Yenagoa
|
| |||||
|
| |||||
| Wuri | |||||
| |||||
| Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
| Jihohin Najeriya | Jahar Bayelsa | ||||
| Babban birnin | |||||
| Yawan mutane | |||||
| Faɗi | 352,285 | ||||
| • Yawan mutane | 207.47 mazaunan/km² | ||||
| Labarin ƙasa | |||||
| Yawan fili | 1,698 km² | ||||
| Bayanan tarihi | |||||
| Ƙirƙira | 1 Oktoba 1996 | ||||
| Tsarin Siyasa | |||||
| Majalisar zartarwa |
supervisory councillors of Yenegoa local government (en) | ||||
| Gangar majalisa |
Yenegoa legislative council (en) | ||||
| Bayanan Tuntuɓa | |||||
| Lambar aika saƙo | 569101 | ||||
| Kasancewa a yanki na lokaci | |||||



Yenagoa[1] wata Ƙaramar hukuma ce[2] kuma babban birnin Jihar Bayelsa,[3] a kudancin Najeriya.[4] Tana cikin yankin Neja Delta na ƙasar a matsayi na 4°55′29″N 6°15′51″E.
Ƙaramar Hukumar tana da faɗin ƙasa da ya kai kilomita murabba’i 706 tare da kiyasin yawan jama’a da ya kai 798,466 a shekarar 2024.[5][6]
Lambar akwatin gidan waya (postal code) ta yankin ita ce 561.[7]
Al’ummar Ijaw su ne mafi rinjaye a Ƙaramar Hukumar.[8][9] Turanci shi ne harshen hukuma,[10] amma harshen Epie-Atissa na daga cikin harsunan gida da ake magana da su a Yenagoa,[5][11] yayin da Ekpetiama, Gbarian, Buseni da Zarama su ma wasu karin harsunan Ijaw ne da ake amfani da su a yankin Yenagoa.[12][13]
Filin jirgin saman Bayelsa (Bayelsa International Airport) filin jirgin sama ne da ke babban birnin Jihar Bayelsa wato Yenagoa, a kudancin Najeriya.[14] Filin jirgin saman ya karɓi jirginsa na farko ranar 14 ga Fabrairu, 2019.[15]
Yenagoa ita ce gida ga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta maza ta Bayelsa United, wadda ke taka leda a gasar Nigeria National League, da kuma ƙungiyar mata ta Bayelsa Queens wadda ke buga gasar NWFL Premiership. Ƙungiyoyin biyu sun lashe kofin Aiteo na shekarar 2021 a rukunin maza da mata bi da bi. An gudanar da wasan ƙarshe na maza a sabon filin wasa na Samuel Ogbemudia Stadium da ke Benin City.[16] Bayelsa United ta doke Nasarawa United da ci 4–3 a bugun fenariti bayan an tashi 2–2 a lokacin wasa da ƙarin lokaci.[17]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Yenagoa Archives". The Guardian (in Turanci). Lagos, Nigeria. Retrieved 2022-03-05.
- ↑ "Nigeria: Administrative Division (States and Local Government Areas) - Population Statistics, Charts and Map". www.citypopulation.de. Retrieved 2022-03-09.
- ↑ "Bayelsa State". BBC News Pidgin. Retrieved 2022-03-06.
- ↑ "About Yenagoa". City Of Yenagoa (in Turanci). Archived from the original on 2021-09-15. Retrieved 2021-09-15.
- 1 2 "population | Definition, Trends, & Facts | Britannica". www.britannica.com (in Turanci). Retrieved 2022-03-06.
- ↑ "MINA Ijaw Population Report 2024 Estimate | PDF | Nigeria". Scribd (in Turanci). Retrieved 2025-05-17.
- ↑ "Post Offices- with map of LGA". NIPOST. Archived from the original on 2012-11-26. Retrieved 2009-10-20.
- ↑ "Overview of Bayelsa – Niger Delta Budget Monitoring Group" (in Turanci). Retrieved 2022-04-20.
- ↑ Ariye, E. C. "The Ijo (Ijaw) People of Delta State: Their Early History and Aspects of Social and Cultural Practices" (PDF). Historical Research Letter. Online. 8: 1–2 – via IISTE.
- ↑ United Nations. "Official Languages". United Nations (in Turanci). Retrieved 2022-03-09.
- ↑ "Spoken languages of African countries - Nations Online Project". www.nationsonline.org. Retrieved 2022-03-06.
- ↑ "Bayelsa moves to save Izon language from extinction". Vanguard (in Turanci). Lagos, Nigeria. 2015-11-03. Retrieved 2021-09-16.
- ↑ Kolesnik, Kay (2018-10-30). "What do you know about Bayelsa State history?". Legit.ng (in Turanci). Retrieved 2021-09-16.
- ↑ "Bayelsa State Government – The Glory of all Lands" (in Turanci). Retrieved 2022-03-09.
- ↑ "Yenagoa Bayelsa Airport Profile | CAPA". centreforaviation.com. Retrieved 2021-09-14.
- ↑ "Samuel Ogbemudia Stadium best in Nigeria —Kwara dep gov". The Punch (in Turanci). 2021-04-10. Retrieved 2022-03-12.
- ↑ "Bayelsa United upset Nasarawa United as Yenagoa clubs rule Aiteo Cup". The Guardian (in Turanci). Lagos, Nigeria. 9 August 2021. Retrieved 2021-09-18.
