Zariya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Zaria)
masallacin fadan zazzau
Zariya
Zaria (en)


Wuri
Map
 11°04′N 7°42′E / 11.07°N 7.7°E / 11.07; 7.7
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaJihar Kaduna
Yawan mutane
Faɗi 408,198 (2006)
• Yawan mutane 725.04 mazaunan/km²
Labarin ƙasa
Yawan fili 563 km²
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwa supervisory councillors of Zaria local government (en) Fassara
Gangar majalisa Zaria legislative council (en) Fassara
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Gidan sarkin Zazzau.
ganuwar Zaria
zazzau place

Zariya (Ko kuma da turanci Zaria, sai kuma Zazzau sunan da ake mata lakabi da shi). Zaria gari ne dake cikin arewacin Najeriya, karamar hukuma ce a cikin jihar Kaduna, tana da iyaka da Funtuwa, babban birnin Kaduna, da kuma Igabi duka a cikin ƙasar Najeriya. A bisa ga ƙidayar jama'a na shekara ta dubu biyu da shida (2006), jimillar mutane dubu dari bakwai da sittin (700060) ne a garin Zariya, to amman daga bisani an kimanta yawan su a shekara ta dubu biyu da sha bakwai (2017), ga jimillar mutane miliyan daya (1000000). Birnin Zariya tana da kilomita dari biyu da sittin (260kms) ne daga garin Abuja, kilomita tamanin (80kms) ne daga Zariya, kilomita dari daya da sittin (160) ne daga Kano.[1] garin Zazzau an saka masa suna ne daga Sarauniya Amina.[2]

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Asalin sarakunan zariahausawa ne dasu ke mulkan su, wanda su ka yi sarauta tun daga shekara ta dubu daya da dari biyar da biyar (1505) zuwa shekarar dubu daya da dari takwas da biyu 1802, A shekara ta dubu daya da dari takwas da hudu 1804 ne Shehu Usman dan Fodiyo yayi jihadi, inda ya yaki sarkin gobir mai suna Yunfa, a Yakin kwoto, daga nan ne ya fara yada sarautarsa da musulunci zuwa masarautun Hausawa, A garin zariya kuma akwai Malam Musa wanda ya dade yana da’awar zuwa ga addinin musulunci, Malam Musa Bafillatani ne, Jin Jihadin Usman dan Fodiyo yasa shima ya karbi tuta daga Usman dan Fodiyo. Da Malam Musa da Yamusa mutumin fulanin Barno suka doso Zariya suka yaki sarki Makau dan kabilar Hausawa, Makau sai ya gudu shi da mutanensa zuwa Zuba, wani gari ne na Gwari da Koro a yankin Abuja a yau, Malam Musa sai ya zama Sarkin zazzau na farko daga kabilar Fulani, bayan rasuwarsa sai aka naɗa Yamusa a shekarar ta dubu daya dari takwas da ashirin da daya 1821 a matsayin sarkin zazzau, shi kuma fulanin Barno ne, daga nan ne Bare-Bari da Fulanin Mallawa suka fara sarauta a kasar zazzau.[3] (Ihayatu (talk) 21:14, 30 Mayu 2023 (UTC))

Birni ne a kasar Hausa wanda kuma yana daya daga cikin garuruwan da Shehu Usman ya bada tutar addinin musulunci ya tabbata a ciki. Birni ne mai dadin zama saboda yanayinsa gashi kuma babbar cibiyar ilimin addini dana boko a arewacin Najeriya. Wannan gari Allah ya albarkace shi da kasa ta noma da kuma ilimin addinin musulunci dana zamani wanda a dalilin haka ne baki daga makotan garin suke zuwa domin neman ilimi kai harma da na kasashen waje da kuma mutanen garin Zariya su kansu, Wadannan garuruwa a wancen lokacin duka suna karkashin mulkin garin zazzau ne, inda Zariya take a matsayin babban birni, amman yanzu wasu daga cikin wadannan garuruwan basa karkashin zazzau.[3] (Ihayatu (talk) 21:14, 30 Mayu 2023 (UTC))

s/n Garuruwa Garuruwa
1-2 Anchau Zaria
3-4 Soba
5-6 Damo Likoro
7-8 Ɗan Alhaji Igabe/Igabi
9-10 Garu Ikara
11-12 Gimba Zuntu
13-14 Giwa Richifa
15-16 Fatika Kargi
17-18 Funkwi Kauru
19-20 Ɗan Maliki Lere
21-22 Durum Kubau
23-24 Ɗan Lawal Kudan
25-26 Faki Kuadaru

Mutane[gyara sashe | gyara masomin]

Asalin mulkin Zariya yana karkashin Sarakunan [Hausawa]] ne, ana kiran garin da zazzau, zakzak ko zegzeg, dukkan wadannan sunayen ana kiran garin zazzau da shi, amman daga bisani sunan zazzau ya canza zuwa Zariya, A inda kuma sarautar aka fi kiranta da zazzau, shiyasa sarkin garin ake kiran shi da sarkin zazzau, mutanen da suka fito daga garin ana kiransu da suna Bazazzagi, jam’i kuma Zazzagawa.[3]. (Ihayatu (talk) 21:14, 30 Mayu 2023 (UTC))

Sarauta[gyara sashe | gyara masomin]

Asalin mulkin Zariya tana karkashin Sarakunan hausawa ne, wadanda ke mulkan masarautan Zazzau, amma daga baya sarakunan Mallawa da fulani suka hada hannu da karfi suka yaki sarakunan hausawa a shekarar 1804. Sarakunan Hausawa na farko sun rayu ne a karni na 15, wadanda a wannan lokacin ba'a iya tina shekarun da sukayi sarauta, amman sarakunan hausawa na biyu sunyi mulki ne a karni na 16, inda aka taskace shekarun mulkin su, har zuwa lokacin da sarakunan Fulani suka yake su, sarkin su na karshe shine Makau a Zariya, a Gobir kuma shine Yunfa.

