Jump to content

Idris Garba

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Idris Garba
gwamnan jihar Kano

ga Augusta, 1988 - ga Janairu, 1992
Mohammed Ndatsu Umaru - Kabiru Ibrahim Gaya
Gwamnan jahar benue

1987 - 1987
Ishaya Bakut - Fidelis Makka
Rayuwa
Haihuwa Lapai, ga Yuli, 1947 (77 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Hausawa
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Manjo Janar, Idris Garba ya kasance Gwamnan Soja na Jihar Benuwe daga shekara ta 1987 zuwa shekara ta alif 1988 da kuma Gwamnan Jihar Kano daga, shekara ta alif 1989 zuwa shekara ta 1992.

Tarihin Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Idris Garba an haife shi ne a watan Yuli na shekara ta 1947 agarin Gulu, Nigeria, Lapai karamar (karamar Hukuma) a Jihar Niger . Yayi karatun sakandare a makarantar Sojan Najeriya, Zaria daga shekara ta 1963 zuwa shekara ta 1967.

Ya shiga Kwalejin Tsaro ta Najeriya, Kaduna, kuma an ayyana shi a matsayin laftanal na biyu a shekara ta 1968. Ya halarci kwasa-kwasai da dama kamar yadda yake a jerin layuka masu zuwa kamar haka:

  • Artillery Troop Commanders Course USSR, July 1970 - September 1971
  • Young Officers Course Nowshera, Pakistan, July - December, 1972
  • Technical Gunnery Course Larkhill, Salisbury, UK, May - August, 1975.
  • Field Artillery Officers Advanced Course, Forstill, Oklahoma, USA June 1977 to February 1978;
  • Command and Staff College, Jaji August 1978 to September, 1979
  • Regiment Battalion Commanders Course, Nigerian Army School of Infantry, Jaji in 1981.

Gwamnan soja

[gyara sashe | gyara masomin]

A shekara ta 1988, Janar Ibrahim Babangida ya nada shi Gwamnan Soja na Jihar Benuwe. Daga nan aka nada shi gwamnan jihar Kano a watan Agusta 1988, yayi aiki har zuwa 1992 lokacin da ya mika mulki ga farar hula Kabiru Ibrahim Gaya har aka kai ga shiga Jamhuriya ta Uku ta Najeriya . Col. Idris Garba ya zartar da wata doka wacce ta soke dokokin da suka gabata tare da bai wa ma'aikatar wasanni ta jihar Kano damar daukar nauyin bunkasa harkokin wasanni a jihar.