Muhammad Inuwa Yahaya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya (An haife shi a Aktoba 9, 1961) Dan Nijeriya ne, Dan'kasuwa, kuma Dan'siyasa. Shine Gwamnan Jihar Gombe wanda aka zaba a 9th ga watan Maris 2019 a karkashin jam'iya mai mulki All Progressive Congress (APC).[1]

Simpleicons Interface user-outline.svg Muhammad Inuwa Yahaya
Rayuwa
Haihuwa Oktoba 9, 1961 (58 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress
Muhammad Yahaya Inuwa, Gwamnan jihar Gombe

Farkon Rayuwa[gyara sashe | Gyara masomin]

An haifi Inuwa a 9 ga watan Oktoban shekarar 1961 a garin Jekadafari, Jihar Gombe. Mahaifinsa, Alhaji Yahaya Umaru, shahararren dan'kasuwa ne.[2]

Karatu[gyara sashe | Gyara masomin]

Bayan kammala karatun sa na firamare da sakandare, Inuwa yasamu gurbin cigaba da karatu a na babban makarantar gaba da sakandare wato a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, inda ya karanta lissafi (Accounting) a 1983.[2]Yasamu shaidar Bachelor's degree.

Siyasa[gyara sashe | Gyara masomin]

Alhaji Inuwa Yahaya ya tsunduma cikin siyasa a shekara ta 2003. Amma yayi suna ne a 2015, inda yazama dan'takarar gwamna a jam'iyar All Progressive Congress (APC) na Jihar Gombe. A October 1, 2018 yasake lashe zaɓen cikin gidan jam'iyar All Progressive Congress (APC) a karo na biyu Dan yin takarar gwamnan Jihar Gombe a babban zaben Najeriya na shekarar 2019[3][4]

Alhaji Inuwa yayi nasara a zaɓen 2019 wanda ya gudana a watan Maris 9, 2019. Yasamu adadin ƙuri'u 364,179, inda ya buge abokin takararsa na jam'iyar Peoples Democratic Party (PDP), Sen. Usman Bayero Nafada wanda yasamu tashi adadin ƙuri'un 222,868.

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. Published. "INEC declares APC’s Inuwa Yahaya Gombe Gov-elect". Punch Newspapers (in en-US). 
  2. 2.0 2.1 "Brief biography of Gombe State Governor-Elect". Daily Trust (in en-GB). 2019-03-19. 
  3. editor (2018-10-01). "APC Votes Yahaya as Gombe Guber Candidate". THISDAYLIVE (in en-US). 
  4. "Gombe 2019: The game changers". Tribune Online (in en-GB). 2018-09-25.