Jump to content

Akure

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Akure


Wuri
Map
 7°15′00″N 5°11′42″E / 7.25°N 5.195°E / 7.25; 5.195
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaOndo
Babban birnin
Yawan mutane
Faɗi 847,903 (2010)
• Yawan mutane 855.6 mazaunan/km²
Labarin ƙasa
Yawan fili 991 km²
Altitude (en) Fassara 350 m
Bayanan tarihi
Ƙirƙira 1150
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo 340106
Kasancewa a yanki na lokaci
Tsarin lamba ta kiran tarho 234
Akure.
Gajeren zance na tarihin Akure cikin yaren Akure daga ɗan asali harshen

Akure birni ne, da ke a jihar Ondo, a ƙasar Nijeriya,[1] kuma itace birni mafi girma kuma babban birnin jihar Ondo. Bisa ga ƙidayar jama'a a shekarar 2006.[2] akwai jimilar mutane 484,798 (dubu dari huɗu da tamanin da huɗu da dari bakwai da casa'in da takwas). An gina birnin Akure a karni na sha biyu.

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Kafin 1914[gyara sashe | gyara masomin]

An samu ragowar tsofaffin dutsu tun na zamanukan da suka gabata a wajen birnin Akure. Har wayau an samu ragowar kasusuwar mutanen da, wanda su ne ragowar mutanen da mafi tsufa da aka taba samu a Afurka ta kudu kimanin shekaru 11000 sukayi rayuwa a baya da suka wuce.

Tarihin gargajiya na tatsuniyoyi sun nuna cewa birnin Akure ta samo asaline daga Omoremilekun Omoluabi, tattaba-kunnen sarki Oduduwa. Yarima Omoluabi ya bar Ile-Ife, masarautar kakanshi ne domin neman wurin zama bayan yaci wata tsatstsaurar gwaji da sarkin Yarbawa na lokacin yayi masa da kanshi, a yayinda ya iske birnin a yankin Akure na yanzu. Fadar sarki (Oba) na a tsakiyar birnin, wacce aka gina a shekara ta 1150 AD.[3] Fadar na da harabobi 15, kuma kowacce nada amfaninta. Misali, a harabar Ua ubura ake rantsuwa da alkawari, a harabar Ua Ikomo ake radin suna, Wasu daga cikin sunayen harabobin sun hada da Ua nla, Ua Ibura, Ua jemifohun, Ua Ikomo. Yanzu an gina wani sabon fada na kirar zamani a yankin kudancin tsohuwar fadar. Oja Oba watau kasuwar sarki tana nan kusa da fadar.

Ana kiran sarkin Akure da "Deji of Akure", wanda hakimai shida ke tayashi gudanar da harkokin sarauta. Gunkin Akure shine mahaifin Omoremilekun Omoluabi wanda ake kira da "Ekun" ma'ana damisa (shine inkiyarsa na sarauta). Wannan dalilin yasa duk wani dan Asalin Akure ake masa lakabi da "Omo Ekun"

Daga 1914 zuwa yanzu[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 1915, gwamnatin turawan mulkin mallaka suka hade yankunan Owo, Ondo da Ekiti wacce ta samar da sabuwar gunduma da cibiyar ta a Akure. Birnin Akure ta zama babban birnin Onda a shekara ta alif 1976.

An nada Adebiyi Adegboye Adesida Afunbiowo II, a matsayin sarkin Akure a ranar 13 ga watan Augusta, shekarar 2010, don gadon kujerar Oba Oluwadamilare Adeshina wanda aka tsige a ranar 10 ga watan June, shekarar 2010, a dalilin rashin da'a ga ababe masu tsarki da daraja.[4] Daga bisani an nada diyar tsohon sarki Afunbiowo, Omoba Adetutu matsayin sarauniya a ranar 30 ga watan Nuwamba, shekarar 2013, bayan tsigeshi.

A shekara ta 2015, An nada Omoba Kola Aladetoyinbo matsayin sarki, bayan ya buge yan takara 12 wanda gidan sarauta na Osupa suka gabatar don zama sarkin Akure na 47.

Labarin Kasa[gyara sashe | gyara masomin]

Birnin Akure na nan a 7°25’ daga arewacin equator, da kuma 5°19’ daga kudancin Meridian. Tana da nisan kimanin kilomita 700km (430 mi) daga kudu-maso-yammacin Abuja, da kuma kilomita 311km (193 mi) daga arewacin Lagos. Akwai bambancin yawan mutane dangane da wuraren zama, wasu daga ciki misali Arakale, Ayedun Quarters, Ijoka, da kuma Oja-Oba suna da kimanin mutum 200 a kowacce hekta guda. A yayinda wasu yankunan kuma kamar Ijapo Estate, Alagbaka Estate, Avenue da kuma Idofin suke da kimanin mutum 60 zuwa 100 a kowacce hekta (24 and 40/acre). Birnin ya fada cikin kasafin yanayi na tropic rainforest zone na Najeriya.

Tattalin arziki[gyara sashe | gyara masomin]

Akure na da gidajen telebijin guda biyu da kuma gidajen rediyo guda takwas: wanda suka hada da NTA Akure,[5] Ondo State Television,[6] Sunshine Radio Akure, Adaba FM, Futa FM, Empire Radio, Positive FM Akure, Orange FM, Galaxy Radio, Crest FM, and Breeze FM.

