Mai Mala Buni
![]() | |||||
---|---|---|---|---|---|
![]() | |||||
25 ga Yuni, 2020 -
29 Mayu 2019 - ← Ibrahim Gaidam | |||||
Rayuwa | |||||
Cikakken suna | Mai Mala Buni | ||||
Haihuwa | Jihar Yobe, 19 Nuwamba, 1967 (57 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Harshen uwa | Hausa | ||||
Karatu | |||||
Makaranta |
Leeds Beckett University (en) ![]() | ||||
Matakin karatu |
BSc in Politics and International Relations (en) ![]() master's degree (en) ![]() | ||||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Wurin aiki | Jihar Yobe | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Mai mala Buni, An haife shi ran 19 ga watan Nuwamba, shekara ta alif dari tara da sittin da bakwai 1967) Miladiyya. (A.c) ya kasance ɗaya ne daga cikin manya kuma jiga-jigan ƴan siyasar Najeriya. An haife shi a Buni Yadi dake karamar hukumar Gujiba, a Jihar Yobe, Najeriya. A halin yanzu shi ne zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Yobe mai ci kuma shine shugaban riƙo na babban kwamatin riƙon ƙasa na jam'iyyar APC dake shugabancin Najeriya.[1][2]
Kafin zaben Gwamnan jihar Yobe, shine sakataren Jam'iyyar All Progressives Party (A.P.C) na ƙasa.
Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]An zabi Mala Buni gwamna ne a babban zaben Najeriya na shekarar 2019 a watan febairu, ƙarƙashin jam'iyya mai mulki All Progressives Congress (APC).[3][4] gabanin zaɓensa gwamna Mai Mala Buni shi ne Shugaban riƙo na jam'iyyar All Progressives Congress a yanzu bayan tsige tsohon shugaban jam'iyyar Adam Oshiomole.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Mai Mala Buni is Yobe gov-elect". The Nation Nigeria (in Turanci). 2019-03-11.
- ↑ "Guber Poll: APC's Buni in early lead in Yobe". The NEWS (in Turanci). 2019-03-10.
- ↑ admin (2018-10-01). "APC's National Secretary Mala Buni Wins Yobe Governorship Ticket". Sahara Reporters.
- ↑ Usman, Shehu (2019-03-11). "Yobe guber election: Governor-elect, Buni reacts to victory, warns gossip, rumor merchants". Daily Post Nigeria (in Turanci).