Jump to content

Kungiyar 'Yan Jaridu ta Najeriya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kungiyar 'Yan Jaridu ta Najeriya

Kungiyar 'Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ) ƙungiya ce ta ƙwararrun masaniyar kafofin watsa labarai da aka kafa don ciyar da lafiya da walwalar 'yan jaridar na Najeriya. Ƙungiya ce ta cinikayya mai zaman kanta ba tare da karkata zuwa siyasa ba ko kuma ra'ayin akida. NUJ an kafa ta ne bisa dogaro da tushe cewa yin magana da murya daya a matsayin ƙungiyar kwararru zata iya tura bukatun mambobinta musamman a bangaren yanayin aiki da Haƙƙoƙin: ‘yancin fadin albarkacin baki, aminci, tsaron aiki da kuma kyakkyawan albashi, daidaiton jinsi, 'yancin walwala, kariya daga haƙƙin mallaka da yaƙi da duk wani nau'i na nuna wariya da danniya. NUJ tana shiryawa tare da tallafawa kamfen da kuma nufin kare haƙƙin 'yan jarida da ƙarfafa yarjejeniyar gama kai.[1][2][3][4][5][6][7]

An kafa NUJ a ranar 15 ga Maris na shekara ta 1955 a Legas a lokacin gwagwarmayar neman ‘yanci daga Turawan mulkin mallaka na Najeriya. Tana da alaka da ƙungiyar kwadagon Najeriya. Membobinta sun karu daga guda 3,950 a shekara ta 1988 zuwa guda 35,000 a shekara ta 2005.

  1. "NUJ, others condemn harassment of journalists by Ebonyi Govt" (in Turanci). 2020-04-22. Retrieved 2020-05-30.
  2. "NUJ condemns attack on journalists in Osun" (in Turanci). 2019-03-18. Retrieved 2020-05-30.
  3. Onyeji, Ebuka (2018-08-16). "NUJ writes Osinbajo, accuses IGP Idris of hounding journalists" (in Turanci). Retrieved 2020-05-30.
  4. "Nigerian journalists discuss ways to ensure improved welfare, security for media practitioners" (in Turanci). 2018-08-29. Retrieved 2020-05-30.
  5. "NUJ President wants more protection for journalists". Pulse Nigeria (in Turanci). 2019-08-16. Archived from the original on 2019-09-14. Retrieved 2020-05-30.
  6. "NUJ rejects FG's plan to regulate social media" (in Turanci). 2019-11-01. Retrieved 2020-05-30.
  7. LeVan, A. Carl; Ukata, Patrick (2018). The Oxford Handbook of Nigerian Politics. Oxford: Oxford University Press. ISBN 0192526324.