Jump to content

Rijau

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Rijau

Wuri
Map
 11°06′N 5°18′E / 11.1°N 5.3°E / 11.1; 5.3
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin NajeriyaJihar Neja
Yawan mutane
Faɗi 122,050 (1991)
• Yawan mutane 38.19 mazaunan/km²
Labarin ƙasa
Yawan fili 3,196 km²
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Rijau

Rijau: Karamar hukuma ce dake Jihar Neja a tarayyar Nijeriya.

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.

A duk lokacin damina zafin jiki ba kasafai yake aɗuwa ƙasa da 54 ° F ko ya tashi sama da 105 ° F, tare da matsakaicin shekara-shekara na 59 ° F zuwa 100 ° F.[1][2]

Mafi tsananin zafin jiki na yau da kullun nakaiwa 97 ° F lokacin zafi kamar yanda akasaba a watanni 2.3, wanda ke gudana daga Fabrairu 16 zuwa Afrilu 25.[3] Afrilu yana da matsakaicin zafin jiki na 99 ° F da ƙananan zafin jiki ya 76 ° F, yana mai da shi watan da ya fi zafi a shekara a Rijau.[4]

Matsakaicin zafin jiki na yau da kullun a ƙasa da 87 ° F yana da kyau a lokacin sanyi na watanni 3.3, wanda ke gudana daga Yuli 2 zuwa Oktoba 10. Disamba, tare da matsakaici a kasa da 60 ° F zuwa 90 ° F, shine watan da ya fi sanyi a shekara a Rijau.[5]

Matsakaicin kason da gajimare ke rufewa a samaniyar Rijau ya bambanta sosai a cikin shekara.[1]

Farawa game da Nuwamba 4 kuma yana da tsawon watanni huɗu, lokacin da ya fi haske a Rijau ya ƙare a kusa da Maris 5. [2]

A cikin Rijau, Janairu shine watan da ya fi washewa a shekara, tare da sararin samaniya ya kasance a bayyane, galibi a bayyane yake, ko kuma wani ɓangare a rufe 61% na lokacin.

Farawa a kusa da Maris 5 kuma yana da tsawon watanni 8.0, lokacin girgije na shekara ya ƙare a kusa da Nuwamba 4 . [3]

Mayu shine watan Mafi kololuwar girgije a shekara a Rijau, tare da sararin sama da ke rufewa ko kuma mafi yawan bangare yana da gajimare da77% a matsakaicin lokaci.[6]

  1. 1.0 1.1 "Rijau Climate, Weather By Month, Average Temperature (Nigeria) - Weather Spark". weatherspark.com (in Turanci). Retrieved 2023-09-10.
  2. 2.0 2.1 "Rijau, Niger, NG Climate Zone, Monthly Averages, Historical Weather Data". tcktcktck.org. Retrieved 2023-09-10.
  3. 3.0 3.1 "Current Local Time in Rijau, Niger, Nigeria". www.generalblue.com (in Turanci). Retrieved 2023-09-26.
  4. "Weather Archive Rijau". meteoblue (in Turanci). Retrieved 2023-09-26.
  5. "Rijau weather forecast for today". justweather.org (in Turanci). Retrieved 2023-09-26.
  6. Atlas, Weather. "Weather today - Rijau, Nigeria". Weather Atlas (in Turanci). Retrieved 2023-09-26.