Jump to content

Rabi'u Musa Kwankwaso

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Rabiu Musa Kwankwaso)
Rabi'u Musa Kwankwaso
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

Mayu 2015 - Mayu 2019
Basheer Garba Mohammed - Ibrahim Shekarau
District: Kano Central
gwamnan jihar Kano

Mayu 2011 - Mayu 2015
Ibrahim Shekarau - Abdullahi Umar Ganduje
Ministan Tsaron Najeriya

ga Yuli, 2003 - ga Augusta, 2006
Theophilus Yakubu Danjuma - Thomas Aguiyi-Ironsi
gwamnan jihar Kano

Mayu 1999 - Mayu 2003
Aminu Isa Kontagora - Ibrahim Shekarau
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya

1993 - 2019
Rayuwa
Haihuwa Madobi, 21 Oktoba 1956 (67 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Makaranta Middlesex University (en) Fassara
Loughbrough University of technology
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party
All Progressives Congress
New Nigeria Peoples Party (en) Fassara
kwankwaso.com

Muhammad Rabi'u Musa Kwankwaso (An haifi Dr. Rabiu Musa Kwankwaso a ranar Lahadi, 21 ga watan Oktoba[1] na shekara ta alif ɗari tara da hamsin da shidda (1956) miladiyya, a garin Kwankwaso da ke a ƙaramar hukumar Madobi ta jahar Kano[2] a jamhuriyar Najeriya[3].

Kwankwaso da Rochas

Dr. Rabiu Musa ya halarci makarantar firamare ta garin Kwankwaso, inda kuma daga nan ya samu ci gaba izuwa makarantar kwana ta Gwarzo, duk dai a neman ilimin firamare. Sannan sai makarantar kere-kere da ke a garin Wudil da kuma kwalejin fasaha ta Kano. Bayan daga nan ya garzaya makarantar kimiyya da fasaha ta Kaduna polytechnic da ke a garin Kaduna, a inda kuma ya samu yin difloma a fannin kimiyya da fasaha ta kasa, da babbar diploma duk a fannin kimiyya da fasaha. Ya samu yin makarantar gaba da sakandire a garin London da ke ƙasar Ingila a kwalejin Middlesex a shekara ta alif dari tara da tamanin da biyu zuwa da uku (1982 zuwa 1983). Kwankwaso ya ci gaba da karatunsa a jami’ar fasaha da ke Loughborough a kasar Ingila a shekara ta alif dari tara da tamanin da uku zuwa da biyar (1983 zuwa 1985) inda ya samu shaidar babban digiri na biyu mai suna Masters degree a turance a fannin fasahar ruwa. Rabi'u Musa Kwankwaso ya kasance hazikin mutum ne a kusan dukkan lokutan karatunsa musamman ta bangaren tsayawa da ya yi domin ganin cewa ya kammala karatu cikin nasara kuma ba tare da bata lokaci ba. Ya kasance dalibi wanda kullum ya ke a sawun gaba wajen karatu da yin dukkan wani aikin aji da aka bashi. An zabi Rabi'u Kwankwaso a matsayin shugaban dalibai a lokacin karatunsa, sannan ya kasance zababbe a kungiyar dalibai ta jihar Kano. Kuma a halin yanzu ɗan siyasa ne a Najeriya.[4]


SIYASA DA AIKI

[gyara sashe | gyara masomin]

Rabiu Musa kwankwaso ya fara aiki a shekara ta 1975, inda ya fara aiki da hukumar ruwa ta jahar Kano, wato Kano State Water Resources and Engineering Construction Agency wato WRECA ya kuma yi aiki na tsawon shekaru( 17), a ɓangarori daban-daban inda har ya zama shugaban ma'aikatar. A shekarar ta ( 1992), aka zabi Kwankwaso a matsayin dan majalisar wakilai ta taraiyar Najeriya mai wakiltar karamar hukumar Madobi. Kuma shi ne ya zama mataimakin kakakin majalisar a karkashin jamiyyar PDP A wani taro da akayi na gyaran kundin mulkin kasa, an zabi Rabi'u kwankwaso a matsayin wakilin jihar Kano. Ya shiga jam'iyyar PDP a shekara ta (1998).

