Jump to content

Ondo (jiha)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Jihar Ondo)
Ondo


Wuri
Map
 7°10′N 5°05′E / 7.17°N 5.08°E / 7.17; 5.08
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya

Babban birni Akure,
Yawan mutane
Faɗi 4,671,695 (2016)
 Yawan mutane 301.4 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Turanci
Labarin ƙasa
Yawan fili 15,500 km²
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Mabiyi Jihar Yammacin Najeriya
Ƙirƙira 3 ga Faburairu, 1976
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwa executive council of Ondo State (en) Fassara
Gangar majalisa Majalisar dokokin jihar Ondo
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo 340001
Kasancewa a yanki na lokaci
Lamba ta ISO 3166-2 NG-ON
Wasu abun

Yanar gizo ondostate.gov.ng
mutanen ondo
Gajeren zance na tarihin Ondo cikin yaren Ondo daga dan asali harshen
kasuwa a ondo

Jihar Ondo Jiha ce dake kudu maso yammacin Najeriya. An kirkiri jihar Ondo a ranar uku 3, ga watan Fabrairun 1976, daga tsohuwar yankin Yammacin Najeriya.[1] Ondo na da iyaka da jihar Ekiti (wanda a da tana cikin jihar Ondo ne) daga arewa, Jihar Kogi daga arewa maso gabas, jihar Edo daga gabas, Delta daga kudu maso gabas, Ogun daga kudu maso yamma sannan kuma jihar Osun daga arewa maso yamma sai kuma Tekun Atlantic daga kudu. Babban birnin jihar shi ne Akure, babban birnin masarautar Akure a da.[2] Ondo na da kasafin daji na mangrove-swamp forest kusa da gasar Benin.[3]

Ana mata lakabi da "Sunshine State" wato "jiha mai haskakawa". Jihar Ondo ita ce ta tara a girma a Najeriya.[4] Kuma ita ce jiha ta ashirin da biyar 25, a fadin kasa.[5] Mafi akasarin mutanen garin yarbawa ne.[6][7] Akasarin mutanen garin yarbawa ne, a yayinda ake amfani da harshen yarbanci a garin. Albarkatun kasar Ondo ya ta'allaka ne a kan man fetur, noman cocoa, da makamantansu.[8] Inda tsaunukan Idenre suke, wanda shi ne tsauni mafi girma a yankin yammacin kasar Najeriya.

daya daga cikin manyan makarantu na jihar ondo

Tana da yawan fili kimanin kilomita murabba’in 15,500, da yawan jama’a miliyan uku da dubu dari hudu da arba'in (kidayar a shekara ta dubu biyu da shida 2006). Babban birnin tarayyar jahar shi ne Akure. Oluwarotimi Odunayo Akeredolu, shi ne gwamnan jihar tun zaben shekara ta dubu biyu da sha daya 2011 har zuwa yau. Mataimakin gwamnan shi ne Agboola Ajayi. Dattijan jihar su ne: Yele Omogunwa, Robert Ajayi Boroffice da Omotayo Donald.

Jihar Ondo tana da iyaka da jihohin shida: Delta, Edo, Ekiti, Kogi, Ogun kuma da Osun.

Akeredolu Oluwarotimi Odunayo daga jam'iyyar APC ne gwamnan Jihar Ondo wanda aka rantsar a ranar ashirin da hudu 24, ga watan Fabrairun shekara ta dubu biyu da sha bakwai 2017,[9] kuma ya karbi mulkin daga hannun Olusegun Mimiko.[10] Mataimakinsa shi ne Lucky Aiyedatiwa.[11]

ondo

Kananan Hukumomi.

[gyara sashe | gyara masomin]

Jihar Ondo nada adadin Kananan hukumomi guda goma sha takwas (18) sune:


Kididdigar Jama'a.

[gyara sashe | gyara masomin]
Kididdiga akan yawan al'ummar jihar Ondo[12]
Local government area Male Female Total
Akoko North-West108,057105,735213,792
Akoko North-East93,06082,349175,409
Akoko South-East41,99540,43182,426
Akoko South-West123,979105,507229,486
Ose73,39571,506144,901
Owo110,429108,457218,886
Akure North66,87864,709131,587
Akure South175,495177,716353,211
Ifedore92,01484,313176,327
Ile Oluji87,50585,365172,870
Ondo West139,400144,272283,672
Ondo East38,03236,72674,758
Idanre66,99662,028129,024
Odigbo114,814115,537230,351
Okitipupa120,626112,939233,565
Irele75,63669,530145,166
Ese Odo78,10076,878154,978
Ilaje154,852135,763290,615
Total1,761,2631,679,7613,441,024
  1. "Ondo Election: 20 things to know about South-west state". 2020-10-09. Retrieved 2022-04-08.
  2. "Ondo | state, Nigeria". Encyclopedia Britannica. Retrieved 2021-09-23.
  3. "Ondo | state, Nigeria". Encyclopedia Britannica. Retrieved 2021-09-23.
  4. http://www.population.gov.ng
  5. "World Gazetteer: Nigeria - administrative divisions (per geographical…". archive.ph. 2013-01-05. Archived from the original on 2013-01-05. Retrieved 2022-04-19.
  6. "The People Of Ondo Kingdom And Their Culture: A Historical Survey And Political Underpinning – Ondo Connects New Era". Retrieved 2021-03-07.
  7. "Geography and Society", The Yoruba from Prehistory to the Present, Cambridge University Press, pp. 1–28, 2019-07-04, doi:10.1017/9781107587656.001, ISBN 978-1-107-58765-6, S2CID 131619880, retrieved 2021-03-07
  8. "Ondo State". Nigerian Investment Promotion Commission. 2019-01-09. Retrieved 2021-03-07.
  9. "Ondo state Governor"
  10. Jannah, Chijioke (2017-02-24). "PHOTONEWS: Inauguration of Rotimi Akeredolu as Ondo governor". Daily Post Nigeria. Retrieved 2022-04-18.
  11. "TODAY (2021-04-08). "2023: Ondo will go the direction of Governor Akeredolu – deputy". TODAY. Retrieved 2022-04-18.
  12. "National Population Commission of Nigeria". population.gov.ng.


Jihohin Najeriya
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa

Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara