Jump to content

Damaturu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Damaturu


Wuri
Map
 11°45′N 11°58′E / 11.75°N 11.97°E / 11.75; 11.97
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin NajeriyaJihar Yobe
Babban birnin
Yawan mutane
Faɗi 88,014
• Yawan mutane 37.2 mazaunan/km²
Labarin ƙasa
Yawan fili 2,366 km²
Altitude (en) Fassara 371 m
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci

Damaturu yanki ne na karamar hukuma kuma babban birnin Jihar Yobe a arewacin Najeriya . [1] Shi ne shedkwatar Masarautar Damaturu .

Wani shatele-talen titi a garin Damaturu
Kasuwar zamani ta Burabura wacce ake ginawa

Damaturu babban birni ne kuma shedikwatar gudanarwar mulki na jihar Yobe kuma inda gwamnan ke zaune, kuma ma'aikatu da hukumomin gwamnatin jihar duk suna zaune acan.

Damaturu tana ɗauke da manyan makarantu uku, Kwalejin fasaha ta gwamnatin tarayya Damaturu, Jami'ar Jihar Yobe da Kwalejin koyon aikin jinya

Damaturu ta samu ne a matsayin gunduma a lokacin da turawan Ingila suka cire ta daga yankin Alagarno . Matakin da Birtaniya ta ɗauka ya haifar da mamayar daular Borno a shekarar 1902 da sojojin mulkin mallaka karkashin jagorancin Kanal Thomas Morland suka yi.

Damaturu ta sha fuskantar hare-hare lokaci da yawa na mayakan kungiyar ta'addaci na Boko Haram a yakin da suke yi na kafa shugabanci a yankin arewa maso gabas. [2]

A watan Nuwamban shekarar 2011, sun kashe sama da mutum 100 a wasu jerin hare-hare da suka aiwatar.

A watan Disambar 2011, sun aiwatar da hare -haren bama-bamai guda biyu .

A watan Yunin shekarar 2012, mahara 40 sun kutsa gidan yari. Fursunoni 40 ne suka tsere sannan aka kashe mutane takwas.

A watan Yunin shekarar 2013 ne maharan suka kai hari s wata makaranta inda suka kashe mutane goma sha uku da suka hada da dalibai da malamai.

A watan Oktoba 2013, mayakan masu shigar jami'an tsaro dauke da dogayen bindigu da kayan yaƙi sun kawo farmaki wani asibiti.

A watan Disambar 2014, mayakan sun sake kai hare-hare. An ji karar harbe-harbe da fashe-fashe, an kuma ce an kona sansanin 'yan sandan kwantar da tarzoma. Haka kuma an buɗewa jama'a wuta a harin jami’ar jihar Yobe.

A watan Fabrairun shekarar 2015, wata budurwa 'yar kunar bakin wake ta kashe mutane goma sha shida a wata tashar yawan mota.

A cikin watan Fabrairun shekarar 2020, an aiwatar da kisan kiyashi a garin Auno da ke kan babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri (Borno). Maharan sun kashe matafiya 30, sun kona ababen hawa tare da yin ɗibar mutane domin neman kuɗin fansa mutane. [3] [4] [5]

Lambar akwatin gidan saƙo na yankin ita ce 620. [6] Karamar hukumar tana da faɗin ƙasar km 2,366. 2 da yawan jama'a da suka kai kimanin 88,014 a ƙidayar da akayi 2006.

Garin Damaturu yana kan babbar hanya matakin A3 kuma a shekarar 2010 yana da yawan adadin jama'a dayakai 44,268. [7]

Layin arewa maso gabas daidai latitude da longitude ya ratsa yankin, gami da ma'aunin digiri 12°00'00"N 12°00'00"E a arewa

Yanayin damina a Damaturu na da tsanani da matsi da kuma yanayin gajimare, yayin da lokacin rani ba shi da dadi, iska, da wani bangare na yanayin hazo. Matsakaicin yanayin zafin jiki na shekara yana daga 58 zuwa 104 Fahrenheit, tare da 52 da 109 Fahrenheit kasancewar ba kasafai bane. [8] [9] [10] Mafi girman lokacin ziyarar Damaturu don ayyukan yanayi na yanayi, bisa ga ma'aunin yawon shakatawa, shine daga tsakiyar Disamba zuwa farkon Fabrairu.

