Jump to content

Nasiru Gawuna

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Nasiru Gawuna
Rayuwa
Haihuwa Nasarawa, 6 ga Augusta, 1967 (57 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Nasiru Yusuf Gawuna (an haife shi 6 ga Agusta a shekara ta 1967 a karamar hukumar Nasarawa, a jihar Kano) mataimakin gwamnan jihar Kano ne mai ci daga watan Mayu a shekara ta 2019 (bayan Hafiz Abubakar). ma'aikacin lafiya ne na Najeriya, ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa.[1] A watan Mayun 2022, ya zama dan takarar gwamna na jam'iyyar All Progressives Congress a zaben gwamnan jihar Kano a 2023.[2]. Ya taba zama mataimakin gwamnan jihar Kano a karkashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje daga 2018 zuwa 2023.[3]

An haifi Nasir Yusuf a ranar 6 ga Agusta 1967, ga iyalan Alhaji Yusuf da Hajiya Fatima, a cikin birnin Kano. Shi zuriyar Garba Gawuna ne da kuma iyalan Sheikh Hassan Gawuna bisa zuri’ar uba da na uwa bi da bi.

Nasiru Gawuna ya shiga makarantar firamare ta Gawuna a shekarar 1973. Ya kammala makarantar firamare ta Gawuna a shekarar 1979, kuma a shekara ta gaba ya shiga makarantar Sakandiren Gwamnati Gwaram (yanzu a jihar Jigawa) inda ya yi karamar sakandare. Bayan ya kammala karatunsa na Sakandare a Makarantar Kimiyya ta Dawakin Kudu a shekarar 1984, ya samu gurbin shiga Makarantar Koyon Ilimi ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya na tsawon shekara daya. Ya kammala karatun share fage a shekarar 1985.[4]

Daga nan sai ya wuce Jami’ar Usman Danfodiyo, inda ya kamala a shekarar 1990 da digiri a fannin Biochemistry.[5]

Sana'ar siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya nada Nasir Yusuf Gawuna[6] bayan murabus din tsohon mataimakin gwamna Farfesa Hafiz Abubakar[7] a ranar 5 ga watan Agusta 2018, Gwamna Ganduje ya kuma rike Gawuna a matsayin abokin takararsa a babban zaben Najeriya na 2019.[8] Kafin nada shi Gawuna ya kasance Kwamishinan Ma’aikatar Gona ta Jihar Kano, tun shekarar 2014 tsohon Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Kwankwaso ne ya fara nada shi kwamishina.[9]

Gawuna shi ne Shugaban Kwamitin Taskforce na Jihar Kano kan Covid-19[10]

Ya kasance shugaban karamar hukumar Nassarawa na tsawon shekaru 8 a karkashin rusasshiyar jam’iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP) yayin da Ibrahim Shekarau ya kasance gwamnan jihar Kano yana aiki da dukkanin gwamnonin jihar guda uku.[11]

Gawuna a wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa Hassan Musa Fagge ya fitar a ranar 18 ga Afrilu 2022 ya yi murabus daga mukamin kwamishinan noma da albarkatun kasa[12]. domin ya samu damar shiga takarar gwamnan jihar Kano a 2023. Gwamnan jihar Kano mai ci Abdullahi Umar Ganduje ya goyi bayan Gawuna ya zama magajinsa a babban zaben Najeriya na 2023.[13] Gwamna Ganduje ya bayyana matakin nasa ne a taron masu ruwa da tsaki a ranar Asabar 7 ga Mayu 2022.[14]

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.


  1. "Tinubu Appoints Gawuna, Akande, Suleiman, 557 others as Chairmen, members of governing councils of federal tertiary institutions". nairametrics.com. 15 June 2024. Retrieved 31 August 2024.
  2. Bello, Bashir (8 May 2022). "Kano 2023 Guber: Ganduje anoints deputy, Gawuna as successor". Vanguard. Retrieved 9 May 2022. 
  3. Murtala, Abdulmumin (19 September 2018). "Kano Deputy Governor, Gawuna sworn-in". Vanguard. Retrieved 29 August 2024.
  4. "Ganduje picks deputy as preferred successor". Daily Trust. 8 May 2022. Retrieved 9 May 2022.
  5. "PROFILE: Kano APC governorship candidate, Nasiru Gawuna - SolaceBase". 6 March 2023. Retrieved 11 July 2024.
  6. "Kano Assembly confirms Gawuna as Deputy Governor". 18 September 2018. Retrieved 29 August 2024.
  7. Ogundipe, Samuel; Ibrahim, Nasir (5 August 2018). "JUST IN: Kano Deputy Governor Hafiz Abubakar resigns". Premium Times. Retrieved 29 August 2024.
  8. "2019: I'll retain Gawuna as running mate – Ganduje". Blueprint. 21 September 2018. Retrieved 29 August 2024.
  9. "Executive Council". Archived from the original on 6 July 2018. Retrieved 21 September 2017.
  10. "Kano relaxes lockdown for one day". TODAY. 22 April 2020. Archived from the original on 29 April 2020. Retrieved 9 January 2021.
  11. Giginyu, Ibrahim Musa (10 October 2020). "COVID-19: Over 35, 000 people to benefit from MSME survival fund in Kano". Daily Trust. Retrieved 9 January 2021.
  12. Bello, Bashir (18 April 2022). "Gale of resignations hit Kano as Chief of Staff, 4 other Commissioners resign". Vanguard. Retrieved 9 May 2022.  Opejobi, Seun (20 April 2022).
  13. "2023: APC announces date for presidential primaries, adopts indirect method". Daily Post. Retrieved 9 May 2022.
  14. "Ganduje picks deputy as preferred successor". Daily Trust. 8 May 2022. Retrieved 9 May 2022.