Jump to content

Bekwarra

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Bekwarra

Wuri
Map
 6°41′38″N 8°58′03″E / 6.69389°N 8.9675°E / 6.69389; 8.9675
Territory claimed by (en) FassaraLua error a mw.lua, layi na 656: invalid value (nil) at index 1 in table for 'concat'.
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin NajeriyaJahar Cross River
Yawan mutane
Faɗi105,497 (2006)
• Yawan mutane344.76 mazaunan/km²
Labarin ƙasa
Yawan fili306 km²

Bekwarra haramar hukuma ce dake a Jihar Cross River a shiyar kudu maso kudancin Nijeriya.[1]

Tana da fadin murabba'in kilomita 306 (118 sq mi), kuma tana da yawan jama'a 105,822 kamar yadda aka yi a ƙidayar jama'a ta 2006.

Lambar akwatin gidan waya ta yankin ita ce 550.[2] Babban yankin da mutanen Bekwara ke zaune shi ne noma, cinikin gyada, ciniki, farauta da kuma shan giyar dabino. An san ta da noman gyada. Sauran amfanin gona da ake nomawa a yankin sun haɗa da shinkafa, masara, doya, rogo, abarba, plantain da ayaba.

An yi amfani da kalmar "Bekwarra" ga takamaiman ƙabilar, kuma hukumomin yankin da daidaikun mutane suna kiranta da Bekwarra. Har yanzu ana rubuta kalmomin 'Bekworrra' da 'Bekworrah', amma an karɓe ta sosai saboda yadda take da daidaito da tsarin muryar da 'yan ƙabilar ke amfani da shi da kuma dacewa da mutanen Bekwarra a lokacin mulkin mallaka.[3]

Suna zaune ne a yankin arewacin lardin Ogoja, a Gabashin Najeriya, tare da iyaka da yankin Arewacin Najeriya. Suna zaune ne a yankin da ya fi murabba'in kilomita 260 ko murabba'in mil 100 kuma iyakar yammacinsa tana da nisan mil kaɗan a Gabashin garin Ogoja. Akwai ƙalilan mazauna wasu ƙabilu a cikin wannan yanki kuma suna kama da babban wuri na daidaito tsakanin harshe.[4]

Yanayin ƙasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Ƙaramar hukumar Bekwarra ta ƙunshi koguna da magudanan ruwa da yawa kuma tana da jimillar girman murabba'in kilomita 306 ko murabba'in mil 118. Ana kyautata zaton matsakaicin zafin yankin shine digiri 25 na Celsius (digiri 77 na Fahrenheit), kuma an kiyasta cewa danshinsa shine kashi 91%.[5]

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.
  1. ↑ "Cross River State". Cross River Hub. Retrieved 2021-09-12.
  2. ↑ "Post Offices- with map of LGA". NIPOST. Archived from the original on 7 October 2009. Retrieved 2009-10-20.
  3. ↑ Stanford, Ronald (1967). The Bekwarra language of Nigeria : A grammatical description (phd thesis). SOAS University of London.
  4. ↑ Omagu, D. O. (2012). The wing of change: Bekwarra in an Age of globalization, Aboki Publishers
  5. ↑ "Bakassi Local Government Area". www.manpower.com.ng. Retrieved 2025-11-27.