Audu Bako

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Audu Bako Tsohon kwamishinan yansanda ne Mai ritaya (anhaifeshi a 1924) Shine gwamnan farko na jihar Kano, Nijeriya a lokacin mulkin soja na General Yakubu Gowon bayan kafuwar jahar daga yankin Arewacin Najeriya.

Tarihin sa[gyara sashe | Gyara masomin]

An haifi Audu Bako a shekarar 1924 a Barikin yansanda dake Kaduna. Mahaifinsa yayi aikin dansanda na tsawon shekaru 36. Audu yayi karatu a Makarantar Kaduna Government School da kuma Zariya Middle School. Bako ya shiga aikin dansanda a 1942. [1]

Gwamnan Jihar Kano[gyara sashe | Gyara masomin]

An nada shi a matsayin Gwamnan Jihar Kano a lokacin tshohuwar jahar ta Kano a 1967 lokacin mulkin soja.

Bako yayi aiyukan raya kasa sosai a jahar ta kano. A shekarar 1969 ya fara gina madatsar ruwa ta Bagauda. Tsakani 1970-1973 gwamnatinsa ta ginan babbar madatsar ruwa ta Tiga, domib bunkasa harkar Noma.

Aikinsa na samar da ruwansha na Timas Danbatta ya tsaya, har sai a shekarar 2008 sannan aka karasa shi inda ake samar da ruwan sha ga kananan hukumomin Dambatta, Makoda da Minjibir.

Rayuwar sa[gyara sashe | Gyara masomin]

Bako yayi ritaya a 1975 lokacin mulkin retired in 1975 Murtala Muhammed inda ya kama aikin noma a jahar Sokoto. Ya rasu a 1980 yabar mata da yaya 11. Bayan rasuwar sa an sauya ma matsar ruwa ta tiga zuwa sunan [2] Audu bako yasha samun kyaututtuka a wasannin kwallon doki (wato Poli).

Ana matukar girmama Bako sosai.[3]

Mazanarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. John N. Paden, Religion and political culture in Kano, University of California Press, 1973, ISBN: 0-520-01738-2, p. 339.
  2. Raph Uwechue, Africa who's who, Volume 1, Africa Journal Ltd. for Africa Books Ltd., 1981, ISBN: 0-903274-14-0, p. 71.
  3. Beverly Blow Mack, Muslim women sing: Hausa popular song, Indiana University Press, 2004, ISBN: 0-253-21729-6, p. 66.