Akure itace cibiyar kasuwanci na yankunan da ake noma kamar na cocoa, doya, rogo, masara, taba da dai sauransu. Har wayau ana noman auduga kuma ana amfani dashi wajen samar da kayan sanyawa a yankin. Hatsi da aka fi nomawa a yankin sun hada da; shinkafa, wake da dawa.

Wuraren kaswanci[gyara sashe | gyara masomin]

Akwai wuraren cin abinci da ya a birnin Akure kamar Chicken Republic, Tantalizers, Captain Cook, Mr. Bigg's, LAH Kitchen & Lounge da dai sauransu.[7] Manyan shaguna kuma sun hada da; NAO supermarket, AFOYEM supermarket, CECI supermarket, PEP stores, Omega supermarket, and DE CHRIS supermarket, OUK supermarket, God's Love supermarket da dai sauransu. Akwai kuma Shoprite Akure mall.

Harkokin Lafiya da Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

A asbitocin birnin Akure akwai kwararrun ma'akatan kiwaon lafiya wanda aka horar sosai don kare lafiya al'umman garin. Har wayau akwai karin wuraren shan magani na gwamnati da kuma wuraren da ba na gwamnati ba. Shirin 'Abiye' health programme wanda Gwamnatin Oluseegun mimiko suka gudanar akan kula mata masu haihuwa da shayarwa ya samu karbuwa a wajen WHO wanda yana daya daga cikin mafi kyawun shirin lafiya da aka taba gudanarwa tare da samar da asibitin Mother-Child hospital.

Birnin na dauke da jami'oi wanda suka hada da; Federal University of Technology Akure, Federal College of Agriculture, School of Nursing and Midwifery, and School of Health Technology. Har wayau tana da sanannun makarantun sakandare da suka hada da; St. Thomas Aquinas College, Oyemekun Grammar School, St. Louis Grammar School, and Fiwasaye Girls' Grammar School. Har wayau birnin na dauke da makarantun gwamatin tarayya wanda suka hada da Girls' College da St. Peter's Unity Secondary School da dai sauransu.

Birnin Akure[gyara sashe | gyara masomin]

A karkashin masarautar Akure na yanzu akwai kananan masarautu guda biyu wanda suke da nasu sarakunan. Birnin ta kasancewa mahaifa ga wasu manyan mutanen Najeriya kamar Chief Olu Falae, Dr Akinola Aguda da sauran sanannun mutane a fannin boko, soji, shari'a da sauran fannukan gwamnati. Philip Emeagwali, wanda ya lashe gasan Gordon Bell Prize,[8] mahaifiyar Sunny Adé, Ralph Alabi (tsohon chairman na kamfanin Guniness Nigerian Ltd), da kuma Kole Omotosho duka yan asalin Akure ne.

Wasanni[gyara sashe | gyara masomin]

A fannin wasanni, Akure da katafaren filin wasan kwallon kafa da ke iya daukan mutum kimanin 15,000. Akwai wani sabon filin da ake ginawa daga kudanci birnin.

Addinai[gyara sashe | gyara masomin]

Akure birni ne dake dauke da mutane mabiya addinai iri-iri; kamar kiristoci, musulmai da kuma masu bin addinin gargaji ko kuma bautan gumaka. Akwai cocuka da dama a garin, akwai babban masallaci (Central Mosque) bisa hanyar Oba Adesida Road wanda yana daya daga cikin kayatattun wurare a garin. Abun jinjinawa shine mutanen Akure na zama lafiya da junansu.

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Akure tana da dan majalisa dake wakiltan ta a majlisar dokoki watau Hon. Simeon Toluwani Borokini (Akure South I), Hon. (Dr.) Abiodun Faleye (Akure North) da kuma Hon. Olajide David Sunday (Akure South II).

Sanannun Mutane[gyara sashe | gyara masomin]

Hotuna[gyara sashe | gyara masomin]


Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "A millennium City Archived June 13, 2010, at the Wayback Machine.
  2. "archived October 26, 2009, at the Wayback Machine
  3. MAURICE ARCHIBONG (August 6, 2009). "Struggles to breathe life into National Museum Akure after 21-year dormancy". Daily Sun. Archived from the original on April 11, 2010. Retrieved 2010-09-19.
  4. "Former Nigerian Presidential Aide, Adebiyi Adesida, Becomes the New Deji of Akure". SharpEdgeNews. August 12, 2010. Archived from the original on 17 August 2010. Retrieved 2010-09-13.
  5. [1] Archived ga Yuni, 8, 2009 at the Wayback Machine
  6. "State Govt Owned". NBC. Archived from the original on 2014-02-08. Retrieved 2014-02-25.
  7. "LAH Kitchen & Lounge Set To Launch In Akure As Recruitment Commences » 9jainsider.com". 9jainsider.com. Retrieved 2020-08-02.
  8. "A Nigerian, A Computer Wizard?". Emeagwali.com. Retrieved 2013-12-11.
  9. "Omoyele, Idowu (2020-05-07). "Harry Garuba: obituary". The Guardian. Retrieved 2021-04-05.