Jump to content

Jam'iyyar PRP

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jam'iyyar PRP
Wikimedia disambiguation page (en) Fassara

PRP ta kasance ɗaya ce daga cikin Jam'iyyun siyasar Najeriya wacce ta kwana biyu. Anyi ƙoƙarin fara kafa wannan jama’iyya a cikin jamhuriyyar siyasar Najeriya ta biyu wato (second republic) da turanci, a cikin jihar Kano. Jama’iyyar ta samu nasarar cin zaɓen manyan jahohin arewacin Najeriya guda biyu daga cikin goma na wancan shekarun. Jahohin sune; Kaduna da kano kafin a cire jihar Katsina cikin Kaduna, haka kaso kafin a cire jihar Jigawa su ne jahohin da jama’iyyar ta PRP ta samu daman nasarar cin zaɓe a wancan lokacin (1971).

Tsarin tutar ta

[gyara sashe | gyara masomin]

Anyi ma tutar jam'iyyar PRP ƙawa da makulli a tsakiyar ta sannan samanta launin ja haka ƙasanta launin baƙi

Wanda ya Kafata

[gyara sashe | gyara masomin]

Marigayi malam Aminu Kano, wanda aka fi sani da limamin canji ko jagoran talakawa, shi ne ya jagoranci kafa jama’iyyar bayan samun saɓani da ya yi da ƙungiyar masu kishin ƙasa (National Movement).[1][2][3]Kamfen ɗinta ya shahara wajen tattara ƙuri'un matasa, tare da yin kamfen da magana a cikin jami'o'i, tare da gabatar da kanta a matsayin mai kawo gyara[4]. Da farko, ta tattara aƙalla kashi 40% zuwa 50% na rating rating,[5] amma a waɗancan lokutan da ranar zaɓe ta kusa, tana da zaɓe mai tsauri tare da ɗan takarar Lakas kuma tsohon sakataren tsaro Fidel Ramos, [6] waɗanda shugaba mai ci a lokacin Corazon Aquino ya amince da su[7].

A cikin kwanakin farko na kirga ƙuri'un, Santiago ne ya jagoranci tseren, tare da kasancewa kan gaba a dukkan birane da kananan hukumomi a Metro Manila. Amma bayan da lamarin ya faru na katsewar wutar lantarki, Ramos ya jagoranci kidayar, kuma daga karshe ya lashe zaben.[8] Santiago ya yi amfani da wannan lamarin a matsayin shaida na shigar da zanga-zangar zaben. [9]Ma’aikatan kafafen yada labarai daban-daban sun zama shaidu kan magudin da aka yi a zaben, inda kalmar nan, ‘Miriam ta yi nasara a zaben, amma ta sha kaye a kirga kuri’u’ ta shahara.[10][11] Sai dai daga karshe kotun koli ta yi watsi da zanga-zangar ta ta.[12] Amma a zaben kananan hukumomi, Lim da Atienza sun tabbatar da nasararsu a Manila.[13]

Zaɓen 1995: Zaɓe tare da NPC[gyara tushe]

Domin zaɓen majalisar dattijai na 1995, Santiago ya shiga jam'iyyar adawa ta Nationalist People's Coalition (NPC) karkashin jagorancin shugaban majalisar dattijai na lokacin Ernesto Maceda.[14] Santiago ya kwace nasara, inda ya zama na 6. A zaben kananan hukumomi, Lim da Atienza tare da wasu 'yan takarar majalisar birni da suka shiga jam'iyyar PRP sun lashe zaben a Manila.[15][16]

An kafa wannan jama’iyya ta PRP a cikin shekarar (1978) biyowa bayan janye takunkunmin siyasa da gwamnatin sojon tarayyar Najeriya ta yi a ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 1978, wacce shugaba olusegun Obasanjo ke jagoranta a lokacin bayan rasuwar Janar Murtala Mohammed. Takunkumin da ya ɗauki tsawon shekaru goma sha biyu (15/01/1966 – 1/10/1978).

Rikice-rikice

[gyara sashe | gyara masomin]

Ɓaraka da aka samu a cikin haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu kishin ƙasa National Movement, tsakanin wasu daga cikin shugabanninta da kuma malam Aminu Kano a ɗaya ɓangaren, a yunƙurin mayar da ƙungiyar jama’iyyar siyasa shi ne abin da ya kai ga dasa ɗan-ba na kafa jama’iyyar ta PRP. Saboda haka ita wannan jama’iyya ta PRP da ƙafafunta biyu aka haifeta; ba a yi goyon cikinta ba bare a yi renonta har ta yi rarrafe. Ko da ma an yin ta wata fuska, to ba kamar yadda aka saba ba. Saboda haka nema ta samu damar yin tserereniya da yayyenta. Har ma ta iya tserewa wasu daga cikinsu. Bayan an kafa wannan ƙungiya a zauren majalisar sake nazarin sabon tsarin mulkin Najeriya, sai ya zama mambobinta a matakin farko ‘yan waccar majalisa ne zalla. Amma daga baya sai aka gabatar da ita ga ƙungiyar dattawan arewa Northern Consultative Forum. Marigayi malam Aminu Kano, mamba ne a waccar majalisa ta sake nazarin sabon tsarin mulki, sannan kuma shugaban kwamatin rubuta tsarin mulkin. Ƙari a kan haka kuma, shi mamba ne na wannan ƙungiya ta dattawan arewa. Saboda haka, sai ya bayar da shawara ga dukkan ‘yan siyasar arewa jam'iyyar NEPU, jam'iyyar NPC, jam'iyyar MBC da sauransu da cewa su shiga wannan ƙungiya baki ɗayansu. Ya ƙara da bayanin cewa, waɗanda suka kafa waccar ƙungiya ta kishin ƙasa, ba cikakkun ‘yan siyasa ba ne a wancan lokacin. Saboda haka, idan har ƙungiyar ta zama jama’iyya, to su za su fara cin moriyar abun. Saboda su za su zama shugabannin jama’aiyyar. Ganau ba jiyau ba, Alhaji Salihu Tanko Yakasai ya ce, “wannan harsashe na malam Aminu Kano, shi ne kuma abin da ya tabbata daga baya”. Shi kuwa Alhaji Salihu Tanko Yakasai, makusancin malam Aminu Kano ne. Kusanci kuma na haƙiƙa. Saboda a wannan lokaci dukkan wasu tarurruka da shi Alhaji Salihu Tanko Yakasai ya ke halarta, yana zuwa ne a matsayin wakilin malam Aminu Kano da kuma tsohuwar jama’iyyarsu ta NEPU.

Rugujewar jam'iyyar PRP

[gyara sashe | gyara masomin]

Rugujewar jamhuriyyar siyasar Najeriya ta biyu; wato rushewar jamhuriyya ta biyu a siyasar Najeriya, shi ne abin da ya kawo ƙarshen wannan jama’iyya. Sai dai, tsohon gwamnanta na Kaduna, Alhaji Abdulƙadir Balarabe Musa, ya sake sabunta ta a wannan jamhuriyyar da yanzu ake cikinta a siyasar Najeriya. Tsawon ran wannan jama’iyya ta PRP shi ne tsawon ran jamhuriyyar siyasar Najeriya ta biyu. Wanda kuma hakan ta faru ne bayan sanarwar rushe jamhuriyyar ta biyu da ya biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 31 ga watan Disamba na shekarar 1983. Wannan shi ne bayani game da farko da kuma ƙarshen jama’iyyar PRP a jamhuriyya ta biyu.

  1. Balana, Cynthia D.; Antonio, Rafael L. (2016-09-30). "Miriam Santiago; 71". INQUIRER.net. Retrieved 2025-06-13.
  2. The Loudest of Them All". Rappler. Retrieved 2025-06-13.
  3. "Mayoralty race at a glance". Manila Standard. Kamahalan Publishing Corporation. May 24, 1992. p. 13. Retrieved December 12, 2024.
  4. One News PH (2022-08-04). Remembering FVR: 'Steady Eddie'. Retrieved 2025-06-13 – via YouTube.
  5. Great Leaders (2015-10-26). Part 2 - Miriam Defensor Santiago Presidential Speech 1992 Elections. Retrieved 2025-06-13 – via YouTube
  6. Pinugu, Eleanor (2025-05-12). "Strength of losing well". INQUIRER.net. Retrieved 2025-06-13.
  7. Shenon, Philip. "Aquino Endorses Ex-Army Chief in Vote". Retrieved November 8, 2018.
  8. Servando, Kristine F. "Miriam: I was cheated, but didn't call for people power". ABS-CBN News. Retrieved November 8, 2018.
  9. Servando, Kristine F. "Miriam: I was cheated, but didn't call for people power". ABS-CBN News. Retrieved November 8, 2018.
  10. Wolfgang, Sachsenroeder (2018-05-30). Power Broking In The Shade: Party Finances And Money Politics In Southeast Asia. World Scientific. ISBN 9789813230750.
  11. One News PH (2022-08-04). Remembering FVR: 1992 elections vs Miriam Defensor-Santiago. Retrieved 2025-06-13 – via YouTube.
  12. Servando, Kristine F. "Miriam: I was cheated, but didn't call for people power". ABS-CBN News. Retrieved November 8, 2018.
  13. "Mayoralty race at a glance". Manila Standard. Kamahalan Publishing Corporation. May 24, 1992. p. 13. Retrieved December 12, 2024.
  14. Maragay, Fei (May 5, 1995). "Maceda conceded defeat – Ramos". news.google.com. Retrieved 2025-05-01.
  15. "Manila poll winners finally proclaimed". Manila Standard. Kamahalan Publishing Corporation. 1995-05-18. p. 164. Retrieved 2025-02-01.
  16. "Lopez to seek disqualification of Mayor Lim". Manila Standard. Kamahalan Publishing Corporation. 1995-05-09. p. 46. Retrieved 2025-01-14.