Jerin jihohi a Nijeriya
Appearance
Jihohin Najeriya | |
---|---|
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | Yankunan Najeriya, federated state (en) da first-level administrative division (en) |
Ƙasa | Najeriya |
Najeriya, Jamhoriya ce mai jihohi 36 da babban birnin taraiya 1. Ko wacce jiha na da matsakaicin iko na gudanarwa da tafiyar da mulki karkashin ikon gwamnatin taraiya. Gwamnatin taraiyar na da mazauni ne a babban birnin taraiyar dake Abuja. Babban birnin taraiyar ba jiha bane, amma wani yankin gudanarwa ne wanda ke dauke da zababbun wakilai a majalisar taraiya tare da sa idon gwamnatin taraiya. Ko wacce jiha ta kasu ne bisa ga kananan hukumomi. A yanzu akwai kananan hukumomi 774 a Najeriya.
Samar da jahohi
[gyara sashe | gyara masomin]Teburi mai nuna tarihin yadda aka samar da jahohi.
Kwanan wat | Wajen da aka kaddamar | Taswirs |
---|---|---|
1960-1963 | A lokacin samun yancin kan Najeriya a 1960, a lokacin an samar da yankuna uku: Yankin Arewa, Yankin Yamma, Yankin Gabas. | |
1963-1967 | A 1963, aka sake samar da sabon yanki, an samar da shi ne a Yankin Yamma ta tsakiya. | |
1967-1976 | A 1967, aka maye gurbin kowanne yanki da jihohi 12. Daga 1967 zuwa 1970 yankin Gabashin Najeriya yayi yunkurin ballewa domin kafa kasar Biafra. | |
1976-1987 | A 1976, aka kirkiri sababbin jahohi bakwai, wanda ya hada su suka zama 19 gaba daya.[1] | |
1987-1991 | A wannan lokacin, akwai jihohi 21 da babban birnin taraiya, Abuja. | |
1991-1996 | Wa nannan lokacin, akwai jihohi 30 da babban birnin taraiya. An kirkiri babban birnin taraiya a shekarar 1991. A 1987 aka sake kirkirar wasu karin jihohi biyu. Kari na karshe shine na 1996, lokacin da mayar da su jihohi 36. |
Rabe rabe
[gyara sashe | gyara masomin]Rarrabuwa da yadda aka kirkiri jahohin Najeria.
Duba
[gyara sashe | gyara masomin]Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Kraxberger, Brennan (2005) "Strangers, Indigenes and Settlers: Contested Geographies of Citizenship in Nigeria" Space and Polity 9(1): pp. 9-27, pages 10, 11, & 15