Kwami

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kwami

Wuri
Map
 10°30′N 11°18′E / 10.5°N 11.3°E / 10.5; 11.3
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaJihar Gombe
Labarin ƙasa
Yawan fili 1,787 km²
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci

Kwami karamar hukuma dake Jihar Gombe, a arewa maso gabashin Najeriya.[1] Hedikwatan ta yana garin Malam Sidi. Kwami yana iyaka da tafkin Dadin Kowa a gabas, a arewa kuma yana iyaka da funakaye da Gombe a kudu. Lambar gidan waya na yankin ita ce 760.

Yawan jama'a[gyara sashe | gyara masomin]

Yawan mutanen Kwami a kidayar shekarar 2006 ya kai dubu ɗari da chasain da biyar da ɗari biyu da chasain da takwas, 195,298.

Yankin wuri[gyara sashe | gyara masomin]

Karamar hukumar Kwami tana da fadin kasa murabba'in kilomita 1,787 kuma tana kan gabar tafkin Dadinkowa. Yankin ya shaida manyan yanayi guda biyu wadanda suka hada da lokacin rani da damina. Matsakaicin zafin jiki a karamar hukumar Kwami shine 32 °C.

Tattalin arzikn Kwami[gyara sashe | gyara masomin]

M Mazauna garin Kwami suna yin ayyuka daban-daban na tattalin arziki amma abin da ya fi yawa shi ne noma da kamun kifi.

Kayan aiki[gyara sashe | gyara masomin]

A watan Disambar 2022, Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya jaddada shirin gwamnatin jihar na fara aikin titin da ya hada Kwami da Malam-Sidi, hedkwatar karamar hukumar, domin rage kalubalen gudanar da mulki da samar da ci gaban tattalin arziki da zamantakewa ga al’ummar karamar hukumar.

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.

Yanayi (Climate)[gyara sashe | gyara masomin]

Lokacin rani da damina sune biyu da suka fi yawa a yankin. Karamar hukumar kwami yana fuskantar 32 °C akai-akai

Manazarta.[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://punchng.com/gombe-gov-visits-kwami-lg-meets-only-revenue-officer/