Danja
![]() | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jerin jihohi a Nijeriya | Jihar Katsina | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 501 km² | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Danja karamar hukuma ce dake a Jihar Katsina, Arewa maso yamman Nijeriya.
An kirkiri Danja ne a shekarar 27/9/1991 An fiddata ne a karkashin karamar hukumar Bakori Jahar Katsina
Ɗanja garin jajaye in kaga baƙi, baƙo ne, marmara ci ‘yar uwar ki ki kwana[1]. P25. Akwai saɓani mai yawa tsakanin masana, game da ainhin wanda ya far kafa garin ɗanja. Ance wani bamaguje ne mai suna ɗanjakau wanda kwararren manomi ni kuma maharbi wanda ya gina rijiya mai zurfin gaske fiye da kafa arba’in da shida[1], sannan kuma ance ja ne, daga garin ɗanja ya kafa wannan garin. A wani ƙaulin kuma har wa yau ance wani mutum ne mai suna ɗanja, ya kafa garin[1].
A zamanin sarkin ɗanja duna ne ya kori dukkan maguzawan dake cikin garin dan ja shi kuma ya gina ganuwar garin[2].
Tarihi ya nuna cewa kwararrafa taci garin danja da yaƙi wanda daga nan ne mutane daga wurare daban daban kamar mutanen likoro, da wazata daga ƙasar zazzau daga kagoro, daga kogo, da bare bari daga gobirawa da kanawa suka kafa unguwannin su a wurare dabam daban wanda t hakan aka samu unguwar kanawa, unguwar fulani, da unguwar gobirawa, da unguwar kagora da sauransu a garin ɗanja[2].
Bayan jihadin shehu usman dan fodiyo an sami zaman lafiya a dukkan ƙasashen hausa da bunƙasan kasuwan da lilin musulunci da kuma ƙarin yawan garuruwa[2]. A lokacin sarkin katsina Muhammad Dikkko ne aka fara gyar ganuwar ɗanja, kuma canza wa kofofin suna zuwa kofar Arewa, kudu, yamma da Gabas[2].
Daga cikin abubuwan tarihin garin ɗanja sun hada da rijiyar ɗanja da ɗanja ya gina, sannan akwai rijiyar duhu wanda idan dare yayi za’ayi ta jin kiɗa na tasowa daga cikinta saboda wannan dalilin ba mai ƙara zuwa bakin rijiyar da zarar magariba ta yi sannan shi kansa kabarin ɗanja yana nan a gindin wata giginya kan tsauni dake tsakanin ɗanja zuwa dabai[3]. Sannan akwai wata kuka mai kogo a ƙofar yamma inda ake haƙo ƙarfen tama don ƙera makaman yaƙi da gyara su tun kafin jihadin shehu usman ɗan fodio[3].
Cigaba
A shekara ta 1903 aka bude kasuwar ɗanja kuma an buɗe fulotin sayan auduga a 1913. Wanda a wannan shekarar har wa yau aka samo gundumar ɗanja, aka naɗa “’iya labaran” matsayin hakimin ɗanja a 1914[3]
An kafa kamfanin buredin “bega” a 1918.
A shekarar 1921 kuma aka gina kurkuku da makarantar elementary.
Har wa yau an gina rijiyar kwakware a 1946.
An gina hanyar ɗanja zuwa bakori a 1947 sannan aka gina ɗanja zuwa zariya a 1951.
An bude asibitin zamani a ɗanja a 1956.
NTC ta buɗe ofishin ta ta kuma gonar taba a ɗanja shekara ta 1962.
A garin ɗanja kuma aka gina kamfanin mazarkwaila na farko a duk fadin garin katsina.
Har wa yau akwai fim na “baban larai” wanda yayi suna a ƙasar hausa, anyi shine a ɗanja wanda ‘iya iro ne magajin farko da ya fara hawa babur a duk katsina.
A shekarar 1977 aka bunkasa babbban asibitin ɗanja ya zama babban asibiti.
Haka kuma nayi hanyar bakori zuwa ɗanja wacce ta zarce zuwa hunkuyi har ta hadu da titin zariya 1978.
A 1974 aka bude “sito da ofishin DI’o’” na frojet a shekara ta 1980.
Gundumar ɗanja ta samu zama ƙaramar hukuma a ranar 24 ga watan satumba a 1991[4].
Tarihin sarautar ɗanja da masana suka nuna ya fara daga lokacin da akai wa ɗanja Ganuwa a 1913 aka taro makaman Katsina Iya Labaran ya fara zama Hakimin Ɗanja. Sai kuma Makama Idi (1928 - 1938) wanda ya zauna a Bakori, sannan an samu canjin suna daga Iya zuwa Makama daga lokacin Makama Idi, Bayan shekara ta 1939 aka koma ana kirar sarautar Ɗanja Sarkin Fulani. Daga 1992 har wa yau bayan ƙirƙiro gundumar Ɗanja aka canza sunan sarautar zuwa Sarkin Kudun Katsina[4].
SUNAYEN WASU DAGA CIKIN SARAKUNAN ƊANJA SU NE:
1. Makaman Katsina Iya Labaran 1914 – 1928
2. Makaman Katsina Idi 1928 – 1938
3. Sakin Fulani Ibrahim 1939 – 1953
4. Sakin Fulani Muntari 1953 – 1956
5. Sakin Fulani Usman 1956 – 1987
6. Sakin Fulani Abubakar Sadiq 1987 – 1991
7. Sarkin Kudu Muhammau Yazid Sadiq 1991 –[5]
Biblio[gyara sashe | Gyara masomin]
Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Danwaire : gwanki sha bara. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. ISBN 978-2105-93-7. OCLC 59226530.
Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]
- ↑ 1.0 1.1 1.2 Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Danwaire : gwanki sha bara. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p.25 ISBN 978-2105-93-7.
- ↑ 2.0 2.1 2.2 2.3 Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Danwaire : gwanki sha bara. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p.26 ISBN 978-2105-93-7.
- ↑ 3.0 3.1 3.2 Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Danwaire : gwanki sha bara. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p.27. ISBN 978-2105-93-7.
- ↑ 4.0 4.1 Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Danwaire : gwanki sha bara. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. pp.27-28. ISBN 978-2105-93-7. .
- ↑ Tarihi, Hukumar Binciken. (1996). Danwaire : gwanki sha bara. Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu ta Jihar Katsina. Katsina: [Dab'in Lamp?]. p.29. ISBN 978-2105-93-7. .