Kano (jiha)
![]() | |||||
---|---|---|---|---|---|
|
|||||
![]() | |||||
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Babban birni | Kano | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 16,076,892 (2016) | ||||
• Yawan mutane | 798.61 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Turanci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 20,131 km² | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Arewacin Najeriya | ||||
Ƙirƙira | 27 Mayu 1967 | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Majalisar zartarwa | Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano | ||||
Gangar majalisa | Zauren yan majalisar dokokin Jihar Kano | ||||
• Gwamnan jihar Kano | Abdullahi Umar Ganduje | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Lamba ta ISO 3166-2 | NG-KN | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | kanostate.net |

Jihar Kano jiha ce da take a Arewa Maso Yammacin kasar Najeriya.[1] Tana da yawan fadin kasa kimanin kilomita murabba’i 20,131 da yawan jama’a miliyan sha ɗaya da dubu hamsin da takwas da dari uku (a kiyasin shekarar 2011). Babban Birnin jihar shi ne Birnin Kano. Abdullahi Umar Ganduje ne gwamnan jihar tun daga zaben shekarar 2015 har zuwa yau. Ya sami matakin zama gwamna ne a jam'iyyar ''All Progressive Congress'' (APC). Mataimakin gwamnan shi ne Nasiru Yusuf Gawuna. Aminu Ado Bayero shi ne Sarkin Kano daga ranar 9 ga watan Maris, 2020 zuwa rana maikamar ta yau. Dattijan jihar sun hada da; Aminu Kano, Maitama Sule, Sani Abacha, Murtala Mohammed, Sanusi Lamido Sanusi, Ibrahim Shekarau, Isyaka Rabi'u, Aliko Dangote, Rabiu Musa Kwankwaso, Barau I Jibrin da Kabiru Ibrahim Gaya.
Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]
An kafa Jihar Kano shekara ta takwas bayan Najeriya ta samu kyancin kai, wato a shekara ta 1968. Jihar Kano tana da iyaka da jihohi huɗu, su ne: Kaduna, Katsina, Jigawa da kuma Bauchi. Ana yi wa Jihar Kano kirari da "Kano ta dabo tumbin giwa ko da me ka zo an fika", wannan kirari yanada alaka da kasancewar Jihar Kano cibiyar kasuwanci ta Arewacin Nijeriya. Aminu Ado Bayero shi ne sarkin Kano.
Kano ne birnin da ya fi kowane birni yawan musulmi a Najeriya.[2]
Ƙananan hukumomi[gyara sashe | gyara masomin]
Kano tana da ƙananan hukumomi guda 44, su ne kamar haka:
Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]
- ↑ "About Kano". Kano State. 2017-12-30. Archived from the original on 2020-05-19. Retrieved 2020-05-19.
- ↑ [1]
Jihohin Najeriya |
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara |
Tarihin Kano a takaice: dw.com/ha/kano/t-19218481