Rabiu Kwankwaso

Ya rike matsayin gwamna a jahar Kano har sau biyu, wato a shekara ta (1999 zuwa 2003), da kuma shekara ta (2011 zuwa 2015). Shi ne Gwamnan farko na jihar Kano a jamhuriya ta hudu kuma ya ci zabe ne duk a karkashin jam'iyyar PDP kafin daga bisani ya chanza jam'iyya ya koma jam'iyyarsa ta APC. A zaben shekara ta (2003), Alh. Rabiu Musa Kwankwaso ya yi rashin nasara ne a hannun Mal.Ibrahim Shekarau. A watan Yuli na shekarar (2003), Olusegun Obasanjo Shugaban kasar lokacin, ya naɗa shi a matsayin Ministan tsaron Najeriya bayan samun rashin nasara da ya yi a zaben.

A shekara ta 2015, Rabi'u Kwankwaso ya yi rashin nasara a hannun Shugaba Muhammadu Buhari a zaben fidda gwani na dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, daga bisani sai ya canza sheka zuwa takarar kujerar Sanata Wanda a nan ne ya samu nasarar cin zaben a shekara ta 2018. Rabi'u Kwankwaso ya fice daga jam'iyyarsa ta (APC) inda ya sake komawa jam'iyyarsa ta da wato (PDP) da niyyar yin takarar Shugaban ƙasa, sai dai bai samu nasara a zaɓen fidda gwani ba wanda aka gudanar a garin Fatakwal. Ana masa lakabi da "kwankwansiyyah". A ranar Talata ne tsohon gwamnan jihar Kano, Musa Rabi’u Kwankwaso ya kawo karshen cece-ku-ce game da ficewar sa daga jam’iyyar PDP a lokacin da ya fice daga jam’iyyar zuwa Sabuwar jam'iyya New Nigeria Peoples Party (NNPP) tare da yin rijistar mamba a shirye-shiryen zaben 2023.

Ya yi rajistar jam’iyyar NNPP tare da samun katin zama dan jam’iyyar a yayin wani takaitaccen biki da aka gudanar a birnin Abuja. A cewarsa, ya fice daga PDP ne saboda gazawar shugabancinta da kuma rashin tsarin dimokuradiyya na cikin gida. Kwankwaso a yayin wani taron manema labarai da ya kira a Abuja, ya ce a shekarar 2021 ya yi watsi da harkokin jam’iyyar PDP kuma ya jira shugabannin jam’iyyar su tattauna da shi sama da shekara guda amma bai samu amsa ba. Ya ce ’yan Najeriya ba su gamsu da nasarorin da aka samu a karkashin Mulkin Jam'iyyar PDP da kuma Jam'iyyar APC ba, don haka suna fatan samun sauyi mai kyau a cewar sa. Ya ce, “A yau, wadanda ba su da tabbas (game da inda na ke) za su tabbata cewa na riga na shiga NNPP".

A shekara ta 2003, bayan ya faɗi zaɓe a karo na biyu a takatar Gwamnan Jihar Kano, Shugaban Kasa Olusugun Obasanjo ya naɗa shi a matsayin babban Ministan Tsaron Najeriya wanda ya riƙe na tsawon shekaru huɗu. Sannan an sake naɗa shi a matsayin Jakadan Najeriya a Dafur dake Ƙasar Sudan a ƙarƙashin gwamnatin marigayi Umar Musa Yar’adua.

1. Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya a watan Janairu a shekara ta ( 1992) zuwa watan Nuwamba a shekara ta( 1993)

2 Gwamnan Jihar Kano 29 ga watan Mayu a shekara ta( 1999) zuwa( 29 ) ga watan Mayu a shekara ta (2003)

3. Ministan Tsaro na Kasa watan – Yula shekara ta ( 2003 ) zuwa shekara ta ( 2007)

4. Babban Jakadan Najeriya a Dafur ta kasar Sudan A shekara ta ( 2007) zuwa shekara ta (2011) 5. Gwamnan Jahar Kano – (29 ) ga watan Mayu a shekara ta (2011) zuwa( 29 ) ga watan Mayu a shekara ta ( 2015) 6. Satanan Kano ta Tsakiya –( 11 ) ga watan Yuni a shekara ta ( 2015 ) zuwa shekara ta ( 2019).

[5] [6] Dukkan yawancin makarantun da Kwankwaso yayi karatu shi ne yake riƙe mukamin shugaban daliban makarantun kuma an taba zaɓarsa a matsayin shugaba.

Rabiu musa kwankwaso da kuma rochas okoracha

Zamansa Gwamna

[gyara sashe | gyara masomin]

An zaɓi Rabiu musa Kwankwaso a matsayin gwamnan jahar Kano a shekara ta( 1999), ƙarƙashin jam'iyyar( PDP), har zuwa shekara ta( 2003), inda ya yi rashin nasara a hannun Ibrahim Shekarau. Kasantuwar sa gwamna a jahar Kano, ya zama wani babban al'amari da ya faru a jahar kano, kamar yadda Kwankwaso ya ke nuna cikakken goyon baya ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo. Tare da yadda ya kirkiro wasu tsarurruka na musamman a gwamnatinsa da kuma yadda rashin nasarar sa ta kasance a hanun tsohon gwamna Ibrahim Shekarau. Sai dai kuma Kwankwaso ya sake nuna sha'awar tsayawa takara a zaben shekara ta( 2007), amma hakan bata yiyuba sakamakon samunshi da wasu laifuffuka da gwamnatin Ibrahim Shekarau ta jam'iyyar ANPP ta yi. Sai kwankwaso ya kawo wanda zai yi takarar a jam'iyyar PDP wato Ahmad Garba Bichi.

Taron Kwankwasiyya kenan, a jihar kano
yan kwankwasiyya a jihar kano
Yadda kwankwaso ya maida kofar nasarawa kenan ta zamani

Kwankwaso bai yi ƙasa a gwiwa ba wajen sake tsayawa takarar gwamna a zaben shekara ta ( 2011 ), kuma ya yi nasarar kayar da jam'iyyar ANPP wanda Salihu Sagir Takai yayiwa Takara. An yi zaben ranar (26) ga watan Afrilun shekara ta (2011), kuma ya kama rantsuwar aiki a ranar (29), ga watan Mayu shekara ta( 2011). Rabi'u Musa Kwankwaso na daya daga cikin Gwamnoni guda biyar wato( G-7 ) waɗanda suka fita daga jam'iyyar su ta PDP tare da sauya sheka zuwa jam'iyar APC.

Akidar siyasar Rabiu Musa Kwankwaso Kwankwasiyya

.

  1. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.channelstv.com/2024/06/22/israeli-women-rush-to-buy-guns-in-october-7-aftermath/amp/&ved=2ahUKEwjt4bf8p_OGAxVWbEEAHV2CDNEQyM8BKAB6BAgFEAI&usg=AOvVaw3ubEadpq7qY5g4-x0qIn6H
  2. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://punchng.com/creation-of-new-emirates-an-assault-on-our-culture-sanusi-defends-kano-unity/%3Famp&ved=2ahUKEwiTmdG8qPOGAxWDV0EAHUZuAB8QyM8BKAB6BAglEAE&usg=AOvVaw0CaLiEeamOvC-lZtWdcvij
  3. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://punchng.com/tinubu-celebrates-as-nigeria-sells-gold-injects-5m-into-economy/%3Famp&ved=2ahUKEwjxhMbsqPOGAxXXQEEAHRtkAKkQyM8BKAB6BAgGEAE&usg=AOvVaw3Xf5WE758v4u2mvR5kIYt7
  4. https://www.bbc.com/hausa/articles/cy6j9ypq2jxo
  5. https://www.africa-confidential.com/profile/id/3939/Rabiu_Kwankwaso
  6. https://blerf.org/index.php/biography/kwankwaso-rabiu-musa/