Robert Ajayi Boroffice
Robert Ajayi Boroffice | |||
---|---|---|---|
11 ga Yuni, 2011 - 11 ga Yuni, 2023 ← Bode Olajumoke District: Ondo North | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | 23 ga Afirilu, 1949 (75 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Employers | Jami'ar Ibadan | ||
Kyaututtuka | |||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Farfesa Robert Ajayi Boroffice (an haife shi 23 ga watan Afrilu, a shekara ta 1949) ma'aikacin gwamnati ne wanda aka zaɓa Sanata mai wakiltar Ondo ta Arewa, a jihar Ondo, Najeriya a ranar 9 ga watan Afrilun shekarar 2011.[1]
Farkon aiki
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Boroffice a ranar 23 ga watan Afrilun shekara ta 1949 a Oka-Akoko, Jihar Ondo, Kudu maso Yammacin Najeriya. Ya zama malami a jami’ar Ibadan a cikin shekarar 1975, sannan kuma Farfesa a fannin dabbobi a jami’ar jihar Legas a cikin shekarar 1986. Ya taɓa rike mukaman gudanarwa a jami’ar jihar Legas da suka haɗa da shugaban sashen, shugaban tsangayar karatu, da shugaban kwamitin malamai.[2]
Ma'aikacin gwamnati
[gyara sashe | gyara masomin]An naɗa Boroffice Daraktan Gudanarwa na Kimiyya a Hukumar Kula da Kimiyya da Injiniya ta Ƙasa[3] a cikin shekarar 1992. Ya yi aiki a kan fasahar ƙere-ƙere da fasahar sadarwa da kimiyyar sararin samaniya da fasaha wanda ya kai ga kafa hukumar bunƙasa fasahar ƙere-ƙere ta ƙasa da Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa da Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta ƙasa.[2]
A cikin shekarar 2004, tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya ba Boroffice muƙamin Officer of the Order of the Niger (OON).[2] A cikin watan Maris ɗin shekarar 2011, an ba Boroffice lambar yabo ta Golden Merit Award a Kimiyyar Sararin Samaniya ta Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Duniya.[4]
Sana'ar siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Boroffice ya fuskanci ƴar adawa a yunƙurinsa na zama ɗan takarar jam’iyyar Labour a mazaɓar Ondo ta Arewa. Ya samu goyon bayan sarakunan gargajiya a yankin Akoko na jihar Ondo.[5] A wata hira da aka yi da shi gabanin zaɓen watan Afrilu, ya caccaki ƴan siyasar da ba su da gaskiya da mutunci, inda suka yi alƙawurran da ba za su iya cikawa ba domin a zaɓe su, sannan su mayar da hankali wajen samun kuɗi da zarar an zaɓe su.[6] A zaɓen dai Boroffice ya samu ƙuri'u 84,290. Ƴan takarar da suka zo na biyu sun haɗa da Sanata Bode Olajumoke na jam’iyyar PDP da ƙuri’u 51,112 da Agunloye Olu na jam’iyyar Action Congress of Nigeria da ƙuri’u 36,601.[7]
A ranar 28 ga watan Disambar a shekara ta 2011, Boroffice ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar Action Congress of Nigeria domin ya cim ma burinsa na zama gwamnan jihar Ondo.[8] Daga baya, ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar All Progressives Congress, jam'iyya mai mulki. A ranar 2 ga watan Yuli, shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmed Lawal, ya bayyana Borrofice a matsayin ɗaya daga cikin mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa ta 9.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://www.premiumtimesng.com/news/top-news/334205-deputy-senate-presidency-boroffice-withdraws-from-race.html?tztc=1
- ↑ 2.0 2.1 2.2 https://web.archive.org/web/20110727142130/http://okaland.okadescendants.org/?p=68
- ↑ https://punchng.com/dad-not-one-to-defect-to-any-party-for-selfish-gains-senator-boroffices-daughter/
- ↑ https://punchng.com/Articl.aspx?theartic=Art201103151213046[permanent dead link]
- ↑ https://allafrica.com/stories/201101140514.html
- ↑ https://web.archive.org/web/20110725001742/http://tribune.com.ng/index.php/politics/19457-desperation-cause-of-violence-in-politics-boroffice
- ↑ https://web.archive.org/web/20110419203046/http://www.inecnigeria.org/downloads/?did=114
- ↑ https://web.archive.org/web/20120108160503/http://myondostate.com/w3/photo-news-boroffice-formally-declares-for-acn/