Salihu Sagir Takai
| Rayuwa | |
|---|---|
| Haihuwa | Takai, 20 Disamba 1955 (70 shekaru) |
| Sana'a | |
| Sana'a | ɗan siyasa |
Salihu Sagir Takai dan siyasar Najeriya ne, masanin ilimi, ya taba rike mukamin kwamishinan gwamna Malam Ibrahim Shekarau kuma tsohon shugaban karamar hukumar Takai ta jihar Kano kuma yazama dan takarar gwamna sau 3 na jam'iyyu uku ANPP (2011), PDP (2015), PRP (2019) da APC(2020). [1]
Rayuwar farko
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Salihu a karamar hukumar Takai a jihar Kano, ya halarci makarantar firamare ta Unguwar Kwalli a Jihar Kano.
Sana'ar siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]An zabi Salihu Shugaban Karamar Hukumar Takai yayin da Injiniya Rabi’u Kwankwaso yake Gwamnan Jihar Kano a tsakanin 1999 zuwa 2002, Salihu Ya Zama Kwamishina bayan an zabi Malam Ibrahim Shekarau Gwamnan Jihar Kano a shekarar 2003 a Najeriya. Shekarau ya nada Takai a matsayin rusasshiyar jam’iyyar All Nigeria Peoples Party ANPP a yanzu All Progressive Congress APC, dan takarar gwamna [1] [2] a 2011 Nigeria General Election wanda Rabiu kwankwaso na PDP ya kayar da shi, Salihu kuma shi ne dan takarar PDP [3] a zaben 2015 inda Pro Abdullahi Umar Ganduje ya doke shi a 2015. (APC) har ma ya taya Gwamnan murna kafin a bayyana sakamakon zaben a hukumance. [4] [5] [6] A 2018 Takai ya sauya sheka zuwa PRP bayan Rabiu Kwankwaso ya nada Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP [6] [7] [8] [9] Takai ya zama dan takarar jam'iyyar PRP inda ya zabi Kabiru Muhammad Gwangwazo a matsayin abokin takarar sa a Nigeria zuwa 2019 Gwamna Abdullahi [10] [11] [12] a karo na biyu, Takai Decamp ya koma APC ya koma tsohon ubangidansa Malam Ibrahim Shekarau
EFCC ta gayyace Takai tare da tsare shi har sau biyu kan zargin cin hanci da rashawa, na farko a lokacin yana kwamishina tsakanin shekarar 2003 zuwa 2007 sai na biyu dangane da asusun yakin neman zaben shugaban kasa Goodluck Jonathan N23bn [2]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Takai joins Shekarau in APC - Daily Trust". dailytrust.com. Retrieved 2023-06-05.
- ↑ "EFCC arrest former Kaduna state governor, Ramalan Yero and ex PDP governorship candidate, Sagir Takai". Linda Ikeji's Blog (in Turanci). 2016-05-17. Retrieved 2021-02-22.