Sarakunan Hausawa na Farko
s/n Sarakuna Shekara
1 Gunguma
2 Matazo
3 Tumsah
4 Tamusa
5 Suleimanu
6 Maswaza
7 Ɗinzaki
8 Nayoga
9 Kauchi
10 Nawainchi
11 Machikai
12 Kewo
13 Bahikarr
14 Majidada
15 Dahirahi
Sarakunan Hausawa na biyu
s/n Sarakunan Hausa Shekara
1 Moman Abdu 1505 – 1530
2 Gudan Dan Masukanan 1530 – 1532
3 Nohirr 1532 – 1535
4 Bakwa Turunku 1535 – 1536

Arziki[gyara sashe | gyara masomin]

Masana'antu[gyara sashe | gyara masomin]

Garin Zariya an san su da sana’o’i daban daban, Garin jere da kajuma suna karkashin Zariya, sun yi suna akan saka ta hannu.[4] Abu mai muhimmancin gaske a kasar Zariya shine Audiga, wanda ake diba daga Zariya da kano zuwa kasashen turawa domin amfanin masana’antu, garin Zariya sun shahara da sakan kayan sakawa, hula, da kuma rini.[5]

Kasuwanci[gyara sashe | gyara masomin]

Zariya gari ne, na kasuwanci da harkar noma.

Noma[gyara sashe | gyara masomin]

Allah ya ba Zariya kasar noma mai kyau.ana noma masara, doya, dawa, dauro, rake, barkono, shinkafa, dss.

Sufuri[gyara sashe | gyara masomin]

Zariya suna da hanyar sufurin jirgin ƙasa da hada Zariya da garuruwan Lagos , Kano, Abuja da kuma Kaduna (birni).[6][7]

Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Zariya cibiya ce ta ilimin addini da boko, a garin ne jami'ar Ahmadu Bello ta ke, bayan ABU akwai makarantun Ilimi kusan 9 a cikin garin Zariya.Kamar; 1. Federal College of Education ((F.c.e)). 2. Nuhu Bamalli Polytechnic. 3. Ameer Shehu Idris. 4. National Institute of transport Technology((Nitt)). 5. Leather Research. 6. Narict 7. National College of Aviation((Ncat)). 8. Napri 9. Institute of Animal research((I.A.R)). Akwai kuma malaman addinin Musulunci manya kaman; 1. Sheikh Mua'azu 2. Sheikh Abdulkadir 3. Sheikh Yahuza

Da dai sauran su.

Addini[gyara sashe | gyara masomin]

Musulunci[gyara sashe | gyara masomin]

Mutanen Zariya ma fi yawansu mabiya addinin Musulunci ne.

Kiristanci[gyara sashe | gyara masomin]

Kasantuwar ma'aikatu na Gwamnatin tarayya a garin Zariya da kuma hanyoyin sufuri da yanayin kasuwanci a garin, hakan ya sa mabiya addinin Kiristiyaniti na kara yawa a garin.

Masana'antu[gyara sashe | gyara masomin]

Akwai masana'antu kamar su "Sunseed", Pz, dasau ransu.

Garuruwa[gyara sashe | gyara masomin]

Da a garin Zariya akwai Ganuwa, amma daga baya duk an cire su.[8][9]

Bibiliyo[gyara sashe | gyara masomin]

  • Professor lavers collection: Zaria Province, Arewa House.
  • Maiwada, Salihu and Renne, Elisha P. (2007) "New Technologies of Embroidered Robe Production and Changing Gender Roles in Zaria, Nigeria, 1950–2005"
  • Gihring, Thomas (1984). "Intraurban Activity Patterns among Entrepreneurs in a West African Setting". Geografiska Annaler. Series B, Human Geography.
  • Smith, Michael G. (1960) Government in Zazzau 1800–1950 International African Institute by the Oxford University Press, London, OCLC 293592; reprinted in 1964 and 1970.
  • Dan Isaacs (28 September 2010). "Nigeria's emirs: Power behind the throne". BBC News. Retrieved 29 September 2010.

Diddigin bayanai na waje[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. http://www.britannica.com/eb/article-9078266/Zaria
  2. https://www.britannica.com/place/Zaria-Nigeria
  3. 3.0 3.1 3.2 professor lavers collection: zaria province.
  4. Maiwada, Salihu and Renne, Elisha P. (2007) "New Technologies of Embroidered Robe Production and Changing Gender Roles in Zaria, Nigeria, 1950–2005" Textile History 38(1): pp. 25-58, page 25
  5. Gihring, Thomas (1984). "Intraurban Activity Patterns among Entrepreneurs in a West African Setting". Geografiska Annaler. Series B, Human Geography. 66 (1): 19–20.
  6. https://www.bbc.co.uk/news/world-africa-21364541
  7. https://www.economist.com/news/middle-east-and-africa/21571481-renovated-railway-line-welcome-more-are-still-sorely-needed-slow
  8. https://web.archive.org/web/20091027035909/http://www.abu.edu.ng/bsn/zaria.php
  9. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2009-10-27. Retrieved 2020-12-27.