Jump to content

Mohammed Ndatsu Umaru

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mohammed Ndatsu Umaru
gwamnan jihar Kano

Disamba 1987 - 27 ga Yuli, 1988
Ahmed Muhammad Daku - Idris Garba
gwamnan jihar Kwara

ga Augusta, 1985 - Disamba 1987
Salaudeen Latinwo (en) Fassara - Ahmed Abdullahi (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa 1950 (73/74 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Mohammed Ndatsu Umaru Gwamnan Soja ne a Jihar Kwara, Nijeriya daga watan Agusta a shekarar 1985 zuwa Disamban shekara ta 1987, sannan kuma ya yi Jihar Kano daga Disamba a shekarar 1987 zuwa Yuli shekara ta 1988 a lokacin mulkin soja na Janar Ibrahim Babangida.[1]

Rayuwar farko

[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 21 ga watan Yuni, a shekara ta 1986, ya buɗe wani sabon gini da aka kammala a Ilorin, jihar Kwara domin ya zauna da sakatariyar kungiyar ƴan jarida ta Najeriya. An shirya rusa ginin ne a watan Yulin a shekara ta 2009 domin samar da filin ajiye motoci yayin ziyarar kwana guda da shugaba Umaru Ƴar'aduwa ya shirya.[2]

A watan Oktoba na shekara ta 1986 ya shirya rabon hatsi ga manoman jihar Kano da ƙwari suka lalata amfanin gonakinsu.[3] A matsayinsa na gwamnan jihar Kano, a shekara ta 1988, Kyaftin Mohammed Ndatsu Umaru ya kafa kwamitoci da suka zagaya jihar, da gudanar da taron jin ra’ayoyin jama’a da kuma shirya shawarwari kan dokoki da tsare-tsare domin magance matsalolin zamantakewa.[4]

  1. "Nigerian States". WorldStatesmen. Retrieved 2010-01-02.
  2. LANRE LAWAL (July 25, 2009). "NUJ, Saraki At Loggerhead Over Demolition Of Press Centre". Osun Defender. Archived from the original on 2011-07-25. Retrieved 2010-01-02.
  3. Mever Ayillaiozi Usman (14 October 1986). "Grain Relief for Kano Pest Victims" (PDF). New Nigerian. Archived from the original (PDF) on June 5, 2011. Retrieved 2010-01-02.
  4. Ujudud Shariff (27 January 2009). "Salute to Divorcees And Widows". Daily Trust. Retrieved 2010-01-02.