Dandume

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Globe icon.svgDandume

Wuri
 11°25′00″N 7°12′00″E / 11.4167°N 7.2°E / 11.4167; 7.2
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jerin jihohi a NijeriyaJihar Katsina
Labarin ƙasa
Yawan fili 422 km²
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci

Dandume karamar hukuma ce dake a kudancin Jihar Katsina, Arewa maso yammacin Nijeriya. Dandume na akan lambar taswira 11°27'30''N da 7°07'37''E.

Ƙaramar hukumar Dandume tana da girman kasa kimanin 422km² da yawan mutane kimanin 145,739 bisa kidaya ta 2006. Manyan garuruwa da suke karkashinta sun hada da: Mahuta gari mafi girma a karamar hukumar Dandume, Nasarawa, Dantankarida kuma Yarkasuwa (tumburkai) da sauran su. Karamar Hukumar Dandume nada fitattun mutane a cikinta da kuma da dumbin mutane a cikin ta.

dandume

Dandume tayi fice ne a bangarori biyu; Noma da kuma Kasuwanci. Galibin mutanen karamar hukumar Dandume manoma ne sunyi fice wajen noman masara, dawa, waken suya, farin wake, dankalin Hausa, tumaturi, jar masara, rake, shinkafa dasauransu. Sannan karamar hukumar Dandume tayi fice wajen kasuwanci inda take da babbar kasuwar buhuna ta hatsi da tayi fice a arewacin Nigeria da take ci sau biyu a sati wato Asabar da kuma Laraba, sai kasuwar mahuta da itama take ci a ranakun Juma'a da kuma Talata.

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.