Jump to content

Akko (Nijeriya)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Akko, Nigeria)
Akko

Wuri
Map
 10°03′N 11°13′E / 10.05°N 11.22°E / 10.05; 11.22
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin NajeriyaJihar Gombe
Yawan mutane
Faɗi 337,853 (2006)
• Yawan mutane 128.61 mazaunan/km²
Labarin ƙasa
Yawan fili 2,627 km²
Altitude (en) Fassara 446 m
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwa supervisory councillors of Akko local government (en) Fassara
Gangar majalisa Akko legislative council (en) Fassara
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo 771

Akko karamar hukuma ce dake Jihar Gombe a arewa maso gabashin Nijeriya.[1]

Kumo itace hedikwatar karamar hukumar Akko.[2] Sa annan Sakateriyar karamar Hukumar Akko yana cikin garin Kumo Akko LGA, Gombe State. Garuruwa ko anguwowin da ke Akko sune kamar su Gona, kumo, pindiga, Garin Garba, Jalingo, Jauro tukur, Kembu, kumo north, Garko, Kumo east, panda, kumo central, Lergo, Garin liman kumo, Marraraban Tumu da sauran su.

Karamar hukumar Akko tana cikin garin Kumo kuma wannan yanki ya ƙunshi Gona, Kumo, Pindiga, Garin Garba, Jalingo Jauro Tukur, Kembu, Kumo North, Kumo East, Panda, Kumo Central, Lergo, Garin Liman Kumo, Mararraban-Tum. , Tashan Magarya, da dai kuma sauransu.

Karamar hukumar Akko tana karkashin jihar Gombe ne kuma gwamna mai ci Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya ke mulki a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).[3][4][5]

Karamar hukumar Akko nada yaruka daban-daban wanda a ƙalla sunkai yaruka talatin (30) ake magana dasu a cikin ta, amma yaren da suka fi yawan amfani dashi wajen magana shine Fulani da Hausa.[6]

Akko nada jami'ar tarayya guda ɗaya wato Federal University Kashere wanda take a garin Kashere.[7] Gombe state University of Science and Technology[8]

  1. "Rome2rio: Discover how to get to Akko from anywhere". Rome2rio (in Turanci). Retrieved 2020-03-30.
  2. https://dailynigerian.com/gombe-rep-construct-schools/
  3. https://www.rome2rio.com/s/Akko-Nigeria
  4. https://tribuneonlineng.com/gombe-governor-dissolves-lgcs-directs-handover-to-senior-officers/
  5. https://dailytrust.com/ipac-kicks-against-plans-to-appoint-lg-caretaker-chairmen-in-gombe/
  6. https://www.ethnologue.com/country/NG
  7. https://oer.fukashere.edu.ng/login
  8. https://www.premiumtimesng.com/news/more-news/571033-buhari-mourns-ex-vc-of-three-nigerian-universities.html