Shehu
Jump to navigation
Jump to search
Shehu kalmace da aka samota daga larabci (شيخ) kuma ana amfani da itane ga mutumin da ilimin mai yawa.
- Sheik (shehu) tana nufi babban malami wanda yake da matukar sani a fannikan ilimi daban-daban
- Ma'anarta a wunin sufaye tana nufin duk mutumin da ilimin sa yakai a yi masa tambayoyi guda dubu kuma yabada amsar su atakai
Ma'anar ta da larabci
- Tana nufin mutum wanda yake da yawan shekaru
- Tana nufin mutum wanda yake jagorancin wani addini
- mutum da yake da girma a wata ƙabila
- mutum da yake jagorancin wata ƙabila
- Tana nufin Mutun mai yawan shekaru musamman ma daga shekara hamsin zuwa shekara tamanin
Anyiwa mutane da yawa lakabi da kalmar shehu a kasar hausa sun da yawa, Wanda suke manyan masana da manyan malamai da manyan mutane a kasar hausa da wasu sasa na duniya.
Daga cikin na kasar hausa sunda da shehu Usman dan Fodio wanda akafi sani da mujadadi, Kuma ana yiwa mafiyan yaron da akasa masa sunan shehu usman wto usman da shehu dimin girmamawa agare shi da nuna kimar sunan sa da al-farmar da yake da ita wajen musulmai musanmanma mutanen arewacin Najeriya da kuma mutanen Nijer.
Wasu daga cikin shehunne[gyara sashe | Gyara masomin]
- Shehu Usman dan Fodio
- Shehu Atiku Salga
- Shehu Abdurrahman Suyudi
- Shehu Abdulkadir Jilani
- Shehu Ahmadu Tijjani
- Shehu Nasiru Kabara
- Shehu Ibrahim Inyas
- Shehu Abdullahi fodio (Gwandu)