da harkokin kamun kifi da kasuwanci, yayin da fitattun kasuwanni irin su Kasuwar Eke da ke Adazi-Ani, Kasuwar Afor da ke Agulu da kuma Kasuwar Nkwor da ke Adazi-Enu ke taimakawa wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙaramar hukumar.[4]
Ƙasa da Yanayi
[gyara sashe | gyara masomin]Ana ganin matsakaicin zafin jiki na Ƙaramar Hukumar Anaocha ya kai digiri 27.5 a ma’aunin Celsius, tare da matsakaicin danshin iska na kashi 79 cikin 100. Yankin na da manyan yanayi biyu, wato lokacin rani wanda ke gudana daga watan Nuwamba zuwa Maris, da kuma lokacin damina wanda yake daga watan Afrilu zuwa Oktoba.[5]
Fitattun mutane
[gyara sashe | gyara masomin]- Emeka Nwokedi — jagoran ƙungiyar waƙa kuma darektan kiɗa
- Peter Obi — tsohon gwamnan Anambra State
- Basil Ezeanolue — farfesa a fannin ilimin cututtukan kunne, hanci da maƙogwaro (Otorhinolaryngology)[6]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "List of Local Government Areas in Anambra State with Headquarters". Xplorer.ng (in Turanci). 2024-11-09. Retrieved 2025-06-30.
- ↑ "Anambra Senatorial Districts". Centre for Community and Rural Development (in Turanci). Retrieved 2025-06-26.
- ↑ "Nigeria: Administrative Division (States and Local Government Areas) - Population Statistics, Charts and Map". www.citypopulation.de. Retrieved 2025-06-30.
- ↑ "Anaocha Local Government Area". www.manpower.com.ng. Retrieved 4 October 2023.
- ↑ "Anaocha Local Government Area". www.manpower.com.ng. Retrieved 4 October 2023.
- ↑ "People - Anaocha". Anaocha (in Turanci). Archived from the original on 2024-11-19. Retrieved 2025-06-28.