Matsakaicin sauyin yanayi a Damaturu

[gyara sashe | gyara masomin]

Daga 12 ga Maris zuwa 23 ga Mayu, lokacin zafi ne, ana samun matsakacin yawan zafin rana da ya wuce 100F, yana ɗaukar watanni 2.4. A Damaturu, watan Afrilu shine watan mafi zafi a shekara, inda matsakaicin zafi akowane rana yana kai kai 104°F kuma kasa da 76°F.

Daga 18 ga Yuli zuwa 26 ga Satumba, sanyi, wanda ke da matsakaicin zafin rana ƙasa da digiri 90 ° F, yana ɗaukar watanni 2.3. A Damaturu, watan Janairu shine watan da yafi sanyi a shekara, inda matsakaicin matsakaicin zafin jiki ya kai 58 ° F kuma sama da 90 ° F. [11]

A cikin kowace shekara, Damaturu tana samun sanannen sauyin yanayi a matsakaicin kaso na rufewar gajimare a samaniya.Lokacin washewar samaniya a Damaturu yana farawa ne daga 6 Nuwamba kuma yana ƙarewa kimanin watanni 4.zuwa 5 ga Maris. Sama tana washewa tarwai ko wani ɓangare da kashi 61 cikin 100 lokacin watan Janairu, wanda shine lokaci nufi washewa a shekara a Damaturu. Kimanin 5 ga Maris shine lokacin da gajimare yake farawa, kuma yana ɗaukar kimanin watanni 8. yana ƙarewa 6 ga Nuwamba. A Damaturu, watan Mayu shi ne watan da ya fi gajimare a shekara inda ake samun hadari a samaniya da kashi 67% na sararin sama. [11] [12]

  1. "Damaturu | Location & Facts | Britannica". www.britannica.com (in Turanci). Retrieved 15 February 2022.
  2. "Boko Haram attacks Yobe community, targets Damaturu, destroys phone..." (in Turanci). 16 February 2020. Retrieved 21 February 2020.
  3. "30 Killed in Boko Haram Attack on Maiduguri-Damaturu Highway". THISDAYLIVE (in Turanci). 10 February 2020. Retrieved 21 February 2020.
  4. "Many stranded as Boko Haram attacks communities on Damaturu-Maiduguri road". TheCable (in Turanci). 6 January 2020. Retrieved 21 February 2020.
  5. "Boko Haram seizes Damaturu-Maiduguri road, travelers stranded". Pulse Nigeria (in Turanci). 6 January 2020. Retrieved 21 February 2020.
  6. "Post Offices - with map of LGA". NIPOST. Archived from the original on 26 November 2012. Retrieved 20 October 2009.
  7. "The World Gazetteer". Archived from the original on 1 October 2007. Retrieved 4 April 2007.
  8. "Damaturu Climate, Weather By Month, Average Temperature (Nigeria) - Weather Spark". weatherspark.com (in Turanci). Retrieved 16 July 2023.
  9. "Damaturu, Yobe, NG Climate Zone, Monthly Averages, Historical Weather Data". tcktcktck.org. Retrieved 16 July 2023.
  10. "Climate & Weather Averages in Damaturu, Yobe, Nigeria". www.timeanddate.com (in Turanci). Retrieved 16 July 2023.
  11. 11.0 11.1 "Damaturu Climate, Weather By Month, Average Temperature (Nigeria) - Weather Spark". weatherspark.com (in Turanci). Retrieved 21 August 2023.
  12. "Climate & Weather Averages in Damaturu, Yobe, Nigeria". www.timeanddate.com (in Turanci). Retrieved 2024-08-15.