Jump to content

Atiku Salga

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Shehu Abubakar Atiku ko Atiku Salga Marigayin ɗan Halliru dan Abubakar dan Musa (Mairisala) an haife shi a shekarar alif dari takwas da casa'in da shida 1896 a garin Katsina.

Asalin sa da Tashin sa

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Mahaifinsa Malam Halliru da kakansa malam Abubakar duk haifaffun Katsina ne. Amma kuma mahaifin kakansa Mallam Musa (Mairisala) yazo ne daga kasar Tunis shi da kuma jama’arsa; shi yasa a ke ce musu Rumawa. Dalilin kiransa da Mairisala kuwa shi ne malamin fikhu na farko da ya kawo littafin Risala kasar Hausa lokacin da ya je aikin Hajji ya gamu da ‘yan’uwansa Larabawan kasar Tunis sai ya fansheta daga wajensu ya kuma taho da ita kasar Hausa ya kuma yaɗa ta.
  • Shehu Abubakar Atiku ya girma a hannun ‘yar’uwar kakarsa mai suna Rahmatu (Yaya Babba) matar malam Abba Dan Fannah a Dandalin Turawa da ke Kano. Ta dalilin kulawarta ne har yay i karatun alkur’ani a hannun mijinta. An shaidi Rahmatu da maca ce mai ibada da tsananin riko da addini. Jajirtacciya mai bin tafarkin darikar Tijjaniya sau da kafa. Sannan mai zartaccen Imani cikin Shehu Ahmadu Tijjani. Ita ce ta tsaya, tsayin daka a tarbiyyarsa har zuwa lokacin da Allah ya yi mata rasuwa a shekarar 1972.

Karatun Addini

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Shehu Atiku ya fara da karatun al-kur’ani a hannun mijin kakarsa Malam Abba Dan Fanna haka ya yi ahalari da kurdabi da alburda da Badamasi duk a wajensa. Daga nan sai ya koma da karatu a wajen Shaihu Muhammadu Salga dan Alhaji Umaru inda ya karanci risala da Iziyya da arshada ta ibn Rushidi da Mukhtasarul Khalil har zuwa babin aure, sannan ya kuma karanta littattafan akida kamar Mukaddamatul Burhamiyya ta Imamu Sunusi da Akidatul wusda da sauransu.
  • Ya karanci littatafan darika kamar su ‘Su’al wal jawab’ na shehu Muhammadu Salga da ‘Yakutul faridah’ na shehu Nazifi. Ya ci gaba da neman ilimi a fannoni da dama kamar tafsiri da Hadisi da harshen Larabci inda ya karanci littattafan Alfiyya ta dan Malik da Ajrumiyya da Mulhatul I’irab da sauransu.

[1]

Ilimin Addini mai zurfi

[gyara sashe | gyara masomin]

Shehu Atiku ya zurfafa iliminsa da neman ilimi a fannonin fikhun darika da tasawwuf da sauran fannonin harshen Larabci a wajen Shehu Abubakar Mijinyawa Bakin ruwa. Ya karanta littafai kamar haka a gun Shehu Mijinyawa kamar su Jawahirul ma’any da Durratul Kharidah ( Sarhin Yakutatul Faridah) [2] da Bugyatul mustafida na shehu Arabi da Alfiyatul tasawwuf ta shehu Mustapha da sauran littattafai da dama Shehu Atuku Sanka ya karbi darikar Tijjaniya a hannun Shehu Muhammadu Sanka a shekarar 1916. Sannan ya yi tarbiyyar Ruhi a hannun Shehu Abubakar mijinyawa. Shehu Atiku na Shehu bai tsaya a karatun littattafai ba, a’a har da harshen Larabci saboda shi ne harshen da malamai kan yi muhawara da shi a tsakaninsu a garin Kano a wancan lokacin. Ya karanta ilimin hisabi a wajen Muhammadu dan Ajurum da Mulhatul-irab ta Imamu Hariri mai littafin mukamah da sauran littattafan da suka shafi adabi da kuma lugga (Harshe) da kuma ka’idojin Larabci. Shehu Atiku na daya daga cikin manyan shaihunnan malamai na garin Kano da ma Afrika baki daya wanda tarihi ba zai taba mantawa da sunansa da gudummawarsa musamman a garin Kano da Najeriya da ma Afrika baki daya. Shehi Atiku ya kasance Shaihin darika wadda ya yi mata hidima jini da tsoka da tunaninda da lokacinsa da ruhinsa. Shehu Atiku ya wallafa litttattafai da daman gaske wadanda a kiyasi ana da tabbacin sun haura casa’in tun daga na rubutun zube da rubutattun wakoki wanda mafi yawa suna Magana ne a kan al’amuran addini da harshen larabci da kuma sufanci. A takaice rubuce-rubucensa sun kasu gida uku wato Sufanci da Adabi da kuma Fikhu.

Wallafa Littafi da Wakoki

[gyara sashe | gyara masomin]

Babu shakka Shehu Atiku ya yi gagarumin kokarin da ba za a raina ba dangane da rubuce-rubucensa na litattafai, da kuma tsara wakoki a harshen Hausa da Larabci a kan abubuwa daban-daban. Misali ya rubuta wakoki na Yabon Annabi S.A.W, Yabon Shehi Tijjani da Shehi Ibrahim Inyass, Wa’azi da gargadi Akida, Ibada. da sauransu. daga cikin wakokinsa akwai;

  1. -Tusamma
  2. -Taimakon Dakiki
  3. -Asma’u zatil jamali
  4. -Matserar mata
  5. -Nasiha ga ‘yan’uwa
  6. -Yabon fiyayyen halitta
  7. -Arzikin masoya
  8. -Tarihin kwaki
  9. -Begen Muhammadu
  10. -Rakada’u

Matsayin sa

[gyara sashe | gyara masomin]

Shehu Atiku Sanka yana da madaukakiyar daraja a wajen malaman amaninsa musamman ta bangarorin ilimai daban-daban tare da karfin hujja da kwarewa wajen bincike da gogewa wajen hujja da fasahar zance. Kuma ya nutse aa cikin ilimin sanin darikar Tijjaniyya hakan ta sanya ya himatu da darussan ta da bincike a kanta har sai da ya zamana ba shi da wanda za a kwatanta shi da shi a wannan fanni. Shehi Atiku malami ne da har a karshen rayuwarsa yana neman sani, mai hakuri da rashin gazawa da kyauta da daukar nauyi. Gidansa ya zama sansani na neman sani inda almajirai ke zuwa daga ko’ina a fadin kasar nan har da Nijar. Daga cikin Almajiransa akwai:-

  1. Shehu Balarabe Jega
  2. Shehu Ibrahim Alti Funtua
  3. Shehu Ahmad Abulfathi Maiduguri
  4. Shehu Muhammadu Jibiya
  5. Shehu Yahya Jibiya
  6. Shehu Muhammadu Birnin magaji
  7. Shehu Ibrahim Kaya
  8. Shehu Adamu Katibi
  9. Shehu Imrana Damari

Allah ya yi wa Shehi Atiku rasuwa ranar laraba 9 ga watan rabi-ul thani 1394 Hijiriyya. Yana da shekaru 64 an binne shi a makabartar Gwauron Dutse.