Aminu Kano
An taskan ce wannan muƙalar a cikin jerin Muƙaloli_masu_kyau a Hausa Wikipedia
Ana sa ran wata rana wannan muƙalar zata kasance a Babban Shafin Muƙalar mu a yau |
Aminu Kano | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | jahar Kano, 9 ga Augusta, 1920 | ||
ƙasa |
Najeriya Mallakar Najeriya | ||
Ƙabila | Fulani | ||
Harshen uwa | Fillanci | ||
Mutuwa | 17 ga Afirilu, 1983 | ||
Karatu | |||
Makaranta |
UCL Institute of Education (en) Kwalejin Barewa Kwalejin Rumfa Kano | ||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya Hausa | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa, Malami, scholar (en) , marubuci da maiwaƙe | ||
Employers |
Federal Ministry of Communications, Innovation and Digital Economy (en) Ma’aikatar Lafiya ta Tarayyar (Najeriya) | ||
Wanda ya ja hankalinsa | Sa'adu Zungur, Mahatma Gandhi da Usman Dan Fodiyo | ||
Imani | |||
Addini | Musulunci | ||
Jam'iyar siyasa |
People's Redemption Party (en) Northern Elements Progressive Union Majalisar Jama'ar Arewa |
Malam Aminu Kano (An haife shi a shekara ta alif dubu daya da ɗari tara da ashirin (1920) miladiya- ya rasu a ranar 17 ga watan afrilu, shekara ta alif dubu daya da ɗari tara da tamanin da uku (1983) Miladiyya Ac. Dan siyasa ne mai matuqar kima, kuma ya yi yaki sosai don kare hakkin yan kasa a Najeriya. Kamar yadda siyasarsa ta nuna, ta hanyar goyon bayan dimukuradiyya, tallafawa mata da kuma goyon baya ga 'yancin furuci kuma yana daga cikin mutanen da sukayi yaqi wajen neman 'yancin kasa a wancan lokaci. Yana daga cikin wadanda suka jogoranci mutane wajen gwagwarmayar kin yarda da turawan mulkin mallaka na Ingila kafin bada 'yancin kai a shekara ta alif 1960.[1]Shi ne shugaban jam'iyar PRP.
Farkon rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifeshi ne a Kano a shekara ta alif 1920, mahaifinshi mai suna Malam Yusufu malamin islama ne kuma faqihi ne, sannan kuma alkali ne a kotun Kano. kawunshi Malam Halilu shi ne ya karantar da shi Alqur’ani, malam Halilu ya kasance Limami ga masarautar Kano ga sarki Abdullahi Bayero (1929-1953). Wanda aka bashi suna da mai tantabaru.[2]
Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]Malam Aminu Kano ya yi makaranta ne a jahar Kano ya yi makarantar Shahuci Primary School da Kano Middle School a tsakanin shekara ta 1930 zuwa 1937, a lokacin yana dan shekara goma, kuma ya yi karatu a Kaduna college (Katsina College wanda yanzu Takoma Barewa College) a shekara ta 1937. Bayan ya gama ya karantar a Bauchi Middle School a shekara ta 1942, a lokacin Abubakar Tafawa Balewa shi ne shugaban makarantan, daga nan sai aka mayar da shi zuwa Maru Teacher’s College, Sokoto.[2] A cikin watan Satumban shekara ta alif 1946 an ba shi tallafin karatu zuwa Jami'ar Institute of Education da ta ke a Landan tare da Prime minister na farko a Najeriya wato Alhaji Sir Abubakar Tafawa Balewa.[3] Dawowarsa ke da wuya, aka kafa kungiyar malamai na Arewa wato (Northern Teachers Association) a Kano a watan Mayun shekara ta alif 1948, wadda wannan kungiya ita ce kungiya ta farko da aka fara kafawa a arewacin Najeriya a Kano a matsayin cibiyar kungiyar malamai.
[3]Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Malam Aminu Kano ya fara siyasa ne tare da Sa'adu Zungur a tsakanin shekara ta 1943 – 1946, inda suka fara kafa General Improvement Union. Su biyun sun yi hoɓɓasa wajen kafa Nothern Elements Progressive Association (NEPA).[4] Malam Aminu Kano ya kasance dan adawa ne kwarai ga turawan mulkin mallaka. Yana sukansu da barna da dukiyar kasa, da kuma 'yan siyasa da ke biyewa turawa bukatunsu na kansu. Hakan ya jawo masa cutarwa matuka daga turawa don su rufe masa baki. A farkon shekara ta 1950 sun kafa jam'iyyun arewa guda biyu, Northern People's Congress (NPC) wacce aka kafa a kan tsarin MacPherson constitution na shekarar 1951 da kuma jam'iyyar Northern Elements Progressive Union (NEPU)
Rasuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Malam Aminu Kano ya rasu ne a ranar Lahadi 17 ga watan Afrilun shekara ta 1993 wacce uwar gidansa Shatu ta sami gawarsa sanadiyar shanyewar ɓarin jiki da ya samu bayan ya yi jinyar cerebral malaria.[3]
Bibiliyo
[gyara sashe | gyara masomin]- Abba, Alkasim. (2006). The Politics of Mallam Aminu Kano, ISBN-978-2557-32-3.
Bincike
[gyara sashe | gyara masomin]- Callaway, Barbara J (July 1987). "Women and Political Participation in Kano City". Comparative Politics. 19 (4): 379–393. doi:10.2307/421813. JSTOR 421813.
- Feinstein, Alan; Feinstein, Alan (1988). "African Revolutionary: The Life and Times of Nigeria's Aminu Kano". Canadian Journal of African Studies. 22 (2): 347. doi:10.2307/485917. JSTOR 485917.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Reference Page on Federal Republic of Nigeria". NigeriaInfonet.com. KEK Technology Inc. Archived from the original on 2007-07-28. Retrieved 2007-05-17.
- ↑ 2.0 2.1 Abba, Alkasim. (2006). The Politics of Mallam Aminu Kano. p.1 ISBN-978-2557-32-3
- ↑ 3.0 3.1 3.2 "Aminu Kano". ZODML. 2014-09-22. Retrieved 2021-04-21.
- ↑ Abba, Alkasim. (2006). The Politics of Mallam Aminu Kano,p.2. ISBN-978-2557-32-3