Masarautar Damaturu
Masarautar Damaturu | ||||
---|---|---|---|---|
masarautar gargajiya a Najeriya | ||||
Bayanai | ||||
Ƙasa | Najeriya | |||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | Jihar Yobe |
Masarautar Damaturu masarauta ce ta gargajiyar Najeriya da ke Damaturu, babban birnin jihar Yobe, Nigeria. Masarauta ce ta farko.
A wani lokaci Masarautar Damaturu tana daga cikin masarautar Ngazaragamo, wacce ke garin Gaidam kuma ta fadada har zuwa Chadi ta gabas da Nijar zuwa arewa.
A watan Nuwamban shekara ta dubu biyu da uku 2003, gwamnan jihar Yobe, Bukar Ibrahim, ya amince da nadin Baba Shehu Hashimi II Ibn Umar El-Kanemi a matsayin Shehu (Sarkin) Damaturu. Hashimi II El-Kanemi an nada shi Sarkin Damaturu a ranar 15 ga watan Mayun shekara ta 2004. Ya gaji dan uwansa Alhaji Bukar Ibn Elkanemi, wanda ya mutu a Makka shekarar da ta gabata.
Hashimi Ibn El-Kanemi ya samu difloma a fannin Akantoci da Bincike a shekara ta 1988 a Ramat Polytechnic, Maiduguri, da kuma difloma difloma daga Tafawa Balewa University, Bauchi a shekara ta 2002. Ya yi aiki a matsayin mai karbar kudi tare da wani kamfanin gona a Damaturu daga shekara ta 1983-1987, sannan ya yi aiki a karamar Hukumar Damaturu a matsayin akawu. Bayan an kirkiro jihar Yobe a shekara ta 1991, ya koma gwamnatin jihar sannan zuwa shekara ta 1996 ya zama Daraktan Kudi da Kaya a Ofishin Gwamna. A cikin shekara ta 2000 dan uwansa ya nada shi Hakimin Damaturu